Shafi na shida

1.9K 206 12
                                    

*MUTUNCIN MACE........*

*TARE DA ALQALAMIN....*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

        0⃣6⃣

     "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musubati wa akhlifni khairan minha" ita kawai usman ke maimaitawa fili da b'oye,tunda uwarshi ta kawoshi duniya bai tab'a fuskantar tashin hankali makamancin wannan da yake ciki ba,saidai yan rok'ar sauk'i da samun d'auki daga wajen ubangijinsa.

      Cikin ikon Allah Allah ya kawo k'ani ga mahaifin usman,wanda yake ma'aikin tsaro ne yana kuma da muk'ami babba,ya tadda maganar hankalinshi ya tashi,saidai ya kwantar musu da hankali yace kada su sake neman masu garkuwa,sannan su ajje kud'in,suci gaba da addu'a zasu shiga binciken lamarin,saidai baiso kowa ya sani suyi shiru da bakinsu,hakan ce kuwa ta kasance,addu'a da sadaka suka tashi yi babu dare babu rana.

       Allah maji roqon bawansa. Ranar sadakar bakwai d'in khairat Allah ya amshi addu'arsu husna ta kub'uta,bisa jagorancin k'anin mahaifin usman d'in,wanda suka tsaya ka'in da na'in cikin kwarewa da hikima irin ta jami'in tsaron da yasan abinda yake,har suka ci nasarar kama su,mutum hud'u ne da aika aikar,d'aya daga cikinsu ma ashe a nan layin gidansu yake,yana da shago da yake sana'ar wanki da guga,sosai abun ya d'aure kan usman,saboda suna gaisuwar mutunci da matashin,saidai daga baya duka bincike ya nuna babu mai laifin kaman badariyya,tunda sun jima suna kula da shige da ficen kowa dake layin,abun sai ya fad'a kanta kasancewar duk cikin masu dabi'ar yawace yawacen mijinta yafi nasu danshi,ko sun debi yaran sauran ba wani kud'in arziqi zasu samu ba,da Allah ne kad'ai yawan yaran da zasu d'iba d'in.

       K'arfe bakwai na maraice ya shiga d'akin da badariyyan ke zaune tunda suka zo gidan,ita d'ayace zaune zugum tana baiwa khairiyya nono,saidai baki d'aya hankalinta ba a wajen yake ba,ita d'aya tasan kalar tashin hankalin da take ciki,bata da nutsuwa sam,bata tab'a zara fita maqotan da take kullum ta Allah zai jaza mata matsala ba a nata d'an gajeran tunanin,uwa uba yau ta tasamma kwana hud'u rabonta da tasa abban khairat a idanunta,saidai ta jiyo muryarshi a falo yana gaisawa da mahaifiyarsa,ita kanta tasan aurenta lilo kawai yake koda ba'a fad'a ba.

     Inuwarshi kawai ta gani gami da sautin sallamarshi cikin d'akin ba tare data zata ba,cikin hanzari da rawar jiki tana gyara zaman khairiyya dake kan cinyarta ta amsa masa muryarta na rawa kana ta hau gaisheshi,amsawa d'aya yayi mata sannan ya jingina da k'ofar d'akin,tashi d'aya ya zabge ya rame,kana kallon fuskarshi kasan walwala ta kasa k'aura,usman mutum mai yawan fara'a da sauk'in kai.

       Sunanta ya kira a maimakon momyn khairat da yaje fad'a wanda ya sanya cikinta juyawa,lokaci guda taji tana buqatar ziyartar bayi,saidai a yanzu ba bayin ne mafi muhimmanci ba a gabanta maganar da yake tafe da ita ita tafi mata muhimmanci,d'orawa yayi da cewa
"Allah ya sani a iya zamana dake na fita duk wani haqqinki kuma ban cuceki ba,ban tauyeki da komai ba,nayi iya yina wajen gyadan dabi'unki da tarbiyyarki amma kika bijirewa hakan,hankalinki mai bankwanta ba sai da kika dasawa rayuwata bak'incikin da bazan mance da shi ba....." Shiru ya d'anyi yana k'utawa ba don ya gama fadin abinda yake son fadar ba,shiru tayi tana goge hawaye
"Kaman khairat....kaman khairat ace har wani yaso lalatamin rayuwarta badariyya kina me?....." Mummunar fad'uwar gaba ta sameta,cikin rawar baki tace
"Wa......waye ya gaya maka?"
"Mutanen da kike zaton sune marufar asirinki mana" ya fada yana bude murya cikin takaicin yadda ba kunya sunzo masa gaisuwa basu barshi da abinda yake ji ba suka tsokano labarin,karma habiba taji labari don tafi kowa zaqewa da bayanin kan idonta abun ya faru tana sake kambama zancan  kamar wani abun arxiqi ne,bak'in ciki da mamakin butulci irin na mutanen ya lullub'e zuciyarta,ashe?,ashe su ba wajen sirri bane?,maganarsa ita ta katse mata tunaninta
"Kinyi nasarar samun abinda kike so,badariyya bazan iya ci gaba da zama dake ba,na yanke shawarar barinki kije ki rayu da mutanen da kike ganin sune farincikinki" ya k'arashe maganar yana saka hannu a aljihunsa ya fiddo da farar takarda aninke ya miqa mata,kai ta soma girgizawa kuka ya balle mata
"Haba abban khairat,kada ka yimin haka mana,ka barni da abinda ya sameni ma na rasa d'iyata,don Allah ka barni na rayu da biyun da sukai saura" cilla mata takardar yayi cikin b'acin rai
"Rasa d'iyarki?,shin waye sila?,wad'annan da kike magana akansu kuma yaushe kika soma damuwa da tasu rayuwar?,wake da tabbacin ba zaki aikata makamancin abinda kika aikata ko ya faru kan khairat ba?.....,kar kiyi gigin tafiya da husna,kina iya ajjiye khairiyya idan kin tashi tafiya,don koda kin tafi da ita kwanaki k'alilan zanzo na d'auketa" yana kaiwa nan yasa kanshi ya fice daga gidan ma baki d'aya.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now