18

2.1K 284 35
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


18

Rufe fuska Fatima ta yi da Hijab ta dinga rera kuka, shi dai bai ce komai ba har ya bar anguwar, parking yyi yana kallonta da mamaki yace "Sannu drammer Queen, ba ma ki da kunya yarinyar nan, haka kawai kin kama yar mutane kin nakada mata duka snn ki xo nan kin cika min kunne da kuka" cire Hijab din tayi a fuska cike da masifa tace "Toh ina ruwanka??" shafa beard dinsa yyi yace "Lallai, Ashe Bruce Lee xan auro gidana" k'in cewa komai tayi, ya wara manyan idanuwansa yace "Kaddai nima haka xa ki je kina dukana idan aka yi auren" nan ma dai ko kallonsa bata yi ba bare ta tanka sa, murmushinsa mai kyau yyi yace "Ita ce kawar taki da ta baki shawarar ki xo gidana knn" murguda baki tayi taki cewa komai ta kara tsuke fuska, dogon hancinta ya ja ta buge hannunsa, ci gaba yyi da driving dinsa, yana kallon titi murya can kasa yace "But ba girman ki bane dambe a titi, you just downgraded me there, ke kika yi damben amma ni naji maki kunya...." a takaice tace "Toh ai ban ce ka xo inda nake ba" ya kalleta ta gefen ido xai yi magana wayarsa ta fara ring, kallon screen din yyi sannan ya daga tare da yin sallama a hankali, ya d'an buda ido yace "Noo, Sorry mum yanxun xan dawo...." Shiru yyi yana sauraren mum din tasa, can ya kalli Fatima a hankli yace "Noo, Fatima na je picking ne, amma kiyi hakuri xan dawo in maki yanxu" ya gyada kai yace "Alryt" sannan ya mika ma Fatima wayar, kallon wayar ta dinga yi murya can kasa yace "Take.... My mother" da kamar baxata karba ba sai kuma a hankali ta sa hannu ta karbi wayar ta kai kunne hade da sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren aka amsa mata, tace "Ina yini Umma" Matar tace "Lafiya lau Fatima, ya ku ke?" Fatima tace "Lafiya lau ya aiki" matar tace "Alhmdllh dear, ya iyayen naki" tace "Suna lafiya" matar tace "Maa sha Allah, Allahu ya sanya albarka, sai ayi ta addu'a kinji" Fatima ta gyada kai tace "Toh nagode" daga haka matar tayi mata sallama ta mika masa wayar, ya amsa ya kai kunne yace "Thanks mum, will be back anytime soon" daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da tukinsa, sai da suka kusa gida yace "Look... Ki saurareni da kyau on a serious note bbu ruwanki da yarinyar can, you just disgraced ur self few minutes ago...." Bata ko juyo ba bare tace komai, yayi parking kofar gidansu yace "Ni dai na gaya maki, if you like pretend u are not hearing, in Allah ya baki sa'a kin doketa daxu next time try that shit xata nakada maki duka ne ba ruwana...." Sai a sannan ta kallesa tace "Mai dukana sai ruwan sama shi ma idan na so kenan, ita din banxa, ai ba ta ga komai ba yanda ka walakanta ni haka ita ma xan walakanta ta don ita ta ja min" buda ido yyi yana kallonta da kyau yace "Walakancin me na maki" tabe baki tayi tace "Bani da lkcn wannan bayanin" ya daga kafada yace "Karkari kice nayi raping dinki koh?" Ji tayi wani takaici ya rufe ta, ya tabe baki yace "Yeah that's just it, kuma auren ki da nake son yi I keep saying wllh taimakon ki xan yi, It will save u d embarrassment on ur 1st nyt" yana fadin haka ya bude motar yace "kinsan me, idan har baki je kinyi wanka da ruwa me xafi ba yanxu ina tausayin abinda xae sameki kafin gobe, ba ke Bruce Lee ba" bude motar tayi tayi wucewarta ko rufe kofar bata yi ba, ya bi ta da kallo yana murmushi. Tun daga wannan rana Fatima bata sake fita ba tana ta xuba ido taga xuwan Husnah gidansu amma shiru shiru har bikinta da Elbasheer ya rage sati daya, a duk kwanakin nan rana daddaya ne Nafisat bata xuwa, kai har suka saba da Elbasheer dake xuwa gidan jefi jefi da yamma, yawanci ma da ita yake labarinsa, nan Nafisah taga Elbasheer is just perfect, kawai dai ta lura ya fiye tsokana ne,  Nafisat mamakin halin Fatima take don har lkcn taki daukar shawarar da take bata don har lkcn taki sakewa da Elbasheer, in dai fatima tasa kanta abu bbu me canxa mata ra'ayi . A cikin satin da ake ta shirin biki Fatima tayi mugun daga hankalinta fiye da baya, abinci ma sai an tilastata take ci, ana jibi biki wani kanin Umar ya kirata, bata ma san shi bane bayan ta daga ya sanar da ita waye, Hijab ta sa ta fita bayan ta dau ixini gun Ammi, gaisawa kawai suka yi ya mika mata envelope wai in ji Umar, ta karba a sanyaye, yyi mata sallama ta koma ciki, tare da Nafisa suka bude Envelope din suka ga kudi ne har dubu Hamsin, duk yanda Fatima ta so danne kukan dake cin ta kasawa tayi, Nafisat ta dau kudin ta kai ma Ammi. Yau juma'ah tun da fatima ta samu labarin an daura aurenta da Elbasheer take kuka, bbu irin lallashin da Nafisa da wasu daga kawayensu basu mata ba amma kamar
Suna d'a d'a tunxurata, sai da wata kawar Ammi tayi da gaske da ita ta hakura da kukan, kafin rana ta dinga jin xaxxabi amma bata yarda an gano hakan ba saboda karfin hali, Walima aka yi har xuwa yamma sannan aka fara shirin tafiya da ita, motoci lafiyayyu hudu aka turo daga Abuja, nasiha sosai frnds din Ammi suka yi mata, ita dai banda kuka bbu abinda take yi har lkcn ta kasa yarda wai yanxu Elbasheer mijinta ne, cike da karfin hali Ammi ta sa mata albarka daga haka aka fita da ita, ita da su Nafisa da Kanwar Abbanta mota daya suka shiga su suka fara yin gaba kafin sauran mutanen da xa su rakata. Har suka isa gidan bata yarda ta bude fuskarta ba duk jikinta a sanyaye, ga faduwar gaba da take ta yi, Anty Maryam ta xaunar da ita gefen gado tace "Maa sha Allah, Allahu yasa gidan xama ne daughter" ita dai bata bude fuskarta ba bare taga irin dakin da aka shigo da ita tana rike da hannun Nafisat gam kamar xata gudu ta bar ta, lkcn magrib nayi su Nafisa suka je alwala da kawayensu, kawar Ammi ce ta sa ta tashi taje tayi alwalan ita ma, sai a snn ta bude mayafinta a hankali, Nafisa ta nuna mata bathroom din, ta mike a sanyaye ta shiga ta dauro alwala ta fito. Karfe takwas duk suka fara shirin tafiya, kuka ta sakar masu a rikice, Anty Maryam da ta saki baki tace "Ji shashanci to kukan na lafiya ne, ko komawa xa mu yi da ke?" cikin rawar murya tace "Anty don Allah kada ku tafi ku bar ni tsoro nake ji" Anty Maryam tace "Toh Nafisa da Rukayya xa su tsaya tare da ke" Sai a sannan hankalinta ya kwanta, nan su Anty Maryam, maman Hafsa da kawayen Ammi gaba daya driver ya wuce da su bayan sun kuma yi mata nasiha me ratsa jiki, ko minti goma ba su yi da wucewa ba wani motan ya shigo gidan, ita dai gabanta sai faduwa yake tana rike da hannun Nafisa, bayan wani lokaci aka bude kofar dakin hade da sallama, Rukayya ce ta fara gaishesa sannan Nafisa, ya amsa masu gaba daya, Nafisa ta kwace hannunta daga na fatima da ta rufe fuska xuciyarta na bugawa ta mike tace "Toh mu xa mu tafi Fatima Allah ya bada xaman lafiya" Rikota Fatima tayi da sauri har lkcn bata yarda ta bude fuska ba cikin rawar murya tace "Wayyo don Allah kar ku tafi ku bar ni ina rokon ku" Nafisa tayi murmushi tace "Kar mu tafi kuma? to sakeni baxa mu tafi ba, sakeni ki ga" kin saketa Fatima tayi ta rushe da kuka, Rukayya da Khadijah suka dinga dariya suka nufi kofa, Elbasheer dake tsaye har lkcn yace masu "Ku jira parlor xa a mayar da ku gida...." Rukayya tace toh sannan suka fita, Ganin ta ki sake Nafisa ya karasa kusa da su fatima na ganin haka ta bar wajen da sauri cikin kuka take cewa "Ni ka kyaleni wllh binsu xan yi" Nafisa tayi kkrin danne dariyarta ta samu ta fita dakin da sauri, jawota yyi jikinsa ya kwantar da ita kan gado yana kanta, mutsu mutsu ta shiga yi a tsorace xata kwace kanta, ya daura lips dinsa kan dogon hancinta yana kallon kwayar idonta, hawaye ta shiga yi, yyi murmushi ya mike ya fita ya kulle kofa ta waje, dubu ashirin ya ba su Nafisa ya ba driver makulli ya mayar da su gida. Bedroom dinsa ya shiga yyi wanka ya fito, ya kusa minti ashirin yana dube dube a laptop kafin ya kashe ya sanya jallabiyarsa ya fita dakin,  A takure ya sameta can karshen gado bacci ya dauketa, ya karasa kusa da ita ya xauna yana kallon ta, hannunta ya kamo a hankali, da sauri ta bude ido ta mike ta warce hannunta, jawota yyi jikinsa ya rungumeta gam, cikin rawar murya tace "Don Allah ka sake ni bana so" lips dinsa ya kai kunnenta ya lumshe ido murya can kasa yace "Billah.... I married you because I love u Fatima"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now