5

2.3K 156 33
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡💡💡

*Wattpad:-Ummishatu*

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA*👌🏻

*BAK'ON YANAYI....!*❤
    (Kafar sadarwa)

*Babi na Ashirin da d'aya (21)*

*Ka guji zubar da mutuncinka akan abunda baida mutunci ko muhimmanci gareka.*

*5*

    ***Cigaba nayi da warware takardar nan nasoma karantawa jiki na rawa wasu hawaye masu dumi kuma na bin kumatu na tamkar anbude fanfo,abunda ke jikin takardar nake sake maimaitawa domin gani nakeyi kamar acikin mafarki nake,saki Abul khair ya rubuta min wai yasake ni saki daya idan aka hada da na baya ya zama biyu kenan idan nasamu miji inyi aure,

Tambayar kaina naketa yi to wai laifin me nayi masa yanzun da ya sakeni? Dama ana yin saki hakane batare da laifin komai ya gifta ba?

Hawayen da nakeyi naci gaba da sharewa ahaka harun yazo ya sameni cikin kidima yake tambaya ta abinda yafaru amma nakasa fada masa saboda ban san ta inda ma zan fara sanar dashi rashin arzikin da yayansa ya yimin ba daga karshe sai takardar ya karba ya duba nan yazauna bayan yayi shiru dan yarasa abinda yake yimasa dadi shima,nidai saida nagama sharbar kukana nagama sannan muka tattara dakyar muka tasamma gidansu innah,zuciya ta babu dadi sannan babu walwala atattare dani haka muka shiga gidan innah sai marhabun lale take yi damu,

Wunin ranar kasa tabuka komai nayi domin hatta abinci nakasa ci araina kuma nayi aniyar tafiya mahaifata gidan iyayena zanje inci gaba da zama tare dasu tunda zawarci ba kaina farau ba kuma inada tabbaccin baza adaina daga kaina ba dan haka da zarar anyi suna zan tattara nawa inawa inyi gaba,

Innah dai da baffa lokacin da harun yasanar dasu abinda Abul khair yayi sun shiga damuwa da fushi mai tsanani dan daga karshe ma sai nida harun ke basu hakuri akan kar suyi fushi dashi hakan zai sake jefashi cikin damuwa da matsala kawai suyi masa addu'a tunda addu'ar iyaye bata faduwa kasa banza.

Tunda akayi haihuwar nan Abul khair bai ko dauki jaririyar ba haka kuma bai siyo ko kyalle ba da sunan ta,komai da miji keyi na hidima idan anyi masa haihuwa sai baffa da harun ne sukayi haka kuma hatta rayon suna baffa ne yayi sannan yayi mana kaya nida jaririyar na fitar suna,nidai kam babu taron sunan da zanyi saboda ina jin wata irin damuwa da bacin rai atare dani gashi kuma banda cikakkiyar lafiya amma duk da haka dai saida mutane suka dan zazzo ranar suna ciki harda dangina yan uwana wadanda suka zo daga kibiya nan aka danyi shagalin suna bawai na azo aganiba saboda komai anyi shine cikin karfin hali yarinya dai taci sunan ummulkhair shine sunan da na zaba mata kuma da hakan zamu kirata,

Kasancewar yan uwana duk sun san halin da nake ciki kowa tausaya min yake yi yana yimin addu'ar samun dacewa da rabo kyakkyawa duniya da lahira,washe garin suna duk suka tattafi sai iya Rahinatu kanwar Abul khair kadai aka bari.

Nidai atsarina bazan sake koda sati daya gidansu Abul khair ba amma koda su innah suka ji sai naga sun shiga tashin hankali nan suka rinka rokona akan inyi hakuri kar intafi inzauna tare dasu harga Allah banso haka ba domin nashirya fita daga rayuwar Abul khair ahalin yanzu sai dai kuma su innah nada wani muhimmanci agareni wanda har bana iya yin musu dasu,hakura nayi na zauna muka cigaba da zama kuma adaren ranar harun ya sameni daki ya tisani gaba akan dole lallai sai na karasa masa labarin da na fara bashi watanni biyu zuwa uku da suka gabata murmushin yake nayi saboda bana son tuna baya bana son tuna abubuwan da suka faru domin tamkar zuma ne da madaci agareni wani sashen mai dadi wani kuma sabanin haka,

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now