4

1.3K 145 13
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

   ......MABUD'IN WAHALA

*04*
   
Sameerah data koma gida cike da kunya ta sanar da Umma zancen turo iyaye da Ya Nurah zai yi, Tayi murna sosai tace zata sanar da Abba tare da mata addu'o'i.

    Washegari Lukman yazo gidan gaishe da iyaye, Yayi b'arin kud'i ba kad'an ba, Allah yayi sa mutum mai kyauta, kowanne d'aki sai da ya ajiye rafar d'aki biyar, Yara ya bisu da dubu d'aya, Gaba d'aya gidan ranar zancen Lukman ake ana fad'in Rahma ta samu mai kud'i, Da yawa na fatan yaransu su samu kamar shi, Rahma jin kanta take a sama, Gwaggo sai washe baki take kamar gonar auduga.

   "Allah ya miki albarka ya'ta yau kin siya mun girma a gidan nan", Cewar Gwaggo, Rahma ta wani k'ara tura Dan' kwali gaban goshi tace " Amin Gwaggo, yanzu za'a fara kece raini", "K'warai kuwa" Ta fad'a tana bata hannu suka tab'a tamkar k'awaye.

    Zuwan Lukman da rabon kud'in da yayi sam bai girgiza Sameerah yasa taji ba dad'i kasancewar wanda zata aura bashi dashi, Kullum fatan ta da burinta su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    Lukman da yajewa iyayensa da zancen auren Rahma, basu nuna damuwar su na talaka bace, fatan su yayi aure shine burin su, K'annen sa uku sunyi aure, biyu mata, d'aya namiji mai shekara ashirin da biyar auren gata aka masa.

    Iyayen Lukman hamshak'an masu kud'i ne, Mahaifinsa Sabi'u k'osa ne a cikin gwamnati dashi ake damawa, Mahaifiyarsa ma tana aiki a NNPC, gidansu yan boko ne, kowa nada yancinsa babu takura, iyayen nasu basu ma wani zauna gida ba balle su sa ido a al'amuran su.

*ZEELISH*
*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

   ......MABUD'IN WAHALA

*05*
   
Rana d'aya aka tsayar iyayen Lukman da Ya Nurah zasu so, Iyaye maza suka bayar da kud'i ayi cefane ayi girki na tarbar su, Gwaggo tace sam bata yarda a had'a musu girki ba, Iyayen Lukman masu arzik'i ne taya za'a had'a da na Nurah, Sai da Mijinta ya mata jan ido, Tayi shiru, Wurin aikin tana ta yada habaici, Umma bata d'aga kai ba balle ta tanka.

     "Masu arzik'i ake wa abun arzik'i", Cewar Gwaggo tana juya tukunyar miya, Rahma tace " Wallahi kuwa", Haka sukayi ta yada habaici har aka gama aikin.

    Bayan sallar azahar, Iyayen Nurah suka fara isowa, Cikin shiga ta kamala da ka gansu, kaga wa'inda addini ya zauna ma, Umar (Dan' wajen jabir) ya musu iso cikin babban falon gidan.

   Abu yaro dan' shekara goma, jikan gida ya shigo da gudu, Yana fad'in "yan gidansu mijin Ya Sameerah sunzo a mota d'aya mara kyau", K'aramin yaro an koya masa son abun duniya, Gwaggo ta kwashe da dariya tace " Yoo dama ai sai haka, wannan matsiyacin", Laure matar Sabi'u tace "K'ila ma hayar ta suka yi", Sauran yara da matan dake tsakar gida aka bushe da dariya.

  Sameerah da Umman ta na jiyowa daga sashen su, Sabgogin gabansu suka cigaba da yi tamkar basu ji ba.

   Ba'a jima ba, suka fara jiyowa jiniyar mota, Yara suka yi waje da gudu suna lek'e, Baba Yahuza ne ya korasu cikin gida, Kowa yana haki ya shigo da rige rigen kawo rahoto, " Motoci masu yawa da kyau ne suka zo ", " Daga ina?", Rahma ta jefo tambayar, Abu Yace "Neman auren ki", Tsalle tayi ta wani yi juyi, Gwaggo ta rafsa gud'a.

      An tarbi juna cikin mutunci da girmamawa, Bikin sati biyu aka saka, Duka iyayen basa so a d'auki lokaci.

    Sameerah da Rahma sunyi murna da jin ba'a d'ibi lokaci mai yawa ba, kowacce burinta ta kasance tare da masoyinta, Rahma akwai masifar son love kuma irin na novel take hangowa, Mace ta auri mai kud'i, ya dinga tarairayarta kamar k'wai.

    Sameerah ta idar da sallar la'asar tana azkar, Wayarta ta hau ruri, bata d'auka ba, har ta tsinke, Sai da ta kammala, Tayi dialing number masoyin nata, Ringing d'aya ya kashe, Ya biyo kiran, Ta d'auka fuska d'auke da murmushi tamkar tana gabansa,

" Tauraruwar mata, nasan yau kina cikin farin ciki kamar yadda nake ciki", Tayi dariya ta yadda ya jiyo sautin, "Allah ya nuna mana ranar aure lafiya", " Amin", "Ina matuk'ar sonki Sahibata", Cikin da jin kunya tace " Nima ina k'aunarka Sahibi na", "Allah ya barmu da k'aunar juna", " Amin", Haka suka cigaba da hirar soyayya har kusan minti 30.

  Rahma keta dialing number Lukman bai d'auka ba, Taja tsaki a karo na ba adadi, "Wai shi sai ayi ta kiransa baya d'auka", Ta jefar da wayar cike da takaici, Wunin ranar cikin jiran kiransa take shiru, Sai b'ata rai take, Gwaggo tayi ta tambaya meke damunta, sai tace ba komai.

   Goma na dare tana shirin bacci, Kiransa ya shigo, farin ciki ya ziyarce ta, Ta d'auka tana sauke ajiyar zuciya, " Ina ka shigo yau?", Ta fad'a kamar zatayi kuka, "Am sorry babyna, na zama busy, ina ordering furnitures da za'a saka gidanmu", " Wow" Ta fad'a cike da murna, "So Ya kike?", " Lafiya lau", "Gud, ina so ki fad'awa su Baba kada su wahalar da kansu yin kayan d'aki", Ba tare da cewa da wani musu ba, Tace " Toh zan gaya musu", Yayi mamakin saurin amsawar ta, Ya basar "Zan kwanta, na gaji", " Toh sai da safe", Ya kashe wayar.

     Ta fito falo tana fad'in "Gwaggo Gwaggo Lukman Yace kada ayi komai na kayan d'aki shi zai yi", " Kaii Allah mun gode ma, Wannan yaro d'an albarka, ya'ta da k'ashin arzik'i kike", Haka suka yi ta murna.

    Umma da Mahaifin Sameerah dama sun dad'e suna mata tariyar kayan d'aki, Gidan Nurah dama ba wani babban gida bane, D'aki d'aya ne da falo sai kitchen, toilet da tsakar gida.

   Gwaggo da ta sanar da Mahaifin Rahma, Yace "Atafur bai yarda akai Yar' sa ba kayan d'aki salon a mata gori", " Wane irin gori, da kake cewa ma muyi mata kayan d'aki kana da kud'in sa irin nasu ne", "Idan munsa namu su cire su sa wanda suke so, amma sai an kaita da kayan d'aki", Rahma ta fashe da kuka tana fad'in " Wallahi Abba zasu raina ni, idan aka kaini da kayan d'aki ba masu tsada ba"

   Baki sake yabi ta da kallo Yace "Ahh lallai, ina k'ok'arin yi miki gata da siyan miki mutunci, toh ai shikenan kin hutar dani, kayan da na siya zan kai a k'arawa Sameerah, kije ba kayan d'aki duk abunda ya biyo baya ba ruwana", Ya kad'e rigarshi ya tashi.

   
    *Bayan sati d'aya*
Ranar asabar ana ta shirye shiryen tarbon lefen su, Yan' uwa duka ana sashen Gwaggo sanin yar'ta zata auri mai kud'i, Sameerah da Umma sam basu damu ba,

    Da misalin k'arfe hud'u yan gidansu Lukman suka fara zuwa, kallo d'aya zaka musu kasan hamshak'an masu kud'i ne, da akwati goma sha biyu, da kud'in d'inki dubu d'ari,

   Kusan k'arfe biyar yan' gidansu Nurah suka so da akwati hud'u, Umma da yan' uwanta kad'ai suka tarbesu duka ana sashen Gwaggo.

    Sameerah tunda akayi azahar tayi wanka tayi ta shirya, ta fice zuwa gidan k'anwar Mamanta, Rahma kam gayu taci ita a dole sai taga akwati nawa za'a kawo mata, idan dangin ango sun buk'aci ganinta zata fita su gaisa.

    Dangin Lukman kuwa sun buk'aci ganin ta, Ba musu ba, Ta fito suka gaisa suna tsokanarta, kasancewar su yan boko basu d'auki abun komai ba.

    Ranar Umma da Sameerah sai da suka kai zuciyar su nesa saboda irin cin kashin da aka rik'a musu a gidan, Umma sai da taji tamkar ta tanka wata zuciya ta hana ta,

   Fad'in suke Rahma tayi goshi ta gaji arzik'i, Sameerah kam akwai rashin arzik'i a tare da ita, Wahala ma zata sha idan tayi aure, Rahma zata gidan hutu.

    Sameerah kam ta yaba da lefenta Kuma taji dad'i, bata d'auka Nurah zai yi haka ba.

    Tana shirin kiransa, nasa ya shigo,
"Sahibata kiyi hak'uri da abunda kika gani nasan ban kai k'arfin mijin Rahma ba", " Haba Ya Nurah ka bani kunya wallahi, ya kamata kasan hali na, a rayuwa ai dole wani yafi wani, ko yatsun mu ka duba tsawon su ba d'aya ba, ni ban damu ba wallahi, Kuma kayi matuk'ar k'ok'ari, naji dad'i sosai, Allah ya k'ara bud'i na alkhairi"

    Natsuwa da farin ciki yaji ta saukar masa, tare da k'ara ma Allah godiya ya had'a sa da mace ta gari, mai hankali da hangen nesa.

*ZEELISH*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now