Shafi na hudu

1.3K 99 1
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*

  *shafi na hudu*

Murmushi mama tayi tabi sadiya da kallo a zuciyarta take tunanin me wanan yarinyar ke nufi? Wanan wani sabon iskanci ta tsiro dashi koko wani kullin take shirin yi? Tabbas akwai wani abu a kasa domin tunda take da da'nta be taba fita kofar gida ba tare da ya nemi izininta ba ballantana ace yau ya fita batare da ya shigo ya gaishetaba tabdijan lallai sadiya akwai abinda ta taka koma menene allah ya mayar mata da abinta, ta saki sassanyar ajiyar zuciya....

  Sadiya kuwa murna kamar ta taka rawa dan dadi burinta ya cika daga jiya zuwa yau abubakar ya canja ya soma zama nata ballantana jiya yadda ya nuna mata kauna da kulawa, gaskiya tayi wauwta da tun farko batayi wanan kissar ba ta tsaya haukar banza, guntun murmushi tayi lallai a gaida bintu data bata wanan shawarar zama ta danyi tana tunanin yadda zata bullowa abubakar idan ya dawo....

******Abubakar kuwa tunda yaje kasuwa ya kasa sukuni domin babu abinda yake tunani sai mahaifiyarsa da kannensa wanda besamu ya gansu ba dik kewarsu ta dameshi ga wani irin so da kaunar yan uwansa da mahaifiyarsa daya darsu a zuciyarsa,wani tinani ne ya fado masa na idan zai koma gida yau ya kamata ya dan siya musu nama suci suji dadi... Da wanan tunanin ya cigaba da harkokinsa da abokanan kasuwancinsa....

*****sadiya tana zaune a daki ta dafa indomie da kwai ta zuba a plate tanaci tana kallo taji sallamar aminiyarta bintu "Assalamu alaikum"

  Da gudu sadiya ta fito cikin tsananin farin ciki fuskar nan dauke da annuri "oyoyo aminiyata oyoyo"suka rungume juna mama dake cikin daki ta fito tana amsa sallama amma daga sadiya har bintu babu wanda ya kalleta bintu ce rike da hannun sadiya sukai hanyar dakin sadiya har zasu shiga bintu ta waigo ta kalli mama dake tsaye a kofar daki tana kallon ikon allah tace "wai nikam kawata dama ulcer gidanku na nan"

  Dariya sadiya ta fashe dashi ta waiga ta kalli mama sanan tace "ina zataje? Ai tana nan tanasa mana ido dik abinda nayi akan idonta"

"gaskiya kawata kina hakuri "sadiya ta tabe baki tace "yana iya muje daga ciki"suka shige daki....

  Zuciyar mama ba karamin suya takeyi mataba, idanuwanta tamkar zatayi hawaye, karamar yarinya ke kiranta da ulcer? Ciwo fa kenan, kenan sadiya na nufin ita annoba ce kenan, innalillahi wa inna ilaihi rajiun zuciyarta ba karamin tafasa takeyi ba haka nan ta daure tana ambaton sunan allah ta koma daki...

  Ruwan sanyi sadiya takawowa bintu sanan tazo gefenta ta zauna, ruwan bintu ta dauka ta sha sanan ta ajiye kofin ta juyo da kallonta ga sadiya, cikin kasa da murya ta soma magana

"kawata yayadai? Incedai kinyi abinda nace ki gwada kafin musan yadda zaayi?"

Sadiya tayi murmushi tayi farr da ido sanan tace "kedai kawata allah yayi miki albarka samun kawa kamarki a wanan zamanim sai an tona, wallahi nayi yadda kikace kuma naga canji jiya kadai.... Ta kwashe komi ta fadawa bintu yadda sukayi jiya,

  Dariya bintu tayi mai isarta sanan ta tsagaita tace "dama kin tsaya kallon ruwa kwado yayi miki kafa ne? Anfada miki ana zama da suruka ne baa shirya ba? Ke kanki bakisan irin shirin da wanan makirar matar tayi akan abubakar ba yake sonta yake mata biyayya kamar zaiyi mata sujada, da kin tsaya bakin ciki ya kasheki wallahi da baki farga ba da wuri harke zata mallake ta rinka juyaki kamar waina kinaji kina gani"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now