13

2.2K 225 33
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


13

Kai kawai ta dinga gyada masa hawaye na sakko mata, yace "Good... Tashi in mayar da ke garin ku, there is still time for you to go to d islamiyya u intended going" ba musu ta mike ya nuna mata kofa, ta nufi kofar a sanyaye, ya bi bayanta, suna sakkowa downstairs ta jirasa bakin kofar parlon har ya karaso, suna hada ido ta dauke kai da sauri, ya bude kofar da makulli sannan ta fita tana goge guntun hawayen idonta, parking lot ya nufa ya bude mata front seat yana kallonta, taki yarda su hada ido, a hankali ta karaso tana share idonta ta shiga motar ya rufe, ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar aka bude masa gate ya fita, sai da suka hau kan titi murya can kasa yace "Am... am sorry for making you cry" ko kallonsa bata yi ba ta hade rai, yyi murmushi yana ci gaba da tukinsa yace "I was definitely on my own kika yi following dina a IG kika fara min rashin kunya....." nan ma dai ko kallon inda yake bata yi ba, bai kuma cewa komai ba sai da suka yi nisa sosai yace "Did you want to eat something?" Nan ma bata ce komai ba sai sabon hawayen da ya taru idonta, ya gangara gefen titi yayi parking yana kallonta yace "All this will surely come to an end one day fatima...." Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni dai ka gaya min me kke so daga gareni, ka gaya min ko xan iya maka ka rabu da ni na har abada" kallonta ya dinga yi har na tsawon minti daya kafin, ya shafa sajensa murya can kasa yace "Kin tabbata xa ki iya yi min abinda nake so kuwa?" Ta share idonta tace "What again, after you've deflowered me, meye kuma kke so a guna da ya wuce wannan, that's all I have and you took it away, we are not rich, I have nothing again to give" ya girgixa kai yace "Noo, you are talking off hook, the question is straight, ce min kika yi me nake bukata daga gare ki, and I answered xa ki iya min abinda nake so?" A sanyaye tace "Meye shi" yace "Xa ki iya?" Cikin rawar murya tace "But I have nothing to offer you again, ni ba kowa bace" ya hade rai yace "Just answer my question xa ki iya?" Ta make kafada tace "In dai sa6on Allah ne ni ba xan yi ba" murmushinsa me kyau yyi yace "Ba shi bane" tace "Toh meye?" Yace "Xa ki amince?" Tace "Idan naga xan iya amincewa" yace "Noo its a deal" tace "Ina jin ka" yana kallonta cikin cool voice dinsa yace "Kawai ki amince in aureki, shi kenan abinda nake so daga gare ki" wani mugun faduwa gabanta yyi tayi kasake tana kallonsa ko kiftawa bbu, lkci daya ranan da ta fara following dinsa da intentions dinsu na following dinsa ya dawo mata a kai, lokacin da ya daina kulata gaba daya da yanda taji a lkcn duk ta damu taji duk duniya bbu Wanda take so sai shi, ko a mafarki bata taba tunanin akwai ranan da Elbasheer xai bude baki yace xai aureta ba, bata san lkcn da tayi murmushi ba don reverse is d case yanxu, duk duniya bata jin akwai Wanda ta tsana irinsa yanxu, yana juya wristwatch din hannunsa yace "Yeahh, I want to marry you not because you deserve me" tana kkrin mayar da hawayen da ya cika idonta tace "ko da kuwa kai kadai ne namiji da yyi saura a duniya wllh da amince in aure mugu mara tausayi kamar ka gwara na mutu ba aure, I hate you.... I hate d reason i met you, kar ka sake ce min xaka aureni don ni ina da mijin da xan aura kuma na fi karfinka...." Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Kallonta kawai yake kafin yace "kika ce kin fi karfina? Did u knw it's a privilege in bude baki ince xan aure ki? Kinsan wanene ni?" Ta dago da sauri tace "Kwarai kuwa nasani, Elbasheer Ahmad kake ko wa? Wanda giyar kudi ke rudarsa ya kuma mance a nan aka samu kudin a nan kuma xa a bar su, macuci sannan kuma maxinaci" bata kai ga rufe baki ba ya fixgota har tana jiyo numfashinsa yana mata wani kallo da idanuwansa da suka sauya kala yace "Ni kike ce ma maxinaci?" Kuka ta dinga yi tana son kwace kanta a tsorace, daga karshe ya tura ta ya ci gaba da tukinsa, nesa da gidansu yyi parking har lkcn ta rufe fuskarta da hijab tana kuka, jinginar da kansa yyi da kujerar motar, Ya lumshe ido yace "Sorry in dai ni ne na sa ki kuka" tana shessheka tace "Bana so" yace "Toh me kike so" jin shirun yyi yawa ta xame hijab din da ta rufe fuskarta a hankali, kallonta taga yana yi, ta hade rai, ya matso kusa da ita yace "Kiyi hakuri nace" kauda kai tayi yace "Kin ji" ta goge fuskarta tace "Naji" murmushi yyi yace "Toh shiga ciki kada mama ta fara neman ki" agogo ya duba yaga hudu da rabi yace "Ko ba yanxu kuke dawowa makarantar ba?" Banxa tayi masa yace "Toh shkkn kilan baki son dawowa gidan ne" daga haka xai ja motar tace "Nooo ni ka tsaya in fita" yace "Tohm"  juyowa tayi ta mairairaice masa tace "Amma don Allah kada ka nuna ma saurayina hoton nan" ya langwabar da kai yace "Baxan nuna masa ba, amma dole saurayin naki yyi hakuri" bude motar tayi jin ya bude lock ta fita ta na kallonsa da kyau tace "Sai dai in kai ne xaka yi hakuri, ko kuma in hada ka da warce take mutuwar sonka wato shaidaniyar da ta hadani da kai, nasan she will gladly accept ni kam nafi karfinka kaje can ka aureta dama da ita kafi dacewa" tana kai wa nan ta kara gaba ba tare da ta rufe masa motar ba, ya bi ta da ido yana murmushi har ta shiga gida, rufe motarsa yyi ya bar anguwar. Da ido Ammi dake xaune tsakar gida ta bi ta da shi, Fatima xata shiga daki bayan ta gaisheta tace "Xo nan" dawowa tayi ta durkusa kusa da ita, Ammi tace "Me ya samu idanuwanki? Kuka kika yi ko me" kamar xata yi kuka tace "Wata ce a islamiyya bata da lafiya har da suma shine ta ban tausayi" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake" mikewa tayi a hankali tace "Ameen" sannan ta shiga daki. Gaba daya daren ranan Umar bai kirata ba, wanda hakan ya tada mata hankali cause that's very unusual of him, to ko dai Elbasheer ya nuna masa hotunan ne, tunanin hakan ya sa gabanta faduwa sosai, jiki a sanyaye ta dau wayarta misalin karfe goma tayi dialing numbersa, har ya katse bai daga ba ta kuma kira bai dauka ba, hawaye ya cika idonta ta rasa wani irin tunani xata yi, ta ma san ya nuna masa ne, number Elbasheer ta shiga kira, har ya katse bai dauka ba, ta fada kan katifa hawaye na sakko mata, wayarta ta fara ring ta mike da sauri ta dauka ko Umar ne taga Elbasheer, a sanyaye ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Uhnn why the call?" Kuka ta sakar masa kamar an aikota, da mugun mamaki ya dinga tambayarta me ya faru taki cewa komai yayi yayi amma taki magana daga karshe ya katse kiran ya sake kira taki dauka, ya kira yyi sau biyar bata ko kalli direction din wayar ba, tayi kuka ta gode Allah kafin bacci ya dauketa, da asuba ring din wayarta ne ya farkar da ita, ta mike xaune da sauri ta jawo wayar, Elbasheer ta gani ke kiranta, ta ja tsaki ta mike ta fita don dauro alwala, ta jima xaune kan darduma bayan ta idar da azkar dinta, har gari ya fara washewa, fita tayi ta share tsakar gidan gaba daya, ta axa wuta ta daura ruwa sannan ta dau bucket ta fita don bbu ruwa a gidan, duk a sanyaye take komai, tayi bucket kusan uku ana hudu kamar ance ta juya taga motar Elbasheer, tsabar tunanin da take bata ga shigowarsa layin ba, fitowa yyi daga motar yana sanye da jallabiya milk color, haka kawai gabanta ya fadi sosai ta juya masa baya da sauri.Har ya iso kusa da ita bata juyo ba, yace "You can do all such of silly things amma kar ki sake kirana kina min kuka a waya, are on ur right senses?" Murguda baki tayi ta kashe tap din ruwan xata dau ruwanta ta wuce ciki, kafa yasa ya tura ruwan ya fadi ya xube kasa, Sai a sannan ta juyo tana kallonsa fuska daure, yace "Ina maki magana xaki dau ruwa ki wuce, did you knw what you deprived me of yesternight?" Tabe baki tayi ta rungume hannayenta tace "I deprived you what you deprived me of also last night, ko ba bacci ba?" Kallonta ya tsaya yi kafin ya gyada kai yace "Allah xai kawo ranan da xa ki ga dare yanda kika ga rana a gidana" daga haka ya juya xai bar wajen, kuka ta sakar masa ya juyo da sauri tace "Shine Sai da ka nuna ma Umar hoton koh?" Yace "Eh an nuna, in dai shi yasa kika kirani kina kuka jiya" daga haka ya nufi motarsa ta bi sa da kallo. Wajen karfe goma na safiyar tana linkin kayanta da Ammi ta wanke mata jiya wayarta ya fara ring, ta jawo wayar tana kallon screen din, Umar ta ga ke kiranta, tayi tsuru kafin ta daga gabanta na faduwa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now