2

257 40 3
                                    

_HASKE  WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers

☆“☆ª☆_☾'☆•'☆´-'☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** '☆´-'☆´-

Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*

” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 02☆.

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU 22*
*kwana na biyu*

Washe gari da misalin qarfe goma sha d'aya da rabi ta fitto daga wanka tana zama gefen gado yahau shafa mata mai, Yana yaba naushin jiki da kyau da Allah yayi mata.
"MATAR KAMAL... "Kai kad'ai kake da mallakinta, ta bashi amsa da faɗin hakan, sai yayi murmushi da cewa, "Tunda nake wurd'a da mata ban tab'a cin karo da yarinya irinki ba, ga naushin jiki, ga kyau, ga dad'in harka...
"Hmmm, na lura da duk lokacin da kake shafamin mai saika fad'i waƴannan kalaman.
Cikin k'asa da murya irin nasu na manya yace "kina jin daɗin hakan, tace "sosai mah, ai duk lokacin da ka yabeni bayan jin daɗi qara ƙaunarka nake, yace "waini da Yaran nan wa kika fiso ne..
Maida kallanta garesa gabaki d'aya tayi da cewa, "Kasan dai nafi samun cikakkiyar kulawa da kyautatawa agunka fiye dashi, kuma kaji ance ZUCIYAH tafi san me kyautata mata..
Takai ƙarshen zancen da tashi ta suturta jikinta,  sanda ta yafa gyalanta ta kuma rataya jakarta kana  taci gaba da cewa, Ina sanka original KAMAL, ina ƙaunarka da kyau, dan Allah karka so wata mace fiye da san da kake min..
Yace "baki da matsala da wannan, dan ina tabbatar miki ko mamansu bana jinta kamar yanda nake jinki a raina...
Saita yatsina fuska alamar Sam bata so ya sako mata Sunan wata wai matarsa ba..
Hakan yasa ta fitta daga room d'in bata ko kallesa yana mata magana Sam bata kulasa ba.

Bai takura mata dasan saita kulasan ba, dan dama yafi kowa sanin halinta akan kishinsa, Sam bata san ya tab'o mata matarsa, koda ko zagin matar tasa zaiyi...

Safina na cikin motar tana jiranta, ta shiga tana jan tsaki.

"Ke lafiyar ki kuwa, ba farawa da gaisuwa sai jan tsaki, Safina ta gaya mata hakan tana me jan motar, "Kedai bari, KAMAL ne ya b'ata min rai, wai daga yin magana ya wani sako min zancen shegiyar matar sa..
   Safina ta girgiza kai da cewa, "Wai me yasa matar nan ta dameki ne MATAR KAMAL, bayan kin fita more mijin nata, dan nayi imani saura kike bar mata tana tab'awa da hakuri, amma duk ran da ya kuskure ya fad'i sunanta a zancenku duk sai kibi ki d'auki zafi..

Tace "Nifa na tsaneta ne kawai, kuma qiris nake jira na wanketa soso da sabulu naga me tsaya mata,..
Safina ta sheqe da dariya tace "bame tsaya mata, dan shi me tsaya matan shi kika cafke, kina sha'aninki MATAR KAMAL, can KAMAL nan KAMAL wai ya abin yake miki ne...

Tab'e tayi, ta ce "Wallahi komai normal..
"Idan ko haka ne dan Allah kiyi hakuri karki kulata, dan kema kinsan had'a mata zafi zakiyi, idan dai har da gasken wanke ta da soso da sabulun za kiyi, dan Allah kiji tausayinta, dan kin Riga da kin gama da ita kwata kwata...

Dariya JAMILAH tayi da cewa, ai ban gama da ita ba, sai ran data ganni da cikin d'aya daga cikinsu, musamman original d'in...
Dariya Safina ta qara kwashewa da ita, tace "tab, ke akwai sauran dirama fah..
Shuru Jamila tayi mata kawai..

Sanda Safinan ta sauketa a kofar gidan nata Sannan tace da ita "kardar a wucce wani wajen, dan Allah kije kiji min da yarana, dan sun kusa dawowa daga skull, yanzu lokacin su ne,.
Dariyar dai Safina ta qara yi da cewa "Toh, baki da da matsala da hakan.

Minti goma da shigarta gidan nata saiga kiran sirikarta a waya wai tazo yanzu yanzu tana jiranta a gidanta, kuma bata jira cewarta ta kashe wayarta..
Tab'e baki JAMILAN tayi kana tashiga kiran wayan mijin nata, kusan kira uku bai d'auka ba, bata damu da hakan ba, haka ta yafa gyalanta ta nufi gidan sirikar tata wanda anan cikin layin nasu yake...

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now