Shafi na biyar

1.6K 150 6
                                    

KUNDIN HASKE

AL-KALUMAN MARUBUTA...

NA KUNGIYAR...
     HASKE WRITERS ASSO

TARE DA AL-K'ALAMIN...

HAFSAT RANO

WAYAR MIJI

Babi na takwas

Shafi na biyar

Sai da likita ya jaddada masa yadda zai kula da ita da abinda yake cikinta, musamman abubuwan da zata ringa ci da sha sannan uwa uba kar a dinga b'ata mata rai. Yana jinshi har ya gama a ransa yana ayyana ko likita be ce ba ai shi kuma sai in da karfinsa ya k'are. Bayan sun baro asibitin a hanyar su ta komawa gida komai ya gani sai ya tsaya ya siya a ganinsa ko xata bukata, yanayin yadda yake tukin ma kamar d'an koyo, sosai abun ya bata dariya.

"Lafiya dai wannan dariya haka, sai kin je kin sa Bbyna ya wahala." Ya tambaya yana fuskewa shi a lallai baya son tayi koda k'wakkwaran motsi ne.

"Gani nayi komai sai ka tsaya ka siya ga kuma wani irin tuk'i."

"Eh saboda lafiyar Bbyna nake yi, kinsan banason komai ya same shi." Ya amsa yana sake tsare wa

"Uhum." Tace kawai taja bakinta tayi shiru

"Ki fad'a mana, in ba tsoro ba."

"A ah babu komai, Allah ya taimaka."

"Ameen." Ya amsa a takaice.

Ko da suka xo gida ma sai da ya rik'e hannunta kar suka dangana da bedroom (d'akin k'wana). A gefen gadon ya sama mata waje yace ta xauna yana zuwa, da sauri ya juya kitchen ya wanko kayayyakin da ya siyo mata dangin su Apple, Yalo, D'ata, Goba, Dabino da sauransu. Aikuwa taci sosai tasha ruwa sannan tabi lafiyar gado tana kunshe dariyarta bayan ta bukaci cin sak'wara.

Tak'ark'are wa yayi,  ya shiga aikin gidan daka shi dai boxer da farar singlet, kafin kace me ya gaji tibis yana sauke numfashi, sak'wara da miyar ganye yayi mata bayan ya shiga youtube ya duba yadda akeyi, babu laifi yayi kokari don dama shi wajen girki ba baya ba saboda zaman hostel da yayi tun daka matakin secondary har zuwa jami'a. Gashi kuma ya kasance d'a namiji Babba a gidansu in da kannensa maza su biyar suka biyo bayanshi, sai ya zamana duk wani aikin gidan suke wa mahaifiyarsu kama daka girki, shara, wanke-wanke sa sauran su.

Tarairaya da kulawa babu irin wadda bata samu a wajen sa, farincikin samun cikin ya sanya sun manta tashin hankalin da suka shiga a baya, sun dinke tsaf sun koma kamar da, lokaci zuwa lokaci takan tuna har sai yanayin da take ciki ya chanja daka farin ciki zuwa bakin ciki, amma duk da haka tana kokarin yakicewa tana farantawa mijinta had'e da tunatar dashi hakkok'in Allah lokaci zuwa lokaci.

Ta lura maza a wannan zamanin suna da karancin ilmin islama, sun fi bada hankalinsu kachokam wajen ganin sun sami ilimin boko, sai anyi auren sai ka ga wani ko sallah da k'yar yake tashi yayi. Kullum burinsu su d'au waya suga me duniya take ciki, yau wanda abu ne ya faru a majalisar dokoki, ko a fad'a shugaban kasa. Daka nan kuma sai chatting da yanmata. A wannan bigiren dole a matsayinmu na mata sai munyi hubbasa wajen saita su, amma ba ta hanyar nuna iko da bacin rai ba, ta hanyar lallami da soyayya da tausasa harshe. Misali;
"Ummm Baban Hanan, ni kuwa sai nake ganin kamar mun d'anyi sanya wajen bauta wa Allah, musamman sallar asuba k'wana biyu bama iya yinta akan lokacinta saboda rashin kwanciya da wuri da muke,  kasan fa wayoyin nan babu abinda suke mana sai dai su kaimu su baromu, gashi sun shiga ranmu sosai, ya kake ganin zamu magance wannan matsalar?"  Ba sai Baban wance ba, ko Abban wance, ko swthrt ko ma dai mene ke kika san mijinki. Ke kikasan yadda zaki yi magana ya fuskance ki, wani a lokacin sai yace toh mu tsara lokacin da zamu dinga kashe waya muna ajiyeta.  Wani mijin ma in kikayi masa haka sai ya hau zagi da cin mutunci yace kin maidashi kafuri kince baya sallah😂. Kowa ita tasan halin kayanta

Wata kuma sai kaga taxo mijin na xaune yana tsaka da dannan wayarsa, dama ta gama k'umewa da bacin rai tana ganin ya fi bawa wayar tasa muhimmanci akan ta, sai kuji tace;

"Abun da ake a gidan nan ba'a kyautawa, mutum in ya kama waya kamar ba gobe, sallah ma mutum be damu yayi ta ba saboda waya." Cikin fushi da kumbura fuska, anan shi kuma gogan zai hau dokin zuciya sai kuma rigima ta barke. Allah ya kyauta.

Bangaren uwar gayyar
Khairat ta tsomale ta zama kamar wadda tayi jinyar shekara guda, babu wani jituwa tsakaninta da Jabir, k'wata-k'wata ya kauracewa zaman gidan ma baki d'aya. Rabon sa da ya zauna yaci abinci a gidan ta manta, barci ne ke kawo shi kawai, anan ya k'ara sumun damar barje hirarsa da yanmatan sa, dama saboda Khairat d'in yake d'an saukakawa, amma yanzu tunda komai ya fashe sai ya bada kaimi cikin rashin tsoro.

Tayi bala'in tayi kukan tayi tashin hankali amma duk a banza, tana farawa yake toshe kunnensa da earpiece. A cikin haka mashkoor ya fara kashin hakori, kafin kace me ya galabaita matuka, babu irin kiran da batayi wa Jabir ba amma fafur yak'i d'agawa. Tana kuka ta sungume shi sukayi asibiti, kafin suje har ya fara amai idanunsa sunyi fari ya matukar galabaita. Kati ta k'arba tabi layi tana kuka kasa-kasa, mutane wajen 10 ne a gabanta gashi likitan  ya fita yana tsaka da duba wani yaro, babu wanda yasan in da yayi har aka ci wajen mintuna goma, wai kuma da sunan emergency unit kenan. Ta kusa da ita ce ta lura da yadda Mashkoor din yake suma, cikin tausaya wa tace ta shiga wajen likitan lokacin da layi yazo kanta. Data shiga ma sai da matar dake kai files wajen likita taso yi mata wulakanci ganin ba sunan ta ne a jikin file d'in da yake gabanta ba. Sai data fita ta kira matar data bar mata layin nata sannan ta yarda.

Duba d'aya likitan yayi ma Mashkoor yasan Allah ya karbi abinshi.

"Sai dai kayi hakuri hajiya, babu abinda zamu iya ma yaronki, he's dead." Ya fad'a cikin hausar sa ta yan koyo.

Wani irin ihun kuka ta saki hankalinta a tashe.

Manage pls.

Rano.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now