3

1.3K 112 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *Al-k'aluman* *Marubuta*

    KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

     *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

   *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN.....*

   _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

             0⃣3⃣

"Ruk'ayyah kitashi kibud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni, duk wannan kukan da kikeyi bashi zaisa afasa aurenki da Kamal ba domin shine yafi dacewa da rayuwanki, Allah yabaki kyau da dirin jiki wanda kallo d'aya za'aimiki asan ked'in matar manya ce ,Kamal shine yadace da rayuwanki ba d'an gdn me waina ba wanda badon yafara samun rufin asiry ba dayanzu mahaifiyansa nanan nacigaba da zama abakin murhu , to kisani nan da kwanaki shida kacal za'a sanya ranan auranki da Kamal kuma sati hud'u kacal za'a saka , don haka kisama rayuwan ki salama ki rungumi arxiki kibar tsiya . "

Umma tadasa aya tana me sakin kafad'un Ruky , wacce ta sake zubewa bisa katifarsu tasaki sabon kuka mai motsa zuciyan me saurarenta , kirjin ta namata wani irin zafi da k'una jitake tamkar numfashinta zai d'aukene , ahankali takai hannu tadafe saitin zuciyanta tanajin yadda yake bugawa tamkar zai rabe gida biyu, itako umma ko ajikinta haka ta tsallake Ruky tafice tana mai jan dogon tsaki

Batayi ko mintuna biyar da fitaba Ruk'ayya tafara jiyo muryan Nadeeya , alamun tadawo daga tafiyan datayi zuwa gdn Anty Maryam wacce takasance qanwar umman su ce , sallama Nadee tayi ad'akinsu bayan tasanar da umma dawowanta tunda tasanya kanta cikin d'akin kukan da Ruk'ayya takeyi ya cika kunnuwanta , cikin saury ta aje jakar kayanta da hand bag d'inta tanufeta tana tambayar

"My sisi lafiyanki kuwa  meya faru ?"

Ruk'ayya tasake sakin wani sabon kukan yayinda Nadeeya ta zauna tareda d'aura kan Ruky bisa cinyarta , tana matuk'ar k'aunan Ruky  domin itace kad'ai jininta da bata da tamkarta aduniya kasancewansu mutum biyu kacal da iyayensu suka mallaka, hannu tasa tana shafa bayan Ruky alamun rarrashi ahankali tafara rage sautin kukan ta hartayi shiru tana sauke ajiyan zuciya , sam Nadee bata damu da Ruky tabata amsar tambayan datai mata ba burinta kukan ya tsaya tasamu sauk'in rad'ad'in datakeji azuciyanta

Shiru d'akin ya d'auka tsayin wasu mintuna kafin Ruky Turaki ta d'aga idanunta ta d'aurashi akan fuskar yayarta Nadeeya , wacce idanunta itama nakan Ruky tana maijin tsananin tausayin yadda KWAD'AYIN IYAYENSU  ke neman yajefa rayuwanta cikin kunci, muryan Ruky ne cikin disasassar muryan ta yakatse tunanin Nadee inda take fad'in

"Ya Nadee meyasa umma bazataji tausayina ba ? Meyasa amatsayinta ta mahaifiya takasa fahimtata bare tabani goyan bayan dazan mallaki abnd yafi dacewa da rayuwata? Wlh ya Nadee Kamal baidace dani ba Kamal bai kamata yazama abokin rayuwata ke kanki shaidace domin aduk lbryn sa da muka samu baya cikin jerin natsatstsun samarin da zakayi alfahary yazama mijin aurenka , Kamal duk wani shashanci da alfasha yana yi shaye-shaye kawai nasan bayayi, Kamal mazinacine bai damu da sallah ba baya ganin girman ko bare sanin mutuncin nagaba dashi , meyasa Abba duk yasan wannan amma shida umma suka dage saina aureshi sbd kawai KWAD'AYIN  abnd yake wadata su dashi , Nadee Kamal bani yakeso ba jikina yakeso kyawun da Allah yabani ke rud'insa , don me baza'a barni na aury mutumin dakemin so na tsakani da Allah ba ? Wlh idn na aury Kamal rayuwata ce zata lalace kitaimakeni ya Nadee kisamamin mafit......."

Wani sabon kukan ne yaci karfin ta harta kasa cigaba da mgn , tsananin tausayinta da kalamanta suka taru suka karya zuciyan Nadee har itama taji wasu zafafan hawaye nabin kumatunta , ahankali takai hannu tashare su tana mai aro jarumta domin kwantar da zuciyan Ruky , cikin sanyin murya take fad'in

"Mafita d'aya ce Ruky shine kisake tsayawa akan addu'a, shid'in wani babban makamine , tabbas Ahmad shine mutumin daya dace dake , shine masoyi nagary me k'aunarki da gsky tabbas KWAD'AYIN IYAYENMU ne kawai yarufe idanunsu suka zab'i Kamal sbd shi d'an gdn arzikine , sun manta cewa shima Ahmad baicire rai da rabo ba , wlh Ruk'ayya nafara gajiya da wannan rayuwan da iyayena , kiduba kiga yadda KWAD'AYIN su yasa suketa koremin samarina, duk wanda yazo yana sona da aure komin rufin asirinsa saisu Abba sun kushesa , shin wai lallai ne saimunyi aure a gdn arziki? alhali mud'in bakowa bane face masu rufin asiry , tun samarin na gary na zuwa yanzu ga yaran masu shid'in sunfara samuwa amma duk babu na kirki , duk wanda zaizo jikinka yakeso iskanci ke kawosa ba aure ba , yanzu kiduba irin rawan jikin da Aliyu keyi akaina amma wlh bani yakeso ba jikina yakeso , burinsa duk in mun had'u yatab'a jikina tun bana bashi dama harya fara cin galaba akaina sbd aure nakeso Ruky kuma shi kad'ai ne ayanzu tsayayyan dayake min mgn aure su Abba sun koremin masu mutuncin , sam basu damu da nagartan wanda suke zuwa garemu ba indai zasuji kud'i a aljifansu , asauke musu kayan arziki na banza wannan wace irin rayuwace ?  Ruky dole sai munyi hakury domin bamu yi dace da iyayen da suke duba nagarta da mutuncin inda zasu kaimu ba sunfi duba gurin kud'i da maik'o. "

Nadeeya takare mgn tana sake kankame qanwarta suka saki kuka mai ban tausayi, dukkanin su ciwo d'aya kedamunsu azukatansu , saida sukayi me isansu kafin su saki juna suna mai tausayama kawunansu tareda Allah wadai da KWAD'AYIN IYAYENSU  dake nema ya rusa musu rayuwa, kiran sallan magriba da akayi yasa Ruk'ayya tafara mik'ewa da kyar idanunta da kirjinta sun mata mugun nauyi sbd tsantsar damuwa datake ciki, saida tayi wanka da ruwa me zafi domin tasamu saukin nauyin da jikinta yayi kafin ta fito d'aure da alwala,

Koda ta idar da sallan bata tashi ba harsai data jira aka kirayi isha'i ta gabatar , kafin ta d'aura da shafa'i da wutiri wayan ta tajanyo tana kiran line d'in Ahmad amma ana sanar da ita not reachable hakan yasake dagula lissafinta matuk'a

Dawowan Abban su yasa itada Nadee suka fice zuwa falon umman su inda duk dare ka'idane anan suke cin abncin tare gaba d'ayansu , koda suka shiga babu kowa afalon hakan yasa Ruky kwanciya bisa kujera tareda lumshe idanunta , sam ko kad'an batama sha'awan sama cikin komi ta fito ne kawai domin hakan shine rufin asirinta daga fad'an dazatasha agurin iyayen nasu

Umma ce tafara fitowa sai Abba nan suka gaidashi tare da masa sannu da zuwa , ya amsa cikin sakin fuska da k'aunar yaran nasa da kullum yake alfahary da haihuwansu , ya sauke idanunsa akan Ruk'ayya wacce idanunta suka kunbura sbd kukan datasha , sai dai baice komi ba ya nufi kusa da ummansu ya zauna yayinda Ruky data kasance k'arama ta mike domin shinfid'a musu abnd suke cin abinci akai , ta jera komi yadda yadace kafin su zazzauna tuwo ne akayi na shinkafa miyan ganye wanda yaji nama da k'ashi sai qamshi ketashi , duk kowa yayi nisa acin abncin amma banda Ruk'ayya wacce tunda tayi loma uku taketa wasa da tuwan ahannunta , Nadee duk tana kula da ita tana sake jin tausayin qanwarta ahankali shima Abba ya kula da Ruky batacin abncin hakan yasa yaciri murya yana fad'in

"Ruk'ayyatu na kardai har yanzu baki hakura da mgn wancan yaron ba , inasha tuni shafinsa ya riga ya kulle ko umman ku bata sanar miki ranan sati zaa sanya ranan auranki da yaron Alhaji Alqasim ba, yakamata kifitar damu kunya kibarmu murab'i tarin arzikin dake tunkaromu kinji d'iyata ina me tabbatar miki bazakiyi dana sanin auren kamal ba , duk wasu munanan halinsa dakikeji ana fad'i sharrin magautane da masu hassada don haka kidaina damu kinji Ruk'ayya ta . "

Abba yakare mgn yana washe baki yayinda Ruky ta saukar da kanta kasa tuni hawayen takaici suka wanke fuskanta , hakan yasa ahankali ta zame hannunta daga plate d'in ta fice batare data iya cewa komiba

Dukkaninsu binta da kallo sukayi sosai tausayinta yasake kama Nadeeya, shikansa Abba da umman sunajin tausayin yadda rayuwan Rukyn ke cikin kunci tunda akafara mgn aurenta da Kamal , suna kuma sane da irin soyayya da shak'uwan dake tsakaninta da Ahmad sai KWAD'AYIN irin gdn arzikin dazata shiga harsuma su saka ran samun nasu kason shike danne duk wani tausayinta da sukeji aransu .

*Ayshat D'ansabo ce*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now