Shafi na uku

7.3K 353 5
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al K'ALUMAN Marubatan HASKE_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
           *NANA DISO*

*DARAJAR MUTUNCIN MU.....*
       _('yan zamani)_

     
BABI NA DAYA
    Shafi Na uku...

Washe gari tun safe walida ta shirya cike da kwalliya amma kuma daga karshe sai tasaka hijjabi da nikaf hakan yasa tayi kyau fitowa tayi cikin murmushin da bai gama bayyana ba tace hajjaju ni natafi ina bukatar adduar ki...

   " Toh walida ki kula kisan me zaki fada kiji tsoron Allah afitar da zakiyi...

     " Tana fita sai ga Aisha ta kunnu mota mutuniyar wannan uztazancin fa haba kada ki badamu mana wallahi nayi tunanin zakiyi shigar da tafi tawa shedanci? Da wuya fa in bamuyi kamu ba...

   " Ke banson zancen banza kinfi kowa sani kawa bata sakani bata hanani yakamata ki lura na shiga duniya don na nunawa manyan cewa talakawan yaran da suke lalatawa suna da gata sune sanadiyar kwanciyar mahaifina a kauye ya kamu da cutar da ba'asan irin taba...

    " Kinga walida kinaso kicemin wai bakya kwanciya dasu banson karya dukkan nin mu fa kinsan asalin mu to menene nayi min karya?

   " Baki isa nayi miki karya ba bakuma ki isa na yaudare ki ba kawa kike ba wata ba so ki iya bakinki kafin naiya miki..

   " Am sorry walida abun bana zafi bani ai zamu iya tafiya..

   Lokacin da suka isa ko zama basuyi ba aka kira sunan walida ibrahim cikin Nutsuwa taje ta tsaya cikin sallama sannan tace wannan wata dama ce da Allah subahanallah yabani domin ina gaban manyan masu mulki da masu ilimi, tabbas duk wanda yaji tsoron Allah acikin lamarinsa To babu ta inda Allah bazai kareshi ba.. Tabbas muna rokon Allah akan wasu bukatun mu kuma sai yabamu karoki lafiya ya baka karoki arzuki yabaka to me isa mu bazamuji tsoron Allah mu taimakawa wanda basu dashi ba? Me isa bazamu guji zaluntar nakasa damu ba? don ka nemi wata dama kuma Allah ya baka baka tunanin ya kwaci yabawa Iyalan wanda muka raina? Me isa muke ganin kamar karfin mulkin mu da karfin mulki ko dukiya bazai iya barin mu ba? Kanar muna yaudarar kan mu ne a tunani na? Me isa bazamu tuna da matasan mu ba ?? sai kuji muna cewa ai wancan basu da kirki bazaka basu ba kokuma zaka zalunci mu? Don Allah mukeyi ko don mutane, Nan walida ta daga hannun ta tace dukkanin mu nan babu mai son talauci Amma me isa muke tozarta marasa shi me isa muka daukesu wanda sukafi kowa kaskanci? Muna tunanin Allah zai barmu Muna wulakanta bayinsa??

   Mu tallafawa matasan mu..Mu taimake yanuwan mu...DanAllah mu daina saka yaron wasu a shayeshaye..
 
  DanAllah mu guji lallata yaran mutane dukkanin abunda mukayi Allah zai tambaye mu,Mungode sosai Allah ya maida kowa gida lafiya..

Tafi akayi mata abisa da kalmar turanci duk tayi bayanin nan Babu abunda ya birge mai martaba irin yarinya kara ace tana bayanin nan nan yasanar da gomna cewa zaiyi mata kyauta..

   " Mai martaba ai irin matan da muke bukata ne wa'yannan nima nabata kyautar million 1 sarki kuma yace yabata kyautar mota nan aka sanar tare da yi musu godiya..

   Dr farida ce tace kinyi kokari walida Amma abubuwan da kika fada sunyi tsauri...

" indai gaskiya kalmace mai tsauri mutane da yawa basu cancanta ayi musu rashin gaskiya ba..

    " Amma yakamata kiyi musu godiya ko?

    Walida ce takarasa gurinsu tayi musu godiya tare da addua.. Gomna ne yace in bazaki damu ba...

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now