Shafi na biyar

1.5K 144 6
                                    

*KUNDIN HASKE*

  AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.

K'UNGIYAR:-
   HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

TAREDA AL-KALAMIN🖋
Zaynab bawa (zeeyybawa)
            
   TALLACE-TALLACE
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA BIYAR*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

    Umma ma ta shirya zaf tana jiran isowarsa domin tasan a ko'ina yake ahalin yanzu yana shirin zuwa domin jin amsa daga bakinta, kuma akowani irin lokaci zai iya isowa."

  Da yamma lik'is umma tana zaune itada humaira a cikin gida, humaira tana qarawa mahaifiyarta wani littafi wanda yanzu shine sukeyi a islamiyya,

Sallama yaro yayi ta amsa masa tana fad'in shigo daga ciki,

Shigowa yayi ya tsugunna gaban umma ya gaidata sannan yadubi humaira yace" yaya humaira ina wuni?"

Lpy ta amsa da fara'arta,

Juyawa yayi ga umma yace" umma  malam yahaya yana sallama dake awaje,

Toh! toh! Madallah ya'isone?"

Juya kace masa ina zuwa,

Miqewa yaron yayi yafice domin fad'in aikarda aka aikeshi,

Tsugunawa yayi gabansa yace" mlm tana zuwa yanzu,

Toh ngd Allah yayi albarka ameen yaron ya amsa had'eda miqewa yayi tafiyarsa abunsa,

Hijabi kawai umma tad'auka tasanya,

Sannan tafita da tabarma a hannunta sanda ta shimfid'e tabarman sannan kuma ta tsaya bakin qofa tace bismillah ka shigo,

Da sallama yashigo ta amsa masa cikin fara'a tace" ga waje nan zauna,

Ganin fara'arda take fuskarsa yanuna masa cewa anyi nasara duk da kasancewar baiji wata kalma daga bakintaba,

Zama yayi can qarshen tabarman itama tazauna d'aya gefen,

Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa yana tambayarta yaya gida yaya yaran,

Lpy qlau Alhmdllhy tabashi amsa,

Toh dama yaune ranar jin amsa tacika toh shine nayi tattaki nazoni domin jin amsar abunda ya sauwaka,

Toh dafarko dai gaskiya kamar yanda kafad'a abayan muba yara bane, bakuma zamu tsaya wasa ba,

Nidai tanawa wajan na amince Allah ya sanya mana alkhairi,

Sannan kuma na sanarda magabatana suma sun amince yanzu komai yarage daga gareka,

Toh wannan haka yake ngd nakuma ji dad'i in sha Allah za'ayi duk wani abunda ya dace,

Amma fa sai dai banason abun yaja lokaci dan banki a kaishi nanda sati d'aya ba bawasa zamu tsayaba bakuma wani dogon nemaba tunda kin fahimceni nima na fahimceki komai sai ayishi akan lokaci,

Banki takaba mlm amma kuma sati d'ayakam ai yayi gaggawa inama ace sati biyu kafin lokacin aii nagama shiryawa,

Eh toh hakanma kinada gaskiya amma kuma zan bukaci ad'aura auren nanda sati d'ayan idan yaso saina baki ishesshen lokaci kafin tarewa,

Saiki gama shirye shiryenki ahankali,

Sannan maganar kayan d'aki kuma nad'auka zanyi miki komai,

Aa mlm baza'ayi hakaba,

Ai wannan hakkinane nayi kayan d'akina dakaina,

Ai toh wannan al'adace ba addiniba,

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now