Shafi na biyar

1.8K 155 10
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


5

Bayan kusan minti goma Sai ga kiran Husnah tace "Ke fito gani a kofar gidanku" Fatima ta mike ta dau hijab dinta har kasa ta saka ta fita xuwa dakin Ammi, durkusawa tayi nan bakin kofa tace "Ammi Umar na jira na waje" Sai dai Ammi tayi mata izinin tafiya sannan ta mike ta fita, tsaye ta xaune ta tadda Husnah kan wani dakali, ta karasa da sauri ta xauna Husnah ta dafe kirji tace "Yanxu ce masa kika yi baxa ku hadu ba Fatima?" Fatima tace "Ke tsaya ni tsoro nake ji fa, ko sanin waye shi ba mu yi ba, what if mugu ne, beside bayan karyar da nayi masa game da babana da inda gidanmu yake kawai Sai ya xo ya ga wannan rubabben gidan Husnah" Husnah ta ja tsaki tace "Kaji xancen banxa ae nuna masa xa ki yi ke baki yarda ya xo ya ga gidanku ba sbda ba gama sanin juna kuka yi ba, don haka gwara ku hadu a eatry xai fi, ke meyasa baki da wayo ne har ynxu Fatima?" Fatima tayi shiru tana kallon ta, Husnah ta kuma jan wani tsaki tace "Ga ki dai kamar wata wayayya amma wllh wata yar kauyen ma ta fi ki wayewa, yanxu kina komawa ciki don Allah ki kara kiransa kiyi masa bayanin nn plss, Allah ni don nasan yana iya xuwa mu hadu ya ganni baxai sake dawowa ba da sai ince mu hadu da shi, kinsan dai kin fini kyau sosai, kuma irinsu basa san bakake sun fi son farare" tana kaiwa nan ta shafa fuskarta tace "Dubi fuskar duk kuraje ai baxai sake dawowa ba wllh idan muka hadu" Fatima dai ta rasa abun cewa, Husnah tace "Nasan me ke damun ki Fatima, yanxu kai ya waye bbu xancen yankan kai da Kidnapping, sannan fa ba wai son shi xa ki yi ba, kawai dai mu samu abinda muka samu muyi dumping dinsa mu nemi wani" Taba ta Fatima tayi da sauri ganin Umar dake tahowa, Husnah ta juya da sauri, ba shiri tayi tsit, ya karaso inda suke da sallama, Husnah ta washe hakora tace "Sannu da xuwa Umar, ina yini" yace "Lafiya lau Husnah ya mutan gidan?" Ta mike tace "Lafiya lau wllh ya kasuwa" yace "Alhmdllh" tace "Toh maa sha Allah" ta kalli Fatima tace "Toh besty bari in wuce kafin inna ta fara kirana, kice da Ammi nagode sosai na wuce, plss kiyi kiran da nace ko xuwa anjima, kin ji, ki kyalesu kishi suke da ke" daga haka tace "Toh Umar Sai da safe" Ya ciro kudi aljihunsa yace "Toh gashi ki hau mota, Allah ya kiyaye a gaida su mama" ta dawo da sauri ta Karba da hannu biyu tace "Haba dai, har da dawainiya haka, to nagode angon Fatima, Allah bar ku tare" murmushi yyi yace "Ameen" ta kalli Fatima da fuskarta bbu yabo bbu fallasa tace "Sai munyi waya teemah" daga haka ta bar wajen, Umar ya karasa ya xauna inda Husnah ta tashi, a hankali ta matsa ta bar distance me d'an yawa tsakaninsu, yace "How you?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya su Ammi?" Tace "They are fyn" shiru yyi na wani d'an lkci, can yace "Kin ji sauki dai yanxu koh?" Ta gyada kai tace "Eh" yace "Maa sha Allah, Kun yi maganan jamb da nayi maki da Ammi kuwa?" Tace "Eh nayi mata tace A'a baxan yi ba" yace "Toh Shkkn, Sai ki yi ta xuwa islamiyya koh, idan muka yi aure har masters Sai kinyi kin ji baby" bata ce komai ba sai wasa da fingers dinta da take, jin yyi shiru na kusan minti biyar ta kallesa ta ga kallon ta yake, tayi saurin kauda kai tace "Kaga Ammi bata san ka xo ba, kawai ce mata nayi xan raka Husnah kuma kar ta ga na dde" yace "Eh gaskiya ne kam" ledan hannunsa ya ajiye mata a kusa da Ita yace "Gashi dear kiyi manage kin ji" bata ce komai ba ya kuma daura mata kudi kan ledan yace "Toh tashi ki wuce ciki, ki gaida su Ammi" mikewa tayi ta dau ledan da kudin tace "Nagode Allah saka da alkhairi, sai da safe" daga haka ta wuce ciki ya bi ta da ido. Direct dakinsu ta wuce ta boye dubu biyun sannan ta bude ledojin biyu, fruits iri iri ne a dayan, dayan kuma gasasshen kaza ta mike ta kai can daki gun su Ammi don ko da wasa bata cin abun saurayi Ammi tace Allah amfana sannan ta fita dakin ta koma nasu tana tunanin shawarar Husnah, xama tayi gefen gado ta dau wayarta ta shiga kiran Elbash gabanta na faduwa, bai daga ba har ya katse sai gashi ya kira, ta daga ta kai kunne a hankali tayi sallama ya amsa, tace "Sorry for what I said the other time you called, just that I don't know you so I can't say to you where I live...." Katse ta yyi yace "I don't think it's necessary you call just to say this" ta tabe baki tace "Why not we meet at an eatry know our self better before...." Katse ta ya kuma yi yace "No no... Its not necessary, kindly get off my line or I cut the call on you" ji tayi gaba daya ranta ya baci, ta ja wani dogon tsaki tace "You shud be the one to get off my line cos you called, do so immediately now" tana fadin haka ta jefar da wayar kan gado ta fita don yin alwala tayi isha, ko da ta dawo gani tayi ya kashe kiran, ta gabatar da sllhnta tayi azkar sannan ta linke hijab ta hau kan gado ta jawo wayarta ta bude data, message dinsa ya shigo tare da WhatsApp messages ta bude IG don duba message din, "I will make you regret ur actions, xa ki san baki da wayo" Tsaki ta ja masa as reply ta kashe datan ta tayi addu'ar bacci.


KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now