Babi na hudu_Maman khady

3.4K 231 6
                                    

KUNDIN HASKE

            Al K'ALUMAN Marubatan HASKE

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
  *MAMAN KHADY*

*ABOKIYAR ZAMA*
(Kishiya)

*BABI NA HUDU*

Shafi na farko

Irin kukan ta datakeyi kai kace mutuwar iyayenta aka gayamata, Abdallah na zaune gefenta yana kallonta tare da lallashin babyn dake hannunshi, yana zaune kusa da ita harta gama kukanta sannan tamika mishi hannunta,shikuma yabata babyn tare da cewa dan Allah bilkisu kiyi hakuri wallahi ina sonki kema kinsani,aure kaddarace daga Allah matukar yana cikin kaddarar mutun to wallahi kobeso saiya yishi,kiyi hakuri bazaki taba canzawa daga zuciyataba insha Allah.

miryarta ashake tace to abban faruok nagode.
  matsawa yayi jikinta sosai tare da rungumeta kusan atare suka sauke ajiyar zuciya.

shekararsu shida da aure Allah yabasu yara biyu umar da kuma amina wacce suke kira da hajiya domin sunan mahaifiyarshice aka saka.
    tun kwanaki yazo mata da maganar yaga wata yarinya yanason ya aureta,tabashi goyon baya dari bisa dari,saidai tunda taji cewa anbashi yarinyar shikenan sai hankalinta yatashi,kunsandai kishi beda dadi musamman akan abinda kakeso.
Tunani tafara waye yakamata tafara fadima wannan damuwa tata,danhaka saita nemi number din kanwar mahaifinta, bayan sun gaisa take gayamata bukarta nason zuwa gareta domin neman shawara.
   karki damu takwarata kizo babu inda zanje yau,Allah yasa lafiya kuke dai?

  Lafiya lau umma zanzo zuwa yamma insha Allah.

Abban farouk zanje wajan umma anjima idan kabani izni?

   kishirya yanzu sai in ajeki,kindaisan bansan tafiyar yamma ko? Idan antaso su farouk zancema usman yakaishi wajan hajiya.

  Sam bata da walwalar kirki domin kuwa shedan yanata kokarin ganin ya cusamata bakin ciki da takaici ita kuma tana kokarin ganin ta yakiceshi.

Da murna umma ta tarbeta,Bayan sun gaisa sai kawai bilkisu ta sakamata kuka hadda sheshsheka domin sai yanzunema take matukar jin kunci cikin zuciyarta,HAJIYA bilkisu ta rungumeta jikinta tare da furtamata kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un,cikin kunnuwanta,nan danan ta farabi itama saida tai kukanta ta gaji sannan ta share hawayenta tagayama umman abinda ke tafe da ita.

Umma tai murmushi kamin tace haba bilkisu me gadon zinare kadda ki badani mana kadda ki karyamin zuciya kefa sunanki kenan kadda ki tozarta masu sunanki matsayinki da  darajarki tafi karfin kitsaya yima kishiya kuka, kiyi hakuri insha Allah babu wata damuwa  akan abokiyar zaman da zaikawimiki nidai kawai shawarar dazan baki itace kadda ki yarda kufara samun sabani akan wannan maganar kowacce mace da halinta zata zauna sannan namiji komai yawan matanshi yana hankalce da halin kowaccensu sabida haka wallahi ahir dinki da biyema sharrin shaidan da makarrabanshi domin yanzune zakiji mutane natacewa zasubaki shawara saidai da wuya kisami wanda zaibaki wadda ta dace.

  kishiyarnan da aketa gudu yakamata ace zuwa yanzu ansaba da itama domin kuwa ai tariga tazama jiki tazama ruwan dare, idan mamanki bata da ita ai yayunki nada ita ko?
   Kuma idan baki mantaba ainima alhaji yatabamin har biyu lokaci guda yanzu ina suke?
   Basu sabida Allah yariga ya rubuta dama bazasuyi dogon zama dasuba duk irin wulakancin da sukaimin na hakura na shanye sunsha yimin duka suyimin taron dangi idan nafadimishi yace karyanake duk zafin kishine da Allah yatashi kamasu saigashi yazo ya tadda suna dukana atsakar gida gaban yarana ina kuka sunayi,Awannan lokacin saida yai kuka sabida takaicin karyatanin da yakeyi dayake bani da hakkinsu nan take duk ya sakesu nikuma yabani hakuri yai wa gari ya waya?
   Bilkisu duk wanda beyi hakuriba to wallahi bazaici ribar zaman duniyaba balle na kiyama.
   Yanzu meke cutar ma auratan wannan zamanin duk bawani abu bane sai rashin hakuri musamman kuma wajan matan kowacce sotakeyi saita samu yanda takeso agidan auranta,Kingako ai wannan bawai abubane me yuwuwa kai ko asiri mace tayi wallahi wataran saita kwashi kashinta ahannu domin ai asirin bazai dawwamaba ko.

Danhaka kiyi hakuri ki jure duk wani abu da zakigani musamman farkon auren insha Allah da ankwana biyu zakiga komai yawuce kinji ko?

To umma nagode sosai insha Allah zanyi kokarin ganin nakare mutuncina dana iyayena da yarana nagode sosai da shawarwarinki gareni.

GIDAN,ABUBAKAR; gidan abubakar kuwa itama dai salma haka maganar take haihuwarta uku duk maza amma kuma Allah yasakama mijinta bukatar aure, yau kwana biyu kenan,ko magana bata hadasu daidai da hakkinshi ta daina bashi tace lallai saidai ya jira amarya tazo ta bashi.

duk irin shawarar da mahaifiyarta take bata kusan abanza domin ta rantse be isa yai wannan aureba saidai idan bata raye,duk kuwa da irin hakurin dayake bata.
   shi tausayima take bashi,ga yara uku sannan kuma ga wani cikin ajikinta.
    tun yana lallashinta harya gaji yafara kyaleta.

Salma zo muyi magana, wani kallon banza taimishi kamin tace kai nifa wallahi ka kyaleni tun kamin inshukamaka rashin mutuncin da saika gwammacema baka aureni.
    Haba salma wai meyasa kike hakane kindaisan ina sonki, sannan ina kaunarki kiduba kiga yaranmu yanda kika daina kulasu sabida wani dalili naki na banza.

    Ni babu wani sona da kakeyi tunda gashinan kana neman kawomin masifa da bala'i to wallahi kasani indai tashin hankaline to yanzu muka farashi.

   Harararta yayi kamin yace kenifa nafara gajiya da wannan banzan surutun naki sannan kuma kina tunanin wannan masifar ta isa ta hanani aurene?
  Tobari kiji wallahi aure babu fashi matukar ina numfashi.

  Gidan Abubakar sam babu kwanciyar hankali kullun cikin masifa da tashin hankali suke sam tahanashi kwanciyar hankali masifae yau daban ta kobe daban.

Takasa tunawa dacewa lallai shi aure hukancine na ubangiji idan yace yafaru lallai saiya faru,sannan masifar mace bata hanashi aikata dukkan abinda da yagadama saima wulakanci da bacin rai lallai mutuncinki zai zube dana iyayenki domin daga lokacin zai fara tunanin lallai bakisami tarbiyyar data daceba.

  To gadai Labarin gida biyu,mun dauko xamu hadu a gida na gaba.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now