2

1.2K 116 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

*K'AIK'AYI...*

BABI GOMA SHA TARA

Page 2

Sam makaranta daya kaita bata yi mata ba, duka mata ne, hijab har yana ja da kasa ga matan wasu low class.

Kullum shine yake kaita kuma yakoma daukota, bata wani damu da wannan ba Dan tuntuni tariga ta saba, takai sati biyu tana zuwa makarantar amma bata kula kowa sai wata Zainab dake kusa da ita da suke gaisawa, haushin yarinyar ma takeji Dan taga kamar wani kallo take mata irin na raini.

Yauma tana zaune Zainab din tazo kusa da ita suka gaisa kamar ko yaushe fuskar khadija a hade, murmushi kawai Zainab din tayi ta zauna kusa da ita tana cewa "kinji yau babu lesson ko? Da fatar kin fada a gida sbd azo daukarki da wuri?" Ba tare da khadija ta kalleta ba ta girgiza mata kai, kallonta Zainab tayi tana murmushi sannan ta gyara zama sit dinta.

Bayan an tashi khadija taje wajen gate din makarantar ta tsaya, Zainab ma tana wurin har aka zo daukarta, zuwa tayi wurinda khadija take tsaye tace "idan babu damuwa kizo mu saukeki gida mana yafi kiyita tsayuwa anan har karfe Biyar" shuru khadija tayi tana tunanin ko yau kadai ma zata sake idan suka kaita, kallon Zainab din tayi da Dan murmushi kadan afuskarta tace "Babu damuwa nagode" motar suka shiga Zainab da khadija na zaune baya kanwar Zainab a gaba, tunda suka shiga motar Wanda yazo daukarsu yake kallon khadija har suka sauketa gida, suna isa gate din gidan Abbansu khadija na dawowa, saida ya tsaya yaga suwaye a motar, zuciyarsa tayi wata irin bugawa da sauri ya bude motarsa ya fito.

Tunda khadija ta hango motarsa gabanta ke faduwa amma sai ta basar tayiwa Zainab sallama ta soma tafiya, suma din gaba sukayi.

Sai da ya iso gabanta idonsa har yayi ja yace "daga ina like"? Muryarta na rawa tace "daga makarant..." "Sai karfe biyar kuke tashi ubanme ya dawo dake kuma waye ya kawo ki" jikinta ya shiga rawa ta somayi baya baya, yowa kanta yayi ta ruga da gudu.

Juwairiyya na tsugune gaban TV tana goge kurar da kayan sukayi sai ji tayi anshigo da gudu, kallon khadija tayi dake haki hawaye na zuba daga idonta tace "meye haka Nana"? Cikin muryar kuka tace "ummi, Abbu dukana z..." Saukar Marin da taji ta baya ya katse mata maganar da ta fara, sai da ta kife a wurin, dukanta ya shiga yi juwairiya tana tsaye tana kallon yadda yake dukar mata yarinya, tsayawa yayi yana huci sannan yace "ki gama kuka kizo ki fadamin gidan uban da kikaje ban yadda dake ba" ya shige dakinsa, ajiyar zuciya juwairiya ta sauke sannan taje kusa da ita tana tambayarta abinda ya faru amma kuka ya hanata bata amsar.

Hakuri juwairiya ta bata sannan tace, "kije ki sallah ki fito muci abinci kar ki dade kuma Kinsan halinsa" gyada mata kai khadija tayi sannan ta shiga dakinsu, bata dade ba Aisha ta dawo ta shigo dakin, tana kallon fuskar khadija ta ajiye Jakarta tace "me kuma kika yi masa yau"? Kallonta khadija tayi tana cewa "Ni na fara tunanin ba Abbu bane ya haifeni, ko tausayina baya ji a sati sai ya dake ni sau uku ko amma Ku yana sonku baya dukanku" shuru Aisha tayi bata kuma magana ba ta shiga toilet, a tare suka fito da Aisha an zauna su kadai ake jira, abbansu sai hararar khadija yake, a takure ta zauna ta kasa cin abinci ma.

Washe gari a school Zainab da khadija ke zaune suna shan fanta, Zainab tace "Ashe ke yar gidan Malam Saifullah ce? Kinji dadi babanki mai kudi kuma ga ilimi" khadija tayi murmushi tace "aikema babanku mai kudi ne, a shagon Ku ake mana siyayya lokacin salla" dariya Zainab tayi tace "Ashe kinsan yayan mu Wanda yakaiki gida jiya"? Khadija ta dago ta kalleta tana cewa "kamar nasan fuskar shi amma dai namanta Inda na sanshi Ashe shima yana tsayawa shagon" Zainab ta ajiye robar fanta dake hannunta tace "wallahi kuwa, Ai shi ya ganeki Dan ya dade yana bani labarinki, jiya har zagina yayi wai school dinmu daya dake Ashe nake wahalar dashi ban taba fada masa ba" Khajida ta zaro ido tana kallonta Zainab ta dake ta a kafada tace "wallahi dai bazaki yiwa yayana wulakanci ba, Dan ma kinyi Sa'a wannan handsome guy din yace yana sonki, kinga kuwa yadda yan mata ke rububinsa?" Murmushi khadija tayi kawai Zainab taci gaba da cewa "ni yace ma in karbo masa lambarki" bata fuska khadija tayi tace "banida waya ai, Abbun mu baya bari na rike waya" Zainab ta harareta tana cewa "ke karki cemin har yanzu baki waye ba? Ni duk samarina da wayar mama nake kiransu" tunanin yadda umminsu ke jefar da waya bata damu da ita ba tayi sai ta karbi takardar ta saka a jaka.

Tunda ta koma gida take tunanin yadda zata dauko wayar sai ta yanke shawarar cewa ummi zata kira Anty jawahir, bayan ta karbo wayar tazo ta zauna ta rubuta numbern ta kira, sai da suka gaisa tace "I'm Nana khadija Saifullah" ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "Alhamdulillahi sweety, na dade ina dakon soyayyar ki dole na godewa Allah dayasa na sameki a saukake ina fatan zan samu fili a zuciyarki, wallahi khadija kece matar da nake mafarkin aure" murmushi tayi sannan tace "kaga anjima zamuyi magana sai zuwa gobe, karka kira kuma Dan wayar ummi ce nakira da ita" tana gama fadar haka ta kashe wayar sannan ta kira jawahir dinda tace zata kira.

Wani juyi kabir yayi bayan ta kashe wayar yace "yes! Na sameta wallahi"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now