Shafi na hudu

1.6K 164 6
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-KALUMAN MARUBUTA...*

*NA KUNGIYAR...*
     *HASKE WRITERS ASSO*

*TARE DA AL-K'ALAMIN...*

*HAFSAT RANO*

*WAYAR MIJI*

_Babi na takwas_

Shafi na hudu

Kokarin saka key yake tayi amma kofa tak'i bud'uwa, mamaki ya shiga yi tunda shi sam be kawo Khairat xata rufe masa kofa ba. Tunanin sa d'aya kar dai ace khairat bata nan ko kuma kofar ta rufe da su a ciki basu sani ba. Sai ya shiga bubbuga kofar da dan karfi.

Duk kokarin da yake na ganin ya bud'e kofar har ya fara bugu akan kunnen Khairat, tana tsaye k'ik'am a tsakiyar falo tana kwasar dariya. Ganin yaci wajen mintuna talatin yana abu d'aya yasa ta d'aga murya bayan ta fito tsakar gidan tace;

"Da ka daina wahalar da kanka ka koma in da ka fito don bazan bude maka ba."

"Auw dama rufe k'ofar ki kayi da gangan khairat? Toh kuwa wallahi kizo ki bud'e kafin na sassab'a miki." Sai ta saki shewa harda tafa hannu.

"Kurarin banza kenan, ta ina ma ka ganni balle ka sassab'a min, ka ga tafiyata ni Allah bamu Alkhairi."

"Khairat! Khairat!!" Ya shiga kiranta da karfi yana bubbuga k'ofar ya ma manta dare ne. Tana tsaye in da take, amma tsananin kishi ya hanata bud'e masan.

Alamun sanya key ya jiyo a bayansa, Malam Hassan mak'wafcin sa ne ya fito haske da touch light.
"Subhanallah, lafiya dai Malam? tun d'azun nake jin kamar bugun k'ofa sai kuma na jiyo muryarka."

Takaici ne ya kamashi da irin tozarcin da Khairat keson jawo masa. Sai ya waske yace;

"Umm ina tunanin barci sukayi gashi na manta ban fita da mukullina ba, amma bari na k'ara gwadawa ko Allah zaisa taji."

Sai ya takarkare kamar gaske ya cigaba da bugu zuciyarsa kamar zata subto. A gadaran ce tazo ta zare sakatar yayi wuf ya fad'o ciki ko sallama beyi wa malam Hassan ba.
Allah rufa asiri." malam Hassan yace ya shige gidansa.

Yana shiga ya rufe ta da fad'a kamar zai dake ta, sai ita ma ta hau dokin zuciya ta hayayyak'o masa kamar xata cinye shi.

"Ban taba sanin baki da mutunci ba wallahi sai yau, ke dama haka kike ashe."

"Haka nake da baka sani ba kenan, toh wallahi in dai akan cin amanar da kake shirin yimun ne wallahi sai kaga abinda yafi haka."

"Shikenan mu zuba ni dake muga wanda zai ci riba, useless."

"Mu zuba d'in aga wanda zai fasa."

Ranar kusan kwana zaune sukayi ana tashin hankali, babu irin sunayen da bata kira shi dashi ba, har cewa tayi yana neman mata waiyazubillah.

Sai shiga d'akin ya sa key ya barta a tsaye falon. Bubbuga kofar ta shiga yi tana zagin sa, ji yake kamar ya fito ya babballata, amma sai ya danne zuciyarsa, karshe sai ya danna numbobin karya ya shiga waya yana ambaton sunayen da suka sa Khairat zubewa a wajen bata shirya ba.

Abinda bata sani ba shine, tun kafin magriba ya tawo gida sai ya had'u da tsautsayi ya bige wani mutumi, Allah dai ya takaita be ji mummunan ciwo ba, dalilin kenan da yasa ya jima sai da ya tabbatar mutumin ya dawo hayyacinsa ya maidashi gida sannan ya tawo.

°°°
A bangaren Idris kuwa yana shiga d'akin ya hangeta chan karshen gado ta kudundune cikin bargo, guiwa a sake ya k'arasa kan gadon ya shige cikin bargon ya k'wanta a bayanta. Ta jishi sarai sai ta rufe idonta kamar me barci,

"Baby!." Ya furta kamar me rad'a cikin muryar dake narkar da ita. Bata amsa ba sai ma k'ara kudundunewa da tayi.

"Ohh masha Allah, ashe tayi barci, bari nayi kissing d'inta nasan bazata sani ba tun da tayi barci." Ya fad'a yana matsawa kusa da ita sosai. Sai ta mik'e da sauri tana runtse ido ganin da gaske yake,
Dariya taso kwace masa ya kanne yace;

"Ya kika tashi ko dama ba baccin kike ba? Umm baby?" Ya fad'a yana kanne mata ido cikin salonsa da Na'ima tafi so.

"Barci nake fa ka tasheni, yanzu nasan da kyar zan koma." Ta amsa tana zunburo baki. Kallon ta ya tsaya yi don rabonsa da ganin irin haka ga Na'imar sa tun kafin abubuwa su faru, dole ya wanke tab'on dake zuciyar ta, a yanzu a cikin daren nan ba sai gobe ba.

"Kin ga dama nima bana jin barci, shikenan sai muci soyayyarmu mu rak'ashe abunmu." Sai ta dan dube shi, kamar ma babu wani abun tashin hankali da ya faru dasu a yan k'wanakin nan, nema yake ta dole sai ya mantar da ita komai. Hure mata ido yayi ya jawo ta jikinsa, duk fushin da takeyi dashi ba zata taba hana mishi hakkinsa ba, ta wannan bangaren kam ta ciri tuta.

A nutse ya shiga nuna mata xallar kauna da soyayya, duk wani motsi da xaiyi sai ya furta "I'm sorry." Sai ta ajiye komai a gefe ta faranta wa mijinta. Sai bayan komai ya lafa ta fashe da matsananin cin kuka, kuka me cike da ma'anoni da yawa, kukan da takejin bazata iya daina shi ba har sai ranar data daina numfashi.

Yana jinta beyi yunkurin hanata ba, sai ma dafe kamsa da yayi kawai yana jin kukan har cikin kokon kansa, sai da tayi sosai sannan zuciyarta ta samu saidah, sai a sannan shima ya sami damar bata baki.

Washegari ta tashi da d'an dama-dama, hira suke da Idris sosai ba kamar yan k'wanakin nan ba da ta zama kamar bak'uwar sa, sai ya jishi a sake har yaso ya zak'e duk a tunaninsa ta manta komai ne, tare suka shiga kitchen ya tayata had'a miyar gyad'a da tuwon shinkafa kasancewar ranar asabar ce babu in da zai je. Bayan sun kammala sukayi sallah ya jasu jam'i, yana lura da ita komai take kawai daurewa take amma kamar bata jin dadin jikinta, tsoron tambayarta yake kar yaje ta sake birkice masa, sai kawai ya dage wajen ganin ya faranta mata da kokarin mantar da ita komai.

Wajen la'asar taji ciwo yana neman addabarta musamman mararta da take wani irin juyawa, a lissafin ta saura wajen sati daya ta fara period, jin yanayin take kamar wadda aka yiwa duka, kasala da wani irin yanayi take jikinta. Lokacin Idris ya fita bayan layinsu wajen wani abokinsa. Yana chan amma hankalin sa na gida. Da k'yar ta shiga kitchen ta dora jollop d'in cus-cus tana cize yatsa.

Sai bayan magriba ya shigo ya tarar da ita a durkushe kan abun sallah. Da sauri ya k'araso gami da sakin ledar hannun sa yana d'agota. Hawaye ya gani k'wance kan fuskarta wanda ya sashi jin wani abu ya tsirga masa. A duniya ya tsani abun da xai bata wa Na'ima rai, gashi yana iya kokarin sa wajen ganin ya mantar da ita komai amma abin yacu tura. Sai yaja baya da sauri yana kallonta

"Wai Na'ima ke kike so nayi miki ne? Na baki hakuri nayi nadama, na fad'a miki sharrin shaidan ne amma kin kasa fuskanta ta, haba Na'ima, Allah ma mu kanyi masa laifi ya yafe mana. Don Allah ba dan halina ba ki sassauta wa kanki, kiyi min hukuncin da kike ganin ya dace dani amma ba ki dinga azabtar da kanki ba." Ya k'arashe yana xama hannun kujerar da take fuskantar ta. Sai ta fashe da kuka tana sake rik'e cikinta, kafin wani abu ta fara yunkurin fitar da duk wani abu da yake cikin nata. Iya rud'ewa Idris ya rud'e, ya rasa ta ina zai fara ma, sannu kawai yake jerawa yana kai komo a falon har ta gama. Sai ta k'wanta lamo a wajen babu sauran k'wari a jikinta. Hannun rigarsa ya nannad'e ya shiga tsaftace wajen kafin ya taymaka mata zuwa toilet ta gyara jikinta. A gefen gado ya k'wantar da ita ya sauya mata hijabi sannan suka fice zuwa asibiti. Gwajin farko aka tabbatar musu da shigar ciki har na sati bak'wai. Ba Idris d'in ba ma hatta Na'ima farinciki sosai ta shiga yi, ballanta na shi uban gayyan wanda kullum addu'ar sa Allah ya azurta su da zuri'a tare da Na'imar sa. Sai a lokacin kunya da tsoron Allah ya k'ara shigarshi. Kunyar abinda ya jima yana aikatawa yake wanda ba dan Allah ya sa Na'imar sa ta gani ba da har yanzu yana kan sab'on. Sai gashi a d'an lokaci kadan Allah yayi masa kyautar da ba kowa ake wa ba, sai ya k'ara kankan da kansa yana bitar Asthagfirullah wa atubu ilaik.

***
Note:
Ita fa binciken wayar miji tana da amfani da rashin amfani, amma rashin amfaninsa yawa garashi. Bana goyon bayan mace ta binciki wayar mijinta. Saboda ba kowanne miji ne ke daukar gyara ba, sannan kuma ba kowacce mace ce ta iya bayar sa gyaran ba, wata garin son nuna masa kuskurensa, sai ta d'aga hankalin gaba d'aya local government d'insu. Lol🤪

Rano a.k.a yayar xoxo🤪🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now