7

1.3K 102 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 7

Duk irin karar da wayarsa keyi kin dagawa yayi, ya tabbatar da wasila ce kuma yadda yake ji idan ya dauki wayar komai zai iya faruwa.
Tsaki yayi a fili yace "nasan wannan munafukar Zainab dince taje tayi min hadi, saina b'allata" ganin babu mafita yasashi mikewa yabar gidan.

Yunwa ta hana saifullahi bacci dama shi gwanin tashi cin abincin dare ne yau kuwa daya tashi daki da palonsa babu kitchen dama gefen juwairiyya yake, Har zuciyarsa yaji tana ciwo fitowa yayi yatsaya sabuwar kofar da aka hudawa juwairiyya, sai da yayi bisimillah sannan ya kwankwansa, Har ya cire rai da zata fito sai yaji alamar bude kofar palonta yaja ya tsaya.

Mamakin ganinsa tayi karfe shabiyu da Rabi yanzu sai taga ya miko mata kular daya karbo abinci gidan Anty asabe yace "Dan Allah koda kadanne Na kasa bacci saboda yunwa" kallon Ahmad tayi da suka fito tare taga ya kura mata ido shima sai ta matsa masa tana cewa "ka tsaya daga nan, bari Ahmad ya kawo maka" gidan ta shiga ta barshi tsaye a wurin, wani kololon bakin ciki ya hadiya, bai taba tunanin rayuwarsa zata zama haka ba abinda yake iko dashi shine yanzu ya gagareshi, Allah ya gani ya soma gajiyawa yanada bukatar iyalinsa akusa dashi.

Tunda aka kawo khadija gidan Anty asabe take mata masifa dama ita bata raina abin fada, sai duk khadija ta kasa sakin jikinta, duk abinda aka kawo akace sha ko Shafa bata musawa, kwanakin nan kalilan duk ta firgice idonta sun zurma kamar wadda tayi ciwon shekara, ita kanta tsoron kallon mudubi take, rabon da tayi bacci kuwa tun ranar da aka gano cikin nan, kullum kwana kuka take musamman yanzu da Anty asabe take tsorata ta da cewar ta rasa darajarta kuma ko mai daren dadewa mijinta sai ya goranta mata koda kuwa shine ya aureta, haka ma mutanen gari, shiyasa gaba daya bata jin dadin rayuwarta.

Tana zaune tanajin Anty asabe Na waya kan cewa tunda angama jere kawai awuce da kayan lefenta gidan sai dai a debo kala biyu da zata saka gobe ranar daurin aure.

A Daren ma kuka ta kwana yi, duk budurwar da zatayi aure a gidan iyayenta take zama, mutane suyita zuwa suna tayasu murna amma ita ga yadda nata yazo, ita daban, babanta daban haka ma mamanta daban.

Ala dole kabir ya shirya zuwa daurin auren nan badan yaso ba, fuskarsa babu walwala gaba daya, yasha mamaki ganin mutanen da sukaje daurin auren dan baiyi tsammanin ganinsu ba.

Babu wasu mutane a gidan juwairiyya saima kannenta da suka zo su kadai, bayan jawahir babu Wanda yasan abinda yake faruwa a gidan su, a gidan Anty asabe nema aka Dan taru saboda yan gidan su saifullahi suna matukar son khadija Dan haka batareda malam yaji ba sukazo saboda idan ya sani ba zai bari suje ba.

Yan daukar amarya suka zo sai yaba kyawon amaryar suke duk da batayi wata kwalliya ba, daga gidan Anty asabe gidansu aka wuce da ita inda aka shiga da ita dakin juwairiyya, su uku ne kawai a dakin, Aisha kanwarta sai umminsu da Anty jawahir.
Da shigarsu khadija ta zube kan gwiwoyinta tana kallon umminsu ta kasa cewa komai, Allah sarki da auren farin ciki ne da ko zatayi kuka sai dai tayi kukan rabuwa da umminta, amma yanzu kuka biyu take yi, kukan rabuwa da Ummi da kuma abinda zata je ta tarar a gidan mijin, bayan zamanda Ummi da abbunsu batasan komai game da gidan aure ba, dagowa tasakeyi ta kalli juwairiyya sai taga itama hawaye take yi tace "ummi kiyi hakuri ki yafe...." jawahir tayi saurin rufe mata baki ta kalli matan da suka tsaya bayanta
Tace "Dan Allah kuyi hakuri Ku zauna palo minti biyar zan fito muku da ita" to suka amsa dashi sannan suka fita, sake kallon umminsu tayi tace "ummi bada son raina ba, sau dayane ummi fyade yayimin wallah.." Kuka yaci karfinta ta kasa ci gaba da maganar, Aisha ma kuka take sai aka rasa mai lallashin wani dakyar jawahir ta fitar da ita daga dakin sai kallon umminsu take tana sake cewa "ummi kiyi hakuri bazan sake ba" jawahir ta tsaya tana kallon ta sannan tace "idan Na sake ji kinyi magana saina kwada miki mari" shuru tayi da bakinta amma hakan bai hana ruwan hawaye zuba ba, sai da suka kaita kan gadon dakinta sannan suka fito, shuru taji Dan babu kawayenta ko daya, sai a lokacin ta tuno da zainab, to meya hana zainab zuwa? Daga baya ta share taci gaba da kukanta. Kanta Har wani irin ciwo yake, tun tana tunanin shigowar Ango har ta cire rai, batareda ta cire kayan jikinta ba ta kwanta tana tunanin halin rayuwarta har bacci ya dauketa.

Saifullahi kam ji yake kamar damuwarsa ta ragu ta wani gefen amma inya tuno saura kwanaki malam ya nemeshi sai hankalinsa ya tashi, kwantawa yayi yana tunanin juwairiyya bacci ya daukeshi, ai juwairiyya kam ranar idonta baiga bacci ba, kwana tayi kuka, abubuwa duk sun hade mata.

Daga gidan su kabir aka kaiwa su khadija abincin safe, lokacin tana zaune a daki tun kayan jiya ne ajikinta taji ana buga kofa, tashi tayi taje ta bude sai taga wani mutum da kulolin abinci, dakyar suka gaisa ta karbo kulolin bayan ya fada mata daga Inda yake.

Ajiye kulolin tayi kitchen Dan batajin ko ruwa zata iya sha, balle me gidan ta tabbatar ba a gidan ya kwana ba.

Sai shabiyu har ta wuce ta gaji da zama tayi wanka amma babu kayan sawa Dan bata gansu a dakin ba kayan jikinta ta maida babu dadewa aka sake kawo abinci tafito da kulolin dazu ta bayar batareda ko taba abincin anyi ba, kitchen ta kai ta ajiye tana tunanin yadda mutumen daya kawo abinci yake kallonta, mikewa tayi ta shiga Neman dakin da aka kai mata kayanta, duka dakunan abude suke sai a nakarshe ta kai hannunta zata bude sai taga an bude kofar, karo sukayi da kabir taja baya kadan tana kallon kasa, shuru bataji ya wuce ba, kafin ta Ankara sai saukar mari taji yace "gidan uban naki ba'a koya miki gaisuwa bane"? Muryarta Na rawa ta durk'usa tana gaidashi, mai makon ya amsa sai yayi tsaki ya harareta yana cewa " useless kawai, wallahi kin debo ruwan dafa kanki, maza ki shiga ki kwashe min tarkacen kayan can naki kafin Na dawo kuma bana bukatar sake cin karo da mummunar fuskar nan taki, idan kika sake ko hango nayi daga nesa a cikin gidan nan saina falla miki mari" jikinta na rawa ta afka dakin, akwatunanta ta janyo ta fito dasu da sauri ta koma dakin da aka kaita tashigar da kayan, saboda zafin Marin har kunnenta taji ya soma ciwo.

Kwanciya tayi a kasa ta fasa kuka, daga kawota jiya har miji ya soma marinta, anya kuwa kabir ne? Kabir dinda ya saba da nuna mata soyayya, kullum adduarsa kada Allah ya raba su, kullum burinsa shine aurensu, dama duk yaudarace da cin amana tana kuka tace "Indai kabir daya rabani da martaba ta bai soni ba, Na tabbata wani namiji ba zai taba sona ba, zan kuma ci gaba da yiwa kabir Allah ya isa Allah ya kwatomin hakkina, idan bai canza ba yaci gaba da musguna min Allah karka nunamin ranar da zan tausaya masa Na furta Kalmar yafiya agareshi, Allah ka nuna masa Kaine sarki" a kasan ta wuni tana dawainiya da yunwa har laasar, kanta Na ciwo sosai ga yunwa, bazata tuna yaushe rabonta da abinci ba.

"Mutumin banza mutumin Wofi, ni zaka janyowa aya da hadisai, babu Wanda ban sani ba, daga baya kenan ko? Inace nan akazo a gabana, a gaban mahaifiyarka da matarka aka kawo yarinya da ciki kace kai ba naka bane, daga baya da aka haifi yaro babu ta Inda ya baro ka, haka mahaifin yarinyar nan ya kawo min Dan nan a cikin gida ya tafi ya barshi, baiwar Allah juwairiyya, itace ta rufa maka asiri bayan tasan duk abubuwan da ka shuka da bin matan da kakeyi bata taba kawo kararka ba ina kuma da tabbacin ko a gidansu babu Wanda yasan abinda ya faru, bakada labarin nasan irin zaman hakurin da takeyi dakai da yaranka, wace mace ce mijinta zaiyiwa wata cikin shege har tayi imanin rike abinda aka haifa, amma baka ganin darajarta baka taba son abinda take so ba, ko ruwa pure water zata maka tuni akan babu sai ta ringa shirya kalamai tana warwarewa saboda karka hayayyako mata, wai kai nan babban Malami ko? Haka malaman sukeyi? Baka San kowa da komai ba sai kanka, harda nuna tashin Hankali wai kai anyiwa yarka ciki to kasani shi Allah ba azzalumin sarki bane, ko yanzu idan kai mai hankaline ka gama ganin wa'azi a rayuwarka, kuma  bari kaji daga yau sai rana mai kamar ta yau kar insake ganin kafarka a cikin gidan nan sai idan ni Na nemeka, kuma ni nace juwairiyya in bazata iya zaman aure da kai ba yanzu gara Ku rabu idan taga dama tace zata iya shikenan amma dole sai ka gyara Dan haka sekaje wurinta karka sake zuwa wurina"

Tunda ya durkusa agaban malam, malam bai barshi yayi magana ba bai kuma bashi damar yi ba har ya sallameshi, dakyar ya iya mikewa yakai kanshi gida, yana kuma da tabbacin kafin washe gari idan ba a dauki gawarsa ba za a daukeshi zuwa asibiti.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now