2

1.4K 124 7
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *Al-k'aluman* *Marubata*

  KUNGIYAR :-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATIONS* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

  *BABI NA GOMA SHA* *BIYAR*

     *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN......* 

    _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu*🖊

                0⃣2⃣

Tana kwance ta lumshe idanunta ne sbd yadda zuciyanta ke cigaba dajin tsanan   Kamal Alqasim, ganin kiranshi da tayi ayanzu shine ya sake dagula lissafinta don tasan baya wuce ace yazo kofar gdn sune , itakam ba abnd ta tsana irin ganin sa .

Labulen d'akin nasu Umma ta d'aga tare da sanyo kanta ciki bakinta d'auke da sallama , ta sauke idanunta akan Ruk'ayyah wacce ta bud'e idanunta tana amsa sallaman da umman tayi , cikin matukar tsare gd umman ta dubeta akaro na biyu tana fad'in

"To hamshak'iya me kunnin rashin jin mgn yanzu nan Ruk'ayyah duk irin fad'an damuke miki nida Abbanku akan wulak'anta wannan yaron bazakiji ba ko, yazo har kofar gdn nan ya d'aga waya yakiraki ki kasa amsa sa duk matsayinsa da sanin koshi d'in waye da kikayi bazaisa kiraga masa bako? To na baki minti sha biyar kishirya kifita yana waje , saura idn kinje kiyi abnd zai b'ata ransa harya gano kina kan bakanki na k'insa shashashan yarinya wacce bata san inda kanta ke mata ciwo ba , ana maganan arziki kina son tura kanki ga tsiya mu zuba nida kene kuma wlh bakida mijin aure daya wuce Kamal indai har mune muka kawoki duniya . "

Ta dire mgn tana huci tareda ficewa daga d'akin cikin tsananin fushi , yayinda Ruky ta fashe da kukan datake rik'ewa tun sanda umma tafara balbaleta da masifa ,sanin b'acin ran dazata shiga idn tacigaba da kukan batai abnd Umman ta umurceta ba yasata mik'ewa ahankali jikinta amatuk'ar sanyaye ta nufi k'aramin bathroom d'insu dake cikin room d'in tawanko fuskanta , koda ta fito goge fuskan kawai tayi tasa tozali a idonta batare datayi kok'aryn shafa komi akan fuskarba ta zura hijab d'inta Red wanda atake ya fito da kyawun fuskanta , sai dai idanunta da suka d'an tasa kad'an tareda sauya launi zuwa ja sbd kukan datayi , takalmi flat ta xura tayi waje tana jin zuciyanta tamkar zata kama da wuta sai dai tafiya take cikin takunta me cike da nutsuwa harta fice daga gate d'in gdn nasu.

Can tahango motar  shi gaba kad'an da gate d'in gdn nasu ya parker hakan yasata nufan motan kanta akasa , Kamal kuwa tunda ta fito idanunsa na kanta ta glass d'in motar harta k'ariso taja ta tsaya ajikin motan batare datayi yinkurin yin noking ba .

Hakan yasa Kamal sakin murmushi yana me bud'e mata seat d'in gaba , amma ko motsi batai ba daga inda take balle yasaka ran zata zauna hakan yasashi d'aga sautin muryan sa me cikeda isa yana fad'in

"Haba gimbiyata kishigo mana. "

Da harshen nasara yayi mgn hakan yasa Ruky ta tab'e baki tana mai bud'e kofar baya ta zauna yayinda kafafunta ke zube ta waje , hakan yasa kamal baya iya kallon fuskanta yadda yake muradi , ranshine ya sosu amma saiya samu kansa da danne b'acin ransa domin komi tayi Burgesa takeyi , rashin tsoranta da kafiyanta yana burgesa matuk'a da irin yadda take nuna kud'i basa rud'anta .

Cire murya yayi akaro na biyu yana fad'in

"My queen ki juyomin da kyakykyawar fuskanki nagani kozan sami nutsuwan zuciya plxx my Ruky babe . "

Ahankali ta juyo da fuskanta suka had'a idanu take Kamal ya sauke ajiyan zuciya yana sake jinta acikin jininsa, yayinda Ruky ta kifamai wata uwar harara muryanta me sanyi da dad'in saurare ta bude tana fad'in

"Uhumm Kamal kake ko wa don Allah ina rokonka daka fita arayuwata kabarni na aury mutumin daya dace da rayuwata, wlh natsaneka bantaba jin zansoka ba Ahmad nakeso shinama alqawarin gina rayuwata tareda shi me yasa zakai anfani da KWAD'AYIN IYAYENA akan abun duniya karabani da farin cikina meyasa ? Don Allah na rok'eka kafita arayuwata don Alla..."

Enough!  Ruky kada kisake gayamin inrabu dake Kamal ya katseta cikeda masifa harwani zafi zuciyansa tafara kafin yaci gaba da fad'in

"Bazan tab'a rabuwa da abnd nakeso ba , Ruk'ayyah bazan iya rayuwa batareda na mallaki abnd nakeso atattare dakeba , inasonki ina tsananin buk'atan na kasance tareda ke akan me zaki dinga had'ani da Allah don ki cutar da zuciyata, bantab'a cin karo da macen danaji sonta yaimun mummunan kamuba sai akanki baby , wlh inban mallakeki ba mutuwa zanyi . "

Yakare mgn yana xuba mata mayun idanuwansa dasuka fara sauya launi ,hawayen dake ambaliya akan fuskanta yake kallo zuciyansa nasake narkewa a k'aunarta , yayinda yakeji wani abu na sake fisgansa zuwa gareta hannu yasa ya cire hankacif d'in dake aljihun wandonsa ya miko hannu domin share mata Hawayen amma sai tai saurin buge hannunsa da k'arfin gske har hankacif d'in na fad'i cikin matukar fusata ta dubeshi cikeda masifa take fad'in

"Kada kasake kace zakai kuskuran sanya k'azamin hannunka akan fuskanta Kamal , kuma insha Allah burinka bazai tab'a cika akainaba mugu kawai mara tausayi wlh i hate u. "

Amemakon yaji zafin mgn datake gaya masa saima ya tsaya galala ya shagala akallon bakinta yadda yake motsawa, yaune karo nafarko da mgn me tsayi yake had'ashi da ita , dad'in muryanta nasake kasheshi sam baiso ta daina mgn ba duk da cewa ba kalamai ne masu dad'i take furtamai ba murmushi yayi yana d'auke idanunsa akan ta ganin yadda tamaida fuskanta waje tana cigaba da share hawayen fuskanta , kafin ya ciri murya yana fad'in

"Baby kisani Kamal yana k'aunarki yana tsananin buk'atarki duk da nasan bamu dace da junaba kaman yadda kikasha fad'i ni mara jine ke kuma natsatstsayi ce , sai dai kisani Kamal bai tab'a son abu bai mallakeshi ba ayanzu bandamu da lallai saina samu soyayyarki ba tunda na rigada nasiye iyayenki ,ban tab'a sanin kud'i suna tasiri akan cikar buriba sai da nahad'u da KWAD'AYAYYUN IYAYENKI , so zan anfani dasu incika burina inmallaki abnd nakeso shi kuma wancan garan da kika mato akansa sai dai sonsa ya kasheki wlh Ruky saina mallake ki amatsayin mata inyi yadda nakeso da albarkatun jikinki . "

Yakare mgn yana sakin murmushi me sauti wanda yasa Ruky sakin wani irin kuka me sosa zuciya , sosai yakejin kukan nata na ratsashi sai dai bazai tab'a yin abnd takeso ba tunda har tayi nasaran shiga zuciyansa ya riga ya kwad'aita da ita tofa saiya cika burinsa akanta hakan yasashi lumshe idanunsa yana sauraren kukan datake rerawa jin shiru yasashi bud'e idanunsa .

Bai ankaraba yaga shigewanta gd aguje hakan yasa yaji tamkar shima yabita cikin gdn don baigaji da ganin fuskantaba, lumshe idanunsa yayi yana mesake jingina da jikin kujeran motan hango wani matashi yayi zai wuce hakan yasashi sauke glass din motar yayi kiransa, envelop yaciro ya mika masa yana fad'in

"Plxxx kashiga can gdn kace sak'one daga Kamal aba ummah , yasake ciro kudi daga aljihunsa yana mik'ama saurayin da fad'in wannan kuma kasa katy awayanka . "

Godia sosai saurayin yaita zubawa ya juya xuwa cikin gdn su Ruk'ayyah domin isar da sak'o cikin sa'a umman yagani zata shiga d'akin su Ruk'ayyah ganin shigowanta aguje data hango daga d'akin ta , sallaman da matashin saurayin yayine ya dakatar da ita tana amsan sak'on kuwa tasanya kanta cikin d'akin tana jin farin ciki na ratsa zuciyanta domin tasan mahad'an rayuwa ne acikin envelope d'in (wato kud'i).

Kwance taga Ruky ta kifa ciki akatifa tana kuka me sauti harda ajiyan zuciya , hakan yasa takarisa bakin katifar tazauna tareda kai hannu ta d'ago fuskan Ruk'ayyah wanda ruwan hawaye kesake ambaliya akansa , cikin d'aure fuska tafara mgn tana fad'in..............

*Ayshat D'ansabo ce* 🖊

KUNDIN HASKE💡Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang