4

1.5K 192 13
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        *_Al’kaluman marubata_*

   *_KUNGIYAR:-_*
_*HASKE WRITERS ASSOCIATION*_
_(home of expert and perfect writers)_

_TARE DA AL KALAMIN_

*_MAMUH GEE_*


_BABI NA GOMA SHA SHIDDA_

*YIWA KAI*


*4*

Koda Suka kamo hanyar gida cikin kulawa ya Dan juyo daga tuqin motar dayakeyi ya kalli amal din datai bacci jikin mamanta kafin ya kalli hafsat din yace"

Hafsat Dan Allah ki maida hankali kibawa 'yarki kulawa yanda ya kamata sbd soyayyarki agareta iya bakinki ta tsaya kin kasa aikatawa a bayyane musamman sbd wainnan banxan kallace kallacen da karatun banxa Wanda Babu inda zai kaiki,

Bance karkiyi ba Amma kiyisa bayan kin gama duk abinda yake dolenki cikin nutsuwa da amanar zuciyarki sbd maganar gskia amal Bata samun kulawar uwa yanda yakamata,

Wannan kukan datake yawan yi yawanci na yunwa ne ko kishirwa kokuma na idan wani Abu na damunta Amma data fara saiki miqawa shamsu ita kilama yanada guraren zuwa Amma kike tauyesa sbd kinsan bazai iya qin lallashintaba,

Ni wlh Ina zarginki idanba maganin bacci kike dirka mata ba danta ringa bacci kina hutawa daga rigimarta sbd kiyi shirmenki.

Kallonsa tayi cikin shagwabe fuska tace"

Wlh MD bana Bata komai ai duk rigimarta bata kaimin can ba dahar zan Bata maganin bacci.

To wannan shegen Rashin sanin ciwon kan naki ai Zaki iya hakan Sarai nasani.

Bata fuska tayi tace"

Menene Rashin sanin ciwon kan tunda saina gama komai nakeyi zaman kadaici ai bayada dadi.

Hmm nidai wannan kumburin da zafin jikin nasan dole akwai abinda ke damun 'yata ga Kuma yawan baccin nan yayi yawa tunda nasan amal bamai yawan bacci bace wlh kwana biyu yayi Bata koma daidai ba mukaje asibiti akacemin maganin bacci kike Bata wlh zakiga bacin Raina.

Sanin Bata bata komai yasan Bata ji fargaba ba Saidai sanyi da jikinta yayi ganin kamar ransa ya baci ahankali ta furta to Allah ya huci zuciyarka.

Bayan isarsu gida duk yanda taso yin kallon daurewa tayi sbd ganin yanda ransa yake a bace gashi dare ne.

Washe gari gidan maman sadeeq taje acan sukai kallonsu hankali kwance sai kusan yamma ta fito ta hadeda uncle shamsu zai shigo gidan maman sadeeq din Dan kawo mata amal dasukaje yawo tun Sha biyun Rana.

Tare Suka koma gidan suna shiga Suka nufi palo nan Suka hau firarsu tana fada masa ai dazu fatimarsa takirata tace mata sunje da amal.

Suna cikin firar Kamal yashigo amal tayi gurinsa tana miqa masa hannu ya dauketa.

Sama yayi da ita tareda Kai bakinsa yayi mata kiss yaji hancinsa ya shaqo masa wani irin qarni jikin rigarta.

Sake shinshinawa yayi Yana Bata fuska bai tantance warin ba yakalli hafsat Yana cewa"

Ki canza mata Kaya Sam wani irin qarni takeyi.

Miqewa tayi tana cewa"

Wlh tun safe sukaje gidansu fatin uncle shamsu sai yanxu Suka dawo qila wasa da barna sukaitayi tunda akwai yara da yawa gidan.

Harda sabon wanka tayi mata duk da itama taji qarnin Amma tasan na dau'da ne sbd gidansu fatin gidan taro ne Kuma irin masu kiwon dabbobin nan ne cikin gida ga kwata cikin gidan.

Tare dukkaninsu sukayi dinner yau har uncle shamsu Wanda Kamal yau abin yaso bashi tsoro sbd yanda amal ke wani irin bacci anyi anyi atayarda ita taci abincin dare takasa barin baccin qarshema rigima tasa tana wani irin kuka aka ringa lallashinta saima sake rikicewa datakeyi.

Yau maman sadeeq gidan Maryam tayi kallonta daganan Suka Dora da firar littafai mai aikinta na kicin tana aikin abincin dare Saidai tanajin firar tasu saiga mijin Maryam din yadawo daukeda wata babbar jaka yashige bedroom dinsa ya ajiye yafito yasake ficewawarsa.

Qarfe biyar za'a fara dramas dinsu saigashi nepa Suka dauke wuta
Cikeda takaicin maryam tace"

Kai Amma wlh Allah ya isa yan nepa dinnan gashi wlh jiya da dare gen dinmu ya tsaya Kuma wlh ba'agyara ba.

Cikin haushin baban sadeeq maman sadeeq tace"

Nikuma wlh baban sadeeq tsabar baqin ciki yaqi subscription wannan watan data ma sbd karnayi karatu wannan watan qin sakamin yayi saidana Kira qanina auwal yaturomin wlh.

Tare Suka miqe suna cewa"

Muje gidan hafsat Dan nasan yanxunan harta kunna inverter din gidanta muje tun kafin ayi nisa.

Daga murya Maryam tayi tace"

Asiya muntafi gidan maman amal idan kingama girkin ki dorawa Habib kunun gyada kinsan yau Yana azumin alhamis.

Kafin su shige gidan hafsat suna fitowa gate din gidan Maryam maman sadeeq ta Kira nuhu dake dakin mai gadinta yafito Yana gyara wando ta hararesa fuska a daure tace"

Meye haka zaka fito wando a hannu.

Sosai Kai yayi Yana sunnewa yace"

Wlh Kaya nake Shirin canzawa kika kirani.

Tsoki tasaki tana cewa"

Nikam nuhu Sam yanzu kanason zamowa rago bansan lalacin dakesa koyaushe kana sinqe cikin dakin baba mai gadi shima wani lokacin aita Kira Yana daki saikace wani abin arzikine a dakin,
Nidai ga sadeeq nan jasa kuje kafin nafito gidan hafsat.

Kama hannun sadeeq din yayi shima sadeeq din tuni yayi hanyar dakin baba maigadi Yana cewa"

Bye bye mama.

Shigewa sukayi gidan Suka baje a Palo nan hayaniya ta tashi aka fara kallo.
#mamuhgee

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now