Babi na 20-Ayusher Muhd

2.3K 207 23
                                    

KUNDIN HASKE

ALKALUMAN MARUBUTA🤝

*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*

*Wattpad :-AyusherMohd*

TARE DA ALKALAMIN

*Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*MENENE MATSALAR?*

*Babi na Ashirin*

Page 1

*********
Da sauri ta dago ta kalleshi, wani lallausan murmushi ya sakarmata tare da kara kallanta.
Wani iri bugu zuciyarta keyi da sauri da sauri bakinta na rawa ta kalli hannunsa daya dauka akan cinyarta.

Murmushi ya sake yace "kefa matsalata dake kenan, ni anya ma kina sona?"
Ya fada cikin yanayi na damuwa.

Tace "kaima kasan ina sanka amma gani nai bamuyi aure ba bai kamata ba."

Dauke hannunsa yai tare da yin tsaki yace "fita daga motar zan wuce gida."

Gabanta ne ya fadi ganin wannan shine saurayin da take tunanin zai aureta, iyaye da 'yan uwa sun sata a gaba da zancen tai aure ga duk saurayin datama zancen turowa sai taji shiru, wannan da take tunanin zai aureta yanzu shima tafiya zaiyi?

Da sauri tace "Abdul kayi hakuri bawai wani abin nake nufi ba."

Cikin wani yanayi ya kalleta yace "zina na nema dake?"
Kai ta girgiza da sauri, yace "to akan me dan kawai na dan tabaki na rage zafi shine zaki maidani dan iska? So kike nabi karuwai?"

Hankalinta a tashe take kallansa, yace "na turo gaisuwa wancan sati, banda wani buri balle na aureki, sai dai sha'awa kwanan nan hanani sukuni takeyi, nama su Baba magana a sa rana wani satin, amma taya zan aureki bayan ba so na kike ba?”

Idanunta ne suka ciciko, shekararta 28 kenan, yan uwa da kawaye sa’aninta duk sunyi aure da ‘ya’yansu, kananta biyu mata ma sunyi aure, ita kenan dashan gorin rashin aure a koda yaushe....

“Katse mata tunani yai da cewa, jeki kawai zan wuce gida.”

Hawayenta ta maida sannan ta kalleshi.
“Jeki”
Kalmar daya kara fada mata kenan wanda yasa ta juya ta bude kofar motar jikinta duk a sanyaye, tana fita yaja motarsa da karfi yabar gun.

Da kallo tabi motar kafin ta juya cikin gida, tana shiga falo taga Umma na zaune a falo ita da yayanta babba namiji suna kallo a tv, jiki a sanyaye ta nemi wucewa ciki.

Ran Umma a bace tace “shima bazai turo asa ranar ba?”
Kallanta tai tace “Umma yace......”
Sai kuma ta kasa magana saboda ta gaji da bada uzuri akan abinda ba ita zata ma kanta ba, kullum ta Allah sai an mata fadan aure ta rasa ya zatai da rayuwarta.

Ya Jabir ne yace “Zahra gobe inkin samu lokaci kije gidan Aunty Rabi zaku fara hada lefe na.”

Wani abu ta hadiya tace “Masha Allah ashe abu yazo.”

Umma ce tace “tunda ke kinba aure baya sai kiyi ta zama a cikin gidan nan, har jikokin gidan sukai lokacin aure, ni wlh Jabir wannan abu ya isheni yarinya sangam sangam a cikin gida, wannan da gidan nan ana karatun boko da har kya kare ba miji, haba ni wannan abu ya isheni wlh, wannan wani irin abu ne wannan?”

Jabir yace “Lokaci ne Umma, dan Allah ku mata addu’a ba wai fada ba.”
Wani takaicine ya kara kamata, juyawa tai ta wuce dakinsu.

Zama tai a bakin gado a hankali wasu zafafan hawaye suka zubo mata, wayarta ta dauka tama Abdul text.

“Dear ka isa gida lafiya?”

Sama da awa daya dayin text din amma ba reply, nan ta kirashi a waya kira uku tamai amma bai dauka ba.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now