Babi na 19-Safiyya Galadanci

1.7K 132 10
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

*K'AIK'AYI...*

BABI NA GOMA SHA TARA

PAGE 1

Agogo yake kokarin daurawa a hannunsa yana tafiya da sauri hadi da yin tsaki, yanayin saurin da yake kadai zai Nuna ma cewa yana matukar uzurce ne.

Sam baya kaunar rasa huduba a masallacin jumu'a balle har ya rasa sallar jumu'an.
Lokacin da ya samu isa masallacin har ana shirin fara sallar, sai duk yayi dana sanin tsayawa gyaran gemun nan amma hakan ya samo asali ne daga makarar da yayi wurin tashi daga bacci.

*SAIFULLAHI* Kenan tsaftataccen ustaz malami ta fannin addinin musulunci, baki ne shi dogo ba kuma siriri ba, yana Tara sumar kai da kuma saje abinda yake matukar so domin yakan bata lokaci wurin gyaran su.

A kowace jumua daga fitowar alfijir zuwa fitowar rana akalla yakan karanta Izu hudu zuwa biyar sannan ya Dora da suratul kahafi, yakan kashe lokaci wajen gyaran farce da kuma gyaran sumar kansa da saje, a kowace jumua kuma bashida wasu kalar kayan da suka wuce farare sai dai ya surka ta baki ta gefen takalmi da kuma agogo.

Yanayin kyau na halittar jikinsa da kuma fuska sukan boye shekarunsa, a kallo daya bazaka tantance yanada iyali ba.

Matarsa daya Juwairiyya da yara shida, uku maza uku mata, babbar yar sa mace mai sunan mahaifiyarsa Nana khadija,  wacce suke kira da Nana, a halin yanzu Nana ta matakin karshe na kammala babbar sakandire, sai Ahmad Wanda yake jss3 yanzu sai Nana Aisha, kabir, Muhammad da auta ummulkhairi.

Bayan kammala sallar jumuar daga masallaci ya kamo hanyar akan hanyarsa ta komawa gidan idan ya hango mabukata masu bara yakan tsaya domin basu sadaka, bayan ya Isa gida yayi parking mota sai ya lura babu motar dauko yara daga makaranta Dan haka yayi tasamma shiga gida domin yaji ya akayi daga bakin uwar gidan.

Karar bude kofar gate din gidan ce ta dakatar dashi ya juyo yana kallon masu shigowa, a lokacin idonsa ya sauka kan Nana khadija, wacce halittarta ta nuna cikar budurci ta gama bayyana bayan haka kuma uniform din jikinta sun nuna halittar sosai saboda hijabin ma bashida wani girma.

Ke! Ya daka mata tsawa a take dukansu suka natsu,
"Daga ina kuke? Ina sahabin yake kuma".

" Abba wallahi motar ce ta samu matsala shine akaita gyara bata tashi ba se yace mu hau adaidaita sahu mu karaso gida ze biyomu daga baya idan ya dawo daga masallaci".
Yadda take maganar ya nuna cewa a rude take.

"Shine kuka tsaya a bakin titi kuna taron Napep? Dan Allah Ku wuce ciki sakarkaru kawai".

Cike da nutsuwa suka shige gidan Dan yaro yayi garaje yasan sauran.

Tsaki yayi yabi bayansu suna shiga gidan kowa yayi hanyar dakinsa, mahaifin nasu kuma ya nufi inda matarsa, yana tafe yana huci.

Gaban mirror take tana gyara zaman daurinta yazo ya tsaya mata akai yana huci.

Shuru tayi tana kallon kasa batare da tayi magana ba.

"Kinsan lokacin dawowar yaran nan daga makaranta amma baki gansu ba kuma kin tsaya kina kwalliya a gaban mudubi".

" Abban Nana, ka duba wayarka bansan adadin Kiran dana maka ba, ka kira sahabi kaji lafiya banga yara sun dawo ba amma baka daga wayar ba".
Da daddaya take zaro maganar gudun yin kuskure.

" kinga Nana kuwa? Wai a adaidaita sahu suka dawo, sun tsaya a bakin titi kenan, yarinyar nan tayi girman da za a ringa hanata yin wasu abubuwan".

Shuru tayi bata amsa masa ba seda ya gama ta bashi Hakuri, sosai kuma take mamakin yadda yake tada jijiyoyin wuya idan maganar data shafi Nana khadija ce baya bari ko kadan ta fita, ya hanata rike waya.

Fita yayi ya zauna Palo yana jiran azo a kawo masa abinci.

Mayafinta ta dauka ta yafa tabi bayansa, sai da ta shirya komai a gabansa sannan ta zauna ta zuba musu abinci a plate daya, hakama yaran matan a plate daya mazan ma, suka yi bisimillah suka fara cin abincin, har suka gama babu Wanda yayi magana.

Zama suka yi na minti goma, sannan suka dauko litattafansu suka zauna gaban Abban nasu.

Karatu ne sai da kowa ya biya aka dora masa wani sannan suka tashi.

Khadija a dakinsu ita da Aisha ta kalli aishan dake tsaye gaban mirror tana gyara zaman wandon jeans dake jikinta tace, "wai dazu bakiga abinda Abba yayi mana ba? Se kace mu muka lalata motar".

Aisha ta tabe baki tace, "kullum Abba se yayi mana fada, musamman ke bansan meyasa yake yi miki haka ba, kiji wai jiya za aje bikin matar uncle Habeeb yace kar aje dake".

Nana ta dad'a tsuke fuska tace "cewa yake na girma yanzu bazan ringa fita yawo ba sedai ayita kulleni cikin gida, wallahi ranar Hauwa taji haushi da banje birthday party dinta ba".

Aisha tayi dariya tace " kema dai ya za ayi kice wai birthday party zaki je? Ko umma bazata barki ba balle Abba".

Tsaki kawai tayi ta kwanta kan gado
Tana jin haushin wannan kulle da babansu yake mata.

Kwance yake kan gado juwairiyya na yi masa tausa tayi gyaran murya.

A hankali yace "inajinki habibaty" duk lokacin da tayi haka yasan da magana a bakin ta.

"Dama akan maganar mai sunan Hajiya ne, sai naga kamar takurar ta mata yawa Kasan yaran zamani yanzu a hankali ake binsu idan muna jansu ajiki munfi sanin halin da suke ciki".

" watarana se Kinyi abu kamar kinsan abinda kike yi sai kuma ki goce, magana daya ce ina nan akan bakana, bazata fita ko ina ita kadai ba in ba tare zaku ba taren ma sai naga dama, idan ta gama secondary school da kaina zan zaba mata miji in mata aure idan taje can sai ya sakata makaranta taci gaba idan yana da ra'ayi".

Dole tayi murmushin yake tace "babu komai Abban Nana Allah ya kaimu lokacin ya kuma ida nufi".

Can kasan murya ya amsa yana cewa " ameen".

Ci gaba tayi da masa tausar tana tunanin hali irin nasa, har koda yaushe bazai taba sauraren shawararta ba, duk kuwa da irin tarin halaccin da tayi masa a rayuwa, ta tabbata a matan zamanin nan babu Macen da zata iya zama da Saifullahi, ita ma kanta hakuri take yi tana kara tausayin kanta da kuma yaranta.

Ranar Monday tunda sukayi sallar asuba babu Wanda ya kwanta a cikinsu seda suka zo wurin mahaifinsu ya biya musu karatu sannan kowa ya kama aikin dake kansa bayan sun gama sukayi shirin makaranta, abin mamaki an canza musu sabuwar mota da za a ringa kaisu makaranta.

Window Saifullahi ya leko ya kalli Nana dake shirin shiga mota yace.
"Nana ki dawo gida, ban fada miki zan canza miki makaranta ba ko?"

Shuru tayi tana kallon kasa hawaye na zuba daga idonta.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now