16

1.6K 146 23
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *Al-K'aluman* *Marubuta*

    KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

     *BABI NA GOMA SHA BIYAR*

      *KWAD'AYIN WASU IYAYEN.......*

       _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

              1⃣6⃣

Yak'are mgn cikin fusata yayinda Ruk'ayyah ta d'ago idanunta dake tsiyayan hawaye , cikeda tsanansa da matsanancin fushi take fad'in

"Cikin jikina na zab'a kamal amma yakamata kasanar dani manufanka abayyane, domin insamu shaidan kaiwa iyayena , suka sakamakon KWAD'AYIN su daya jefani cikin wannan masifan danake ciki "

Kukane yaci k'arfinta tanaji badon tsoran Allah da gudun sabama saba data zubda cikin kodan tsanan datakema wanda yazama silan samuwan sa, sai dai zuciyanta na tsoran aikata hakan batasani ba ko iyakan rabonta ne wannan d'in

"Ina nufin idn bazaki yadda azubda cikin ba kije dashi gdn ku kiraineshi acan , na sakeki saki biyu bana bukatan ganinki da d'auke da abnd ban shirya amsan saba "

Kamal yayi mgn tareda ficewa cikin fishi tamkar zai tashi sama, a falon k'asa yasamu Dr. Rayyan zaune batare daya kalleshiba ya wucesa yai waje , ganin hakan yasa yarufama kamal d'in baya wanda harya kunna motarsa , yaja aguje kaman zai tashi sama megadi ya bud'e mai gate yafice ,Dr. Rayyan ma motarsa yashiga yabar gdn yana Allah wadai da halin kamal tareda tausayin Ruky shikenan ya cuci yarinyan mutane yasaketa da k'aramin ciki ga k'arancin shekaru .......

Ruk'ayyah kuwa anan falon ta zube tana kuka , zuciyanta zafi yake tamakar tacireshi tahuta haka takeji , bataji harta koma ga Allah bazata tab'a tsanan wata halitta kaman yadda ta tsani kamal Alqasim ba , ahankali ta mike jiri na d'ibanta da taimakon dafa bango da kujerun falon takai kanta d'akin ta , wayan ta ta d'auka takira Nadeeya

Bugu biyu ana uku Nadeeya ta d'aga wayan da sallama

"Ya Nadeeya kitaimaka kizo kutafi dani nima yau nawa auren yak'are , kuzo ina cikin halin dabazan iya kawo kaina gd ba "

Ruky tayi mgn tana kuka tareda datse layin tabar Nadeeya da d'aukan salati wanda harya janyo hankalin ummah Mariya dake can nesa da ita tana gyaran farce ta waiwayo tana tambayanta

"Lfy Nadeeya irin wannan salati haka meya faru ne? "

"Ummah Ruky ce takirani wai tana cikin wani hali aje ataho da ita , nihar jinayi ma tana fad'in itama ko aurenta yak'are... "

"Innalillahi wainnailaihirraju'un"

Abnd ummah Mariya ta furta kenan tana cigaba da fad'in " subhanallah ni Mariya me kuma yafaru ? Bari kigani insanar da Abban naku ya kariso da wuri muje mugani, karkiyi saurin kiran Habeeba don Allah "

"To ummah "
Nadeeya ta fad'i jikinta na matuk'ar rawa hankalinta yatashi dajin yadda muryan Ruk'ayyah yake burinta kawai su isa taga halin da take ciki

Koda aka kira Abba Mahmud cikin sa'a yana dabda karisowa gd ma hakan yasa ko shigo da motarsa baiyiba yakirasu awaya su fito kawai su wuce

Har rige-rigen shiga gdn suke tsakanin Nadeeya da ummah Mariya ake byn sun kariso, jin shiru afalon k'asan yasasu haurawa sama karo nafarko da Nadeeya tasoma tako gdn Ruk'ayyah kenan, tsananin bata cikin nutsuwanta baima sa tabi takan tak'arewa komi kallo ba

Sheshshek'ar kukan dasuke jiyowane yasa suka nufi kofan dasuke zaton nan ne Ruk'ayyah ke ciki , a durkushe suka sameta tayi amai takasa ma motsawa daga wajen idanunta sun kunbura sbd kuka , gaba d'aya tasake zabgewa tayi wani irin fari tamkar babu jini ajikinta

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now