3

246 45 4
                                    

_HASKE  WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers

☆“☆ª☆_☾'☆•'☆´-'☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** '☆´-'☆´-

Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*

” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 03☆.

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU 22*

*Kuyi hakuri sister na rashin jina da bakuyi ba jiya*

Dake Mara gaskiya ko a ruwa yake gumi yake, hakan yasa hankalinsu tashi ba d'an kad'an ba, cikin tashin hankali JAMILAH tatashi ta cintsa kanta da sauri shima ya shiga gyara kansa ta nuna masa wajen b'uya kana ta fitto bakin get d'in tana cewa waye..
Wani saurayi ne ya amsa mata da cewa, dan Allah nan ne gidan Alhaji Muktar..
Sanda ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "ba nan bane gidan gaba ne... Yace "Toh na gode..

Haka ta koma taga ogan nata duk ya had'a gumi, tamai dariya da cewa, "Toh bashi bane saika fitto, yace "dan Allah kibar maganar wasa ki gaya min gaskiya, tace "Allah da gaske nake, kasan bazan maka wasa irin wannan ba..
Fitowa yayi da rungumarta yana cewa, gaskiya duk ran da asirinmu ya tonu akwai matsala  Babba, tace "Kai zakaga hakan, danni ko kad'an bani tunanin zuwan wannan ranar..
Murmushi kawai yayi mata, da haka kuma suka qara bajewa.

Washe gari *kwana na uku*

Basu rabu da juna ba sai kusan goma da rabi..
Sam basu so hakan ba, dan basu gajiya da junan nasu..

Haka ta gyara gidan ta shiga kitchen tahau dafe dafe dan tayi waya da mijin nata yace mata yana kan hanya..

Can wajen qarfe uku ya iso, KAMAL yaro ne nutsattse me hankali, ga kyau ga d'an abin hannunsa, yana san  JAMILAH fiye da komai a rayuwarsa, dan ta cika dukkan wasu sharid'ansa, tana kyau sosai, wanda hakan yana cikin burinsa nasan Auran mace me kyau over, gata da iyayi da kisisina da shagwab'a irin ta yara yaran mata, uwa uba ba ƙaramin jin daɗin harka da zaman takewa yake da ita ba...

Mace ce wacce bata da qiwa akan tsabta dayin duk wani abu dazai d'auke hankalin duk wanda take tare dashi, ga ibada dan ba lefi tana da ibada sosai..
  Gane hakan yasa ya  qara jinta da ƙaunarta aransa...

Cike da so da ƙauna take ta faman tararrayarsa, tsayawa kallanta kawai yake, dan shi dai kam komai take burgesa take..

Ta kallesa da fararan idanta masu qara burgesa tamai fari dasu tace, "Gaskiya dole na qara godema Allah daya halicceka yasa kuma ka zamo miji gareni, wallahi Baby ba ƙaramin sanka nake ba, ina sanka ina ƙaunarka sosai fiye da komai na rayuwa ta, tunda na rasa iyayena bayan Aure na dakai, na qara maka wani Babban matsayi cikin raina.... Tana zuwa anan cikin kalaman nata da matso kusa dashi da sakala dukkan hannuwanta biyu akan kafaɗinsa taci gaba da cewa, bakaji yanda ayanzu nake ji a raina bane, ji nake kamar na cinyeka d'anye, kullum maganata da zuciyata dama kana kusa dani, dama dama dama aikin naka ya dawo nan, danafi kowace mace murna da farin ciki a rayuwa..
Murmushi yayi mata da cewa, "Insha Allah zan dad'a dagewa da Addu'a kan Allah yasa fatan ki ya tabbata, dan nasan dole na fiki farin ciki, kasancewar har gobe bazan yarda da cewar kinfi ƙaunata akan ƙaunar da nake miki ba..

Wani shegen murmushi tayi dajan hannunsa zuwa bedroom dan ya watsa ruwa ya kuma ci abincin data girka masa..


Safina ko dake jiya a hotel ta kuma kwana, hakan yasa tana komawa gida tafara baccin gajiya, har yaranta suka dawo daga skull me aikin nata ta shiryesu suka tafi madarasa bata tashi ba, sanda tayi mararta ta murd'a kana tatashi a gigice..

Ganin Lokacin sallah yasa tatashi a daddafe, tayi sallar, Saidai me kamar jira ake ta idar da sallar ciwan ya qara ram da ita fiye dana d'azu..

Safina tana da tsoran ciwo, tunda aka tab'a cire mata afandis shekarun baya take jin tsoran ciwan ciki, dan ba qaramin azaba taci ba, Toh yanzu jin ciwan cikin tayi kamar na afandis d'in, wannan yasa ba shiri ta zura doguwar riga sai asibiti, Allah yasa asibitin ma kusa ne nan takai kanta cikin lokaci qanqani..
Doctor Aminu ya duba ta ya tabbatar mata ba afandis ke damunta ba, Ciki ne da ita na wata d'aya da sati biyu....
Ai saiga Safina ta gwalalo ido, tace "Ciki ciki wane iri.. doctorn yayi murmushi da tabbatar mata ciki ne, har ya fara bata shawarar ta kula da shi da kyau dan Wannan baya san wahala, ba irin cikin da tayi abaya bane, wato na d'anta Salim da yayarsa Hanifa...

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now