Shafi na biyar

2K 214 16
                                    

KUNDIN HASKE

AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE

HASKE WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA SHA BIYU

*MUTUNCIN MACE........*

*TARE DA ALQALAMIN....*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


          0⃣5⃣

     Har suka isa bakin motarshi bai waiwayo ya dubeta ba,yayin da ita kuma take ci gaba da binshi,yana niyyar bud'e murfin motar wayarshi ta sake tsuwwa,ya fasa abinda yayi niyya ya saka hannunashi a aljihun gaban rigarsa ya fito da wayar yana duba mai kiran,karawa yayi a kunnensa bayan yayi sallama
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" kawai yake maimaitawa babu adadi,wanda ambatarta ya sanya gaban badariyya mummunar fad'uwa,cikin zafin nama ya bud'e motar ya shiga ya tadata,tana niyyar bud'ewa don itama ta shiga saidai tuni ya figeta ya fita daga harabar station d'i n.

    Baki ta saki galala tana bin motar da kallo,sai data gaji da tsaiwa don kanta sannan ta taka ta fice zuwa bakin titi,tana tunanin yadda zata kai kanta gida bayan bata dako qwandala,daga bisani ta yanke shawarar ta d'auki shata har qofar gida idan sun isa ta shiga ta biyashi kud'in,tun cikin adaidaitan tunani yaqi barinta,jinta take baki d'aya a muzance,da wannan tunanin suka isa gida.

      Da fari ta zaci ko qwaqwalwarta ce ko idanunta suja samu matsala,ganin cikin k'an k'anin lokaci gidan nata yana neman tashi daga sunan gida izuwa sunan kufai,ga mutane d'ai d'aiku tsaye gaban gidan da alama suna tattaunawa ne kan sauyin da gidan ya samu cikin lokaci q'anq'ani haka,sauka tayi daga adaidaitan cikin d'imuwa ta isa gaban gidan tana qare masa kallo kamar wata shashasha,ciki ta shige kai tsaye ba tare data tsaya sauraren maganar da mazan dake tsaye waje suka mata ba,mutum baifi uku ta tarar a ciki ba suna qarasa kashe inda baiji ruwa ba,ta kalli gabas da yamma kudu da arewa na gidan,sai kawai ta d'ora hannu akanta ta kurma ihu tana kiran
"Wayyo Allah na shiga uku na,ina husna ina khairat,ya Allah ka taimakeni" ta ambata tana ci gaba da kururuwa wadda ita ta assasa soma shigowar mutane cikin gidan,soma bata baki wasu suka soma yi suna lallashinta,saidai sam bata jin me suke fad'a,a zauce ta miqe ta fice daga gidan ta fad'a gidan maman rahama,sam ta mance da batun wani mai adaidaita da kud'insa,shima ganin halin data tsinci gidanta sai ya gyad'a kai kawai ya burga babur d'insa ya bar layin yana fad'in
"Allah ya kyauta,ya kiyaye gaba".

       Sauran k'annenta ta taras a gidan cikin matuqar mutuwar jiki na halin da suka ga khairat a ciki,tambayarsu ta hauyi maman rahaman suka shaida mata sun tafi asibiti kai khairat ita da abban rahama,kuka ne ya b'arke mata
"Me ya samu khairat d'in?,kaddai ace gobarar ta sameta?" Kai kawai suka iya d'aga mata
"Na shiga uku na lalace khairat d'ina,wanne asibiti ne?" Nan suka shaida mata asibitin,sai ta kwasa zaya fice,dakatawa tayi saboda tunowa da tayi da husna
"Husna fa?" Ta tambayesu
"Bata cikin gidan gaskiya don bamu ganta ba" tsoro da fata suka had'u cikin ranta,fatan Allah yasa ita ta tsallake da kuma tsoron ina take?.

      Gida gida haka ta dinga bi neman husnan,saidai babu wanda ya ganta yau d'in baki d'aya,haka ta d'ebe lokaci mai tsaho tana nemanta layi bayan layi amma ba'a samu wanda ya ganta ba,daga k'arshe ta yanke shawarar tafiya asibiti wajen khairat.

     Tsaye yake gaban gadon tunda yazo asibitin,tuni idanunsa suka jina da sauya kala cikin d'imbin b'acin rai zalla baqinciki da kuma tausayin yarinyar dake kwance,baki d'aya jikinta lullube yake da bandaji,baka iya ganin kamai nata sai k'ofofin hanci dana idanuwanta,tunda yazo asibitin babu abinda ya iya yi,kafin isowar nashi abban rahama ya riga daya gama komai dama,bayan ya iso ya jajanta masa sannan suka koma gida shi da maman rahaman da niyyar taje tayi abinci ta kawo,ko sau d'aya bai d'aga kai ya dubi badariyya data shigo tana rusar kukar ba,ta jima zaune kusa da yarinyar tana rusar kuka wadda zuwa yanzu idanuwan khairat d'in a rufe yake numfashi kawai take fitarwa,bata ma san wainar da ake toyawa ba,bai k'aunar ganinta ko misk'ala zarratin,tsantsar tsanarta da haushinta kawai ke zagaya jiki da jininsa,yana jin kaman ya tashi ya shak'eta ko zai rage jin radad'i da ciwon da zuciyarsa ke masa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now