Shafi na hudu

2.2K 194 20
                                    

KUNDIN HASKE

            Al K'ALUMAN Marubatan HASKE

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
  MAMAN KHADY

ABOKIYAR ZAMA
(Kishiya)


BABI NA HUDU

Shafi na hudu

Jin motsin shigowarsu ya sata tashi ta nufi falon inda takejin hayaniyar mutanan gidan, Jikinta ba k'aramin sanyi yayi ba da taga megidan nasu da yaranta sun baje kaji sunataci ga kuma amarya agefe tana tsiyaya musu ruwa idan dame buk'ata.

Turkashi lallai bak'aramin gibi tajama kantaba.

"Sannu da fitowa aunty"

Cewar jidda "Yauwa sannu jidda ya yaran?"

Duk sunyi mamkin yanda ta amsa kamar babu wani abu cikin ranta. Mik'o mata wani kulli tayi domin taga sai had'iye miyau take kunsan abunku dame ciki. Aiko da sauri ta amshe tare da bud'ewa tana cewa "Ashe dad'i kukeci na gode jidda" Beyi niyyar tankawaba amma dole yace wani abu, saida ya kalli salmar sosai kamin yace "Dole faki b'oye sunanta sabida yaran nan banso suma su dinga k'iranta da sunanta kingane ko?"

Cikin sanyin jiki ta amsa da cewa "Toh shikenan zandinga k'iranta da aunty dan Allah kuyi hakuri ku yafemin wallahi sharrin shaid'an ne na tuba Abba"

Bedaice komai ba amma harga Allah yaji dad'i, itako jidda ai nan da nan murnarta tak'i b'oyuwa inda tace "Babu komai wallahi dama ni ban kullaceki ba."

Kusan daga wannan lokaci sai aka sami zaman lafiya cikin wannan gida, A lokacin ne salma tagane cewa tabbas abokiyar zama rahmace idan kasami ta gari. Duk wani aikin gidan kusan jidda ce keyi musamman yanzu da cikin salma yake ta dad'a girma ga kula da yaran ga kuma kula damegida wanda dama matukar cikinta ya girma to gudun shi takeya wajan shimfid'a wannan karanma beda matsala domin jidda bata tab'a nuna gazawarta akan shi ba.

Tabbas wani lokacin rashin ganewa ke samu gudun abokiyar zama sai kuma tsabar son zuciya irin namu amma tabbas abokiyar zama duk jarabarta wallahi saikun karu da junanku.

Gidan Abdallah ma hankalinsu kwance yake basu da wata matsala sosai aysha tana ba bilkisu girmanta yayin da itama take k'ok'ari wajan ganin bata cutar da itaba, Kansu had'e yake irin sosai d'innan wanda yau ina zuwa gidan na taddasu su uku suna hirarsu megida Abdullah da kuma matanshi biyu yana cewa.

"Wallahi ba k'aramin dad'i nake jiba idan na shigo cikin gidan nan ina sonku matana kuma ko'ina ina matukar yin alfahari da samunku amatsayin matana fatana, Allah ya kore sharrin shaid'an tsakanin mu baki d'aya."

Ameen suka amsa baki d'ayan su, kamin bilkisu t d'ora da cewa wallahi ban tab'ajin dana sanin karin auren kaba kaga gashinan yanzu hankalina kwance na samu 'yar k'anwata muna temakon junan mu ai duk me hakuri to tabbas yana tare da nasara nasan dana tashi hankalina da yanzu kila bani gidannan, nifa masu gudun abokiyar zamama dariya suke bani wallahi domin matuk'ar namiji ya fara maganar aure to wallahi babu wata faffaka da zata hanashi yi koda mace bokaye takebi kuwa..."

Aysha tace "Uhmm ai aunty yanzu harda 'yan mata wallahi domin koni lokacin da akace me mata zan aura kuka nai tayi sabida inajin tsoron kadda in fad'awa muguwa saida mama tai tabani shawara da addu'a sannan na sami nutsuwa, Amma sosai akejin tsoron auran me mata."

Dariya duk suka yi kamin Abdallah yace "Bari intayaku hirar kunsan kuwa duk macen da ta tashi hankalin mijinta dan zai mata abokiyar zama soyayyarta barin zuiyarshi  take yi dan haka garama tun farko maganin kadda ayi to kar a fara domin shi aure kaddarace matukar yana cikin kaddararka to wallahi kota halin k'ak'a sai mutun yayishi, dan haka zakiga duk macen da tasan kanta to wallahi bata gudun abokiyar zama dan Allah kadda kubari shaid'an yai tasiri cikin zukanku Alllah yai muku albarka"

Ameen suka amsa shi kenan basu da sauran matsala cikin gidan su.

Gidan Abbakar ma kwanciyar hankali ta wanzu cikin gidan hankalinsu ya kwanta yana matukar k'ok'ari wajan ganin be nuna ban-banci tsakanin suba salma ta shiga taitayinta sosai domin talura ta kusa tsinka igiyarta da kanta sosai take ganin girma jidda wadda ke wahal mata dare da rana kuma ba ta tabbatar da amfanin abokiyar zama ba, sai da nak'uda ta kamata gashi abbakar ya tafi abuja wani aiki, dakyar ta samu ta lalubo number d'in jidda ta k'irata aiko nan da nan ta iso gareta cikin ikon Allah ta dinga gaya mata abunda zatai mata har Allah ya sauketa lafiya wannan karonma namiji ta kuma samu mazanta hudu kenan, har hawayen dad'i saida jidda tayi hakama salma domin tasan inbacin temakon jidda d'in da sai dai kawai tajira taga abinda Allah zai yi, cikin daren nan tagama gyara ko'ina da ina itama anan d'akin tai kwanciyarta kusa da jariri, saida asuba sannan suka gayama me gida k'aruwar daya samu.

***

A rayuwa fa duniya 'yar hak'uri ce matsawar kinyi hakuri to tabbas kina tare da samun dukkan abinda kikeso, zaman duniya bana k'iyama bane  tazo ta zauna ku fahimci juna duka-duka kwana nawa zakuyi ku rabu ko mun manta da mutuwa ne?
  
Mutuwa baza ta tab'a barin mu dawwama da juna ba dole wataran saita rabamu so kike yi saikin mutu sannan mijinki ya fara raragefen neman waccen da zai auro tazo ta gana musu azaba ko 'ya'yan ki?

Naga matan dake hana mazan su aure daga karshe su b'ige da neman mata wanda daga karshe har aje asamo musu wata muguwar cutar yaxo kema ya sanya miki.

Akwai wacce zata hana mijin nata aure sai kuga Allah ya kasheta sabida akwai rabon wasu yaran ajikin wata.

Masu yima abokiyar zama asiri kuwa domin had'a ta da wani mugun abu kuwa tabbas ku tuba tun kamin lokaci ya kure maku domin kuwa Allah yana yima azzalumai talala sannan ya kamasu ta inda basu zata ba K'ALUBALE gareku mata.

_Mata muji tsoran Allah mudaina juya baya ga maganar Allah, tabbas shine mafi sanin masu sani shine yasan abunda yake nufi da abokiyar zama tunda har ya halarta zama da ita. Akwai ciwo idan za'a yi miki ita amma idan kika yi hak'uri zakiga ba komai bane._

_Na gode duka-duka anan na kowa karshen wannan d'an gajeren labarin Allah ya amfanar damu alkhairi duniya da lahira._

MAMAN KHADIJA CE DAGA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION BYE.💡

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now