Shafi na biyu

1.4K 108 1
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL'KALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TASKAR: Khadija Ahmad*😊

*RAYUWAR NI 'YA SU*

Babi na goma sha d'aya

2)
*Not edited*

  Duk da halin da nake ciki be hanani ansa sallamar ba tare da kallon ba'kin fuskokin inna fad'ad'a fara'arta tare da cewa
  "Ah ah su hajiya ummi ne yau a gidan namu?"
  "Ashe zaki shedani rahila"
"Me ko ze hana bismillah ga waje ku zauna"
"To madallah bismillahi" wacce aka kira da hajiya ummi tace tare da zaunar da yaron fake ri'ke da hannunta a gabanta.
Tsam nakoma cikin d'akin dana fito ba tare da nace uffan ba suna nan zaune yanda na barsu se aunty jummai dake musu fad'a, sakai nayi na wuce dan har yanzu raina zafi yake min.ta gefen ba'kin na ra'ba zan wuce naji Inna na fad'in
  "Ke baki iya gaisuwa bane?"
A duburburce na waiwayo har 'kasa na tsugunna Ina gaishesu da fara'ar su suka ansa min, nan d'aya cikinsu tace
  "Hajiya a'i kin shaidata kuwa?"
" Haba ummi ai ko ba'a fad'a ba Ina kallon idonta nasan Raheena ce abinda yake Iri d'aya ai ni tanan kad'ai zan iya gane family d'in ki, questionable look nabita dashi kan ta katseni da zancen makaranta ina bata ansa kan ta Shimin albarka nan take fad'a min ita d'in mahaifiyar uwata ce , a guje na fad'a kanta na fashe da wani irin kukan dad'i, itama rungumeni tayi gam tana shafa bayana  tare da ban baki nan aka barni dasu kowa ya watse bayan sunci abinci sunyi sallah baba malam ya shigo inda ta shaida masa ma'kasudin zuwan ta wato ta dawo da Aliyu gida dan yashiga cikin 'yanuwansa, bud'an bakin baba malam se cewa yayi
"Bisa wani dalili zaki dawo dashi?"
A razane na kalleshi Kula da haka yasa yace "ke tashi ki bamu wuri" a sanyaye na shiga d'akina jikin 'kofa na jingina na kuma fashewa da marayan kuka wannan shine ga samu ga kuma rashi yanzu baba malam yana nufin su ko da shi kenan jin magana nayi ta bayan d'akina na d'age labulen dan ganin su waye Inna na hango tare da su farida da fad'ima tana cewa
"Ai zasu ga iya shege wlh se de ya zauna can d'akin guga dake BQ bade cikin gida ba yaron da bashi da hankali haka kawai tsautsayi yasa wataran ya fad'awa yarana Ni me 'ya'ya mata"
Farida ta amshe"Ni kuwa Inna da zaki d'auki shawarata da karkice komai ki jira kiji abinda baba malam zece"
"Hakane kuma fa kar ace dan ba d'anki bane" cewar fad'ime
"To ayi ta fad'a mana ai.."
  "Inna kizo inji baba malam"
  "To ganinan" ta kalle "Inazuma" ta shigo ciki ni da nake bakin window 'kirjina ya shiga duka tun 'karfi kai jama'a wai shin meke faruwa danine?
**          **          **

Bayan wasu kwanaki Aliyu kullum cikin d'akin su sagir yake kwana  kwatsam rannan nayi gyaran d'akin su sagir se na janye akwatin kayansa nakai d'akina ai kuwa washe gari abinka da mara lafiya duku duku ya hau neman kayansa  ni bansan ya akayi ba yade le'ko d'akina ya janye akwatin ya fita ashe kafin ya shigo d'akina ya lelle'ke d'akunan su fad'ima ranar kuwa balbalin da Inna tayi cikin gidannan ba kad'an bane ana haka sega sallamar aunty rakiya muka gaisa ta nufi Aliyu da fara'arta wande ke la'be bayan kujera a 'kasa saboda Inna ta hanashi zaman kujera ko carpet gudun wai kar yayi mata fitsari ko kashi, hannu ta mi'ka masa ya sunkuyar da kai bakin nan washe yana yar dariya hannunsa ta 'kasa yana wasa dasu ta shafa kansa kawai tare da ce masa
  "Allah ya baka lafiya" nan ma shiru yayi mata, Inna data shigo falon tace
  'a a ke kuma fa daga Ina naga akwatin ki a bakin 'kofa" narai narai tayi da Ido batare da ta furta komai ba Inna tace "shigo ciki" nidai na bisu da Ido tare da waiwayo wa na kalli d'anuwana da nakeji har cikin jikina nace "zakaci abinci" tare dayi masa alama da hannu" seda ya wawwaiga yaga babu kowa se ya mi'ke ya kama hannuna duk da kyankyami irin nawa wlh banji shi kan Aliyu ba dan dayawa nike share mishi yawun dake dalalo mishi  da tissue dining naga mun nufa tabbacin zeci abincin kenan harda ka min kujera na zauna shima yaja ya zauna kamar wani me hankali ya shiga nuna min kwanukan wato na zuba mishi kwalla ta cicciko idanuna tunowa da nayi cewar Idan baba malam ya tarar da Aliyu kan dining ze yi fad'a saboda beson 'kazanta bare shi dake dalalar da yawu cikin dabara na jashi zuwa varender bayan na zaunar dashi nashiga bashi a baki dan Idan nace yaci da kanshi baya iya ci sosai yanaci Ina masa wasa bayan ya gama na bashi tablet dita nayi masa playing wani video din hotunan mu tun daga kan Abba har zuwa kan haule yana ta kalla haka muka wuni se zuwa dare nakejin dalilin zuwan aunty rakiya ashe wai mijinta ne yace bazataje ondo NYSC ba wanda da a kano zatayi batasani ba yaje yasa aka turata ondo a tunaninsa baba malam baze bari ba ai kuwa baba malam yace zuwa ba fashi idan lokacin yayi ta shirya su tafi da Abdullahi.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now