Shafi na uku

1.6K 135 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

*Haske Writer's Association*💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

   *RAYUWAR WASU MA'AURATA...*

  *NA*

*UMMU BASHEER*

*Babi na goma sha uku*

Page 3





.....Wani irin ihu ta saki lokacin da taji an watsa Mata  ruwan sanyi,  a firgice ta tashi. Ganin shi a tsaye rike da bottle water ya tsorata ta. 

Fuska a daure yace " Dan uban ki barci kika zo yi gidan nan. "

Tashi tayi tana tsane rigar ta " A'a kayi hakuri Safwan Dan Allah "

Buge Mata baki yayi har sai da yayi jini.  A rud'e take son yin ihu.

Yasa yatsan shi kan lips dinshi alamar tayi shiru.

Shiru tayi yayin da hawaye ke zubo Mata.

"Wuce kije ki kawo min abinci " Yana fadin haka ya koma parlour.

Ko Kayan bata tsaya cirewa ba domin gudun b'ata lokaci. 
Kitchen ta shiga ta hada abincin a tray ta Kai kan dining table.  Tare da ciro mango juice mai sanyi a fridge ta ajiye.

Cike da ladabi da biyayya ta Isa kusa dashi tace ta Kai.

Sai danna waya yake.  Bai kula ta ba.  Nan ta kara fad'i ai ko a fusace ya dago Kai "Naji ai "

Ita tayi serving nashi abinci.  Sai ta tsaya jiran ya gama domin in Yana cin abinci ka'ida ne ta tsaya har ya gama.

Yana gamawa ta fara kwashe Kayan zuwa kitchen. 

"Ki same ni a daki na" Abinda taji yace kenan .

Sharp sharp ta dan gyara gurin ta koma Dakin ta ta cire Kayan tasa wasu na barci.  Kasancewar dare ne. Sai da ta feshe  jikin ta da turare domin yanzu sai yace tana wari ba karamin aikin Safwan bane.

A hankali ta shiga Dakin.  Ya kashe wuta sai bedside lamp ne kawai a kunne.  Tsayawa tayi nan ko ya daka Mata tsawa.

"Bana son munafurci . Uban me kika tsaya yi anan"

Jiki na rawa ta Isa bed din.  Kafin ta hau ya jata kai.  Tare da kashe lamp din.


Bayan wani lokaci naga ta fito ta koma bedroom dinta.  Kuka kawai naga tana yi.

Alwala tayi tare da yin sallah tana rokon Allah ya kawo Mata sauki cikin al'amuranta.


****************

"Yau ashe babbar bakuwa ne a gidan nawa " cewar Ramla wacce ta taro zee.

Dariya zee tayi.  Suka zube a kujera tare da gaisawa.

Nan fa hira ta barke.  Kasancewar weekend ne zee bata ga Milhan ba. Ta kasa hakuri can dai tace "mutumiyar halan oga baya nan ne? "

Tabe baki tayi "Yana can Dakin shi, yanzu Zaki ga ma ya fito kila yaje Restaurant ya siyo abinci tunda rana tayi "

"Ah haba Restaurant fa kika ce zaije "

"To shi yaga zai iya ai.  Kinga ni abinci bai dame niba.  Yanzu idan nayi yan ciye ciyen Kayan Zaki na sun ishe ni "

Zee tace " to ko in daura mai ne"

Cikin halin ko in kula tace " idan kinga Zaki iya "

Mikewa tsaye tayi "mai zai Hana "

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now