9

1.2K 129 10
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 9

Sai da suka kwana suka wuni da shi a asibiti saboda jininsa da ya hau sannan suka dawo, yaran a gida suka kwana suka dai dan babu Wanda yasan bashida lafiya Aisha zata iya yi musu girki mazan kuma zasu iya gyara gida, matsalar tunda abin nan ya faru ba koda yaushe suke zuwa makaranta ba.

Sai washe gari da safe suka dawo gida dan yace baya son zama asibitin nan yafison a sallame shi ya koma gida, amma da suka dawo sai ya langwabe kamar baiji sauki ba, juwairiyya kuma hankalinta duk ya tashi tana zaune kusa da shi shikuma yana kwance kamar mai bacci yace, "ki duba sunan Garbu a wayata pls yazo ya cire waccen barnar Malam yamin" kadan tayi murmushi ta dauko wayar tayi dialing numbern yana dagawa
Ta kara masa a kunne suka yi magana.

Malam yaji dadin yadda da juwairiyya tayi ta zauna da auren Saifullahi, dama yana tunanin indai ta bar Saifullahi to akwai babbar Marsala, tun daga hakurin da tayi na zama dashi yasan babu wata mace da zata iya wannan sai ita kuma bayaso taga kamar yana tauye mata hakki shiyasa baya wasa da damar ta.

Tsayawa tayi tana kallon tarkacen ledodin dake kasan dakin, Capet ce ja a shimfide sai katifa mai dan tudu a gefe da karamin fridge, ko wurinda zata saka kayanta babu, a hankali ta soma tsince ledodin dake kasa sai taga wasu daga ciki ba ayi amfani da abinda ke ciki ba, dubawa tayi batasan ko meye ba sai ta karanta rubutun dake jiki, jefar da abun tayi cike da kyankyami ta kalli katifar, tsaki tayi sannan ta fita waje ta samo wata wahalalliyar tsintsiya ta share dakin ta cire zanin gadon dake kan katifar, kayanta ta ninke su da kyau ta shimfida zani gefen katifar ta dorasu akai, kwalin dake gefen fridge ta dauka indomie guda daya ta rage a ciki ta dorata kan fridge din sai ta zuba inners dinta ciki.

Sai da ta kwanta tunanin rayuwarta yazo mata, tayi kuka har ta gode Allah, ga ciwon da taji a kafa saboda ba a gyara ya soma damunta, hakanan bacci ya dauketa sai Safiya ta farka toilet din tsakar gidan na gargajiya tasa ruwa ta share tana tunanin yadda zata samu sauran kayan amfaninta ko sabulun wanki batada balle na wanka. Ruwan sanyi ta watsa tayi alwala sannan tayi sallah.

Tun daga wannan ranar ta fita hayyacinta, kabir ko tunda yayi sabuwar amarya har ga Allah ya manta da wata mutum a gidan.

Yunwa kuwa ta kulla aminta da ita dan batasan ta inda zata bi ta samu abinci ba, yau dataga alamar zata kashe kanta ne sai ta shiga cikin gidan  ta samu wasila zaune a palo da kabir suna soyayyar su basu ganta ba har ta shiga kitchen, sauran abincin da suka rage ta dauka ta zauna tana ci, wasila data shigo daukarwa kabir ruwa ta ganta ta tsorata dan ita bata taba sanin tana rayuwa da wata acikin gidan ba, ihu tayi ta koma Palon da gudu tana Kiran kabir yazo ya gani.
Koda yaje ya samu khadija a tsugune tana sude plate din abincin, ya kalli wasila yace "haba sweety wai baki Santa ba? Khadija ce fa uwar gidanki, amma dole ki tsorata bari na fitar miki da ita" mamaki ya kama khadija ta zuba musu ido tana kallon su, hannunta ya rike ya kaita tsakar gida yace "karki sake shigowa nan se idan ni na nemeki ko wasila" hawaye suka zubo daga idonta tace "Dan Allah ka kaini inda Ummi" saida ya harareta sannan yace "uwar taki da ubanki suna sonki suka kawo ki nan? Karki gayamin maganar banza in kakkarya ki mahaukaciya kawai" yana gama fadar haka ya koma cikin gida ya samu wasila na fushi saboda ya rike hannun khadija saida yayi lallashinta.

Tofa! Idan yasa kafa yabar gidan sai wasila ta janyota tasata aikin gidan kuma tayi mata barazanar idan batayi ba sai ta fadawa kabir yayi mata duka dan shi yace ta ringa kiranta tana sakata aikin gidan, wasa-wasa har wankin kayan wasila khadija ce gashi bata saba ba saboda mugunta har zannuwan gado take bata ta wanke.

Tunda Aisha ta tashi take kuka yau hankalin juwairiyya ya tashi, sai ta tambayeta meya faru tace "ummi Nana tunda aka kaita bansake ganinta ba, yanzu nayi mafarkin wai ta mutu" dukda tasan mafarki ba gaskiya bane saida gabanta ya fadi tacewa Aisha "to kiyi hakuri ai mafarki ba gaskiya bane insha Allahu tana nan lafiya, barin fadawa Abbanku ya kaiku kuganta yau ko hankalinki zai kwanta " gyada mata kai Aisha tayi sannan ta fita.

Abbansu yakalli juwairiyya yace "to harke dauko mayafinki muje sai mu barsu can har yamma amma banda Ahmad" duk da tana jin kunya amma tasan ko ita taba son ganin yar ta dan haka ta shirya suka tafi.
Daga waje Saifullahi ya tsaya yace su shiga idan zasu fito sai su taho da khadijan su gaisa bazai shiga ba.

Sunkai minti biyar suna buga kofa sannan aka bude. Wasila sai taga kamar ta sansu dan haka ta basu hanya suka shiga, bayan sun zauna suka gaisa sai juwairiyya tace "khadija fa? dan kira mana ita" sai a lokacin ta gano yan gidansu khadija ta yamutsa fuska tace "khadija tana dakinta can tsakar gida daga haka ta shige dakinta ta rufo kofa.

Shuru juwairiyya tayi sannan ta kalli Aisha tace "Kodai ba nan bane"? Ahmad yace " ummi bari dai Aisha ta duba tsakar gidan" hanyar da wasila ta nuna nan Aisha ta bi ta fita tsakar gidan, kaya ta gani jibge a tsakar gidan ga wata mata a kwance gefenta da roba babba da alama wanki take yi.

Khadija jin motsin mutum yasa ta dago sukayi ido hudu da Aisha.
Da sauri Aisha ta matsa kusa da ita ta rikota tana kuka tace "innalillahi Nana meya sameki? Me kike yi haka? Ummii!" Ta kwallawa umminsu kira, juwairiyya taji muryar Aisha kamar tana kuka tana Kiran ta, sai suka zo tsakar gidan da sauri ita da sauran yaran, ganin abinda Aisha kewa kuka yasa ta kasa yin kukan ma, hijabinta ta cire ta ta dago khadija suka kama mata ta dorata a bayanta suka fito harabar gidan.

Suna fitowa sukaji ance "kai" kabir ne ya leko sai Ahmad yaje ya tsaya yana kallonshi ya mikawa Ahmad takarda ya koma ciki, Ashe banzan yana nan cikin gidan lokacin da suka zo, wasila ta kara zuga shi shine ya rubuta takardar sakin khadija.

Saida juwairiyya ta kwantar da ita baya sannan ta kalli Ahmad da khadija tace "wani ya Dora kanta a cinya wani ya Dora kafa motar bazata daukemu ba na zauna gaba da sauran yaran"

Saifullahi yayi shuru ya dafe kansa baice komai ba ya kunna mota suka tafi, sai lokacin Ahmad ya lura da kumburin kafar khadija tayi.

Direct suka wuce da ita asibiti aka duba ta lafiya lau take saidai yunwa da kuma ciwon da taji a kafa.

Basu kwanta ba bayan an rubuta mata magunguna suka koma gida.
Saifullahi ganin abin yake kamar film.

Washe gari da sassafe ya aika yara gidan da mota biyu akwashe kayan khadija sai aka kirashi akace gidan a rufe yake, yace su balla kofar, babu bata lokaci sukayi yadda yace.

Sai yamma kabir da wasila suka dawo daga ziyarar da suka tafi yau, daya ga abinda ya faru gidan hankalinsa ya tashi yace, "barayi sun shigo gidan nan, shiyasa bana son ana fita abarmin gida ba kowa" ya soma hauka dan gidan ko cokali ba a bari ba.
Wasila tafishi shiga tashin hankali dan tasan sedai ta mutu gidansu bazata samu ko gado daya ba balle har gado uku.

Zama yayi ya kira babansu yana cewa "wallahi baba mun fita ne tun safe yanzu mundawo gidan bakomai an balla kofa an shiga ankwashe komai ko cokali ba a barmana ba" babansu yayi murmushi yace "kabir kenan, masu Abu dai sun aiko ankwashe musu kayansu dama saboda yarsu suka kawo kayan ka koreta me kayanta zasuyi a gidanka"?

Shuru kabir yayi danshi ya manta da kayan khadija ne, baba ya katse masa tunani da cewa " ka kwashe sauran tarkacenka ka barmin gida kafin gobe"
Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa, dan yayi alkawarin sai kabir ya dandana kudarsa sakamakon zubar masa da mutunci da yayi ya kaskantar da yar mutane.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now