6

122 17 0
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

                        *6*

Subhanallah ! Shi ne kalmar da ya fi to a bakin su, cikin tashin hankali su ka zo ƙanshi domin ba shi taimakon gaggawa. Hajiya da Ɗanta Imrane ƙanen Almustapha sai kuka su ke a ganinsu mutuwa zai yi, haba Hajiya me ye haka? Da girmanki da komai za ki tsaya kuka maimakon ki masa addu'a. Alhaji yarona ya na kwance tamkar gawa ka ke maganar girma? Oh Ni A'isha na shiga uku! Ɗaga wannan ta shin hankalin sai wannan, Ya Allah ka ya fe min idan har wani laifi na maka ka ke jarabtata da abubuwa iri iri. Da haka ta dauko ruwa mai sanyi ta zuba mai a fuska bai motsa ba, ta kara zuba mai nan ma shiru cikin damuwa ta zuba mai sauran ruwan da ya yi saura ajiyar zuciya ya sauke ya miƙe a zaɓure suka riƙeshi kokarin fisgewa ya ke ya na kuka ya na cewa, "Don Allah Abba kada ka min wannan hukuncin ka jikaina ka taimaki rayuwata, Maryam ita ce Ruhina kana rabamu zan iya mutuwa ka yi hakuri don Allah Abba ya ida maganarsa cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro." Da sauri Hajiya A'isha ta kai dubanta ga ɗanta da kuma mijinta, domin ba ta fahimci maganarsa da kyau, ta zuba ma mijinta idanu ta na jiran karin bayyani, shi kuma ya kawar da ƙanshi gefe irin baya son wasa ɗin nan, tausayin yaronsa ya rufeshi Almustapha mutum ne mai tsananin jin kunyarsa tabbas Maryam ta samu gurbi mai girma a zuciyarsa wani gefe a ranshi ya na mai ce mai ya janye kudurinsa, amma ya ɗanne dole ya nuna masa kuskurensa na niyyar rabuwa da Maryam da ya yi, dole ya san cewa Maryam mai daraja ce da kuma tsada ta hakan zai kara riƙe ta da muhimmanci.

Ka min shiru! Ba zan yarda da wa'innan kallamanka na karya Almustapha, Maryam diyar Aminina ne ba zan lamuci ka tozartata, da bakinka ka ce a raba auren, ɗan uwa**ka giya kasha a lokacin da ka yi furucin? Saɓar rashin kunya da rashin ta ido a gaban iyayenta fa ka yi maganar, yan zu da ta samu lafiya za ka wani cewa a ya fe maka kuskure ne? Ka yi kaɗan ka ji na gaya maka. Ƙshedi na na ƙarshe shi ne ka gaggauta kawo min  takardar Maryam nan da sati ɗaya Hajiya ta na niyyar yin magana ya daga mata hannu ya bar wajen domin dariyar da ya ke neman ƙubce masa yadda Almustapha ke kuka da kuma yadda matarsa ta haɗe rai idan ya cigaba da zama a falon za su ƙaryar masa da zuciya ya hakura shi kuma bai shirya yin hakan a yanzu.

Ya shige dakinsa ya barsu a falo cikin tashin hankali.

Mum ki yi wani abu Please Abba fa da gaske ya ke ya karasa maganarsa tareda kwantar da ƙanshi bisa kafafunta, yi shiru hakanan mana tamkar ba namiji ba, duk laifinka ne ai nima a lokacin ka bani haushi amma ka shiga dakinka ka yi wanka ka zo ka ci abinci In shaa Allah zan samu mahaifinka muyi matanar. Cikin murna ya miƙe ya nufi dakinsa zuciyarsa ta masa sanyi. Da ido Hajiya A'isha ta bi Ɗanta har ya ba ce mata shi dai Imrane murmushi ya ke domin yayansa ya birgesa matuƙa, shi ma Allah ya hadasa da mace tagari wace za su yi soyayya irin na yayansa.

*Maryam*

Sai wajen karfe biyu na dare ta farka tareda addu'a a bakinta, mahaifiyarta ta yi hamdallah tareda nuna godiyarta wajen Allah ta taimaka mata wajen mikewa su ka shiga banɗaki, ta gasa mata jikinta sosai ɗaga bisani ta ja mata kofa domin ta yi wanka a tsanake.

Wani irin farinciki ta ke ji a zuciyarta ba ta san me ya sa, wani irin natsuwa na shigarta Almustapha ne ya fado mata a rai ta yi murmushi ya na can ya na barci da haka ta yi wanka ta fito duk jikinta babu kwari, baƙin gado ta zauna Hajiya Amrah ta kawo mata turarre ta fesa tare da ba ta ruwan rubutun da malam ya ce a ba ta tare da shayi mai kauri ba ta yi musu ba ta amsa ta sha ta zura rigar barcinta ta yi addu'a mahaiyarta ta kunna mata kira'atu bakara  nan da nan barci ya kara yin gaba da ita. Ajiyar zuciya Hajiya Amrah ta sauke ta na jin tausayin ɗiyarta tillon ɗiyar da Allah ya ba su yarinya karama ta shiga jarabawa iri iri Allah da ikonsa komai ya zo ƙarshe yanzu ɗiyarta ma za ta ji daɗin aure da farinciki tamkar kowa, gefenta ta kwanta ta jima kafin barcin ya dauketa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now