5

1.1K 107 7
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 5

"Ohh Ku masu ba a fada ko, to bazan yadda ba wannan karon duk abinda kakeji dashi nima ina ji dashi kuma wallahi sai Na dauki mataki, Abu Na karshe da zan tunatar dakai idan ka manta shine baka isa ka yiwa Allah wayo ba" tana gama fadar haka ta kama hannun khadija ta mikar da tsaye, bata tsaya sauraren ihunsa ba ta shiga dakinta da ita, wanka tayi mata da ruwa mai zafi sannan ta kwantar da ita.

Zama tayi gefenta tana danna wayarta kafin ta kara wayar a kunnenta tayi sallama.

Saifullahi ko juyawa yayi yabar gidan bai tsaya ko ina ba sai gidansu kabir, yayi Sa'a mahaifinsu Na nan, Alhaji maishinkafa kuwa jin Malam saifullahi ne a gidansa yasa aka bashi izinin shiga palonsa, saifullahi mutum mai hankali da girmama mutane, zama yayi suka gaisa sosai sannan saifullahi ya soma magana "Alhaji bance Na gani ko kuma ina shaida ba amma khadija yata tana dauke da ciki, Na matseta Dan dole ta fadamin wanda yamata cikin sai tace kabir ne Dan nan gidan Allah shine mafi sani, ka taimakeni rayuwar yata ta lalace da ranar wani akanta, banida wata shaida ko hujja da zan bayar amma tun daga irin kulawa da tsaron da nake bawa khadija har ta iya aikata haka nasan bazan taba bada shaida akan dana ba, bansan taya zaka dauki maganar ba amma kayi min uzuri ina cikin tashin hankali" kallonsa Alhaji yayi sannan yace "nima din ban gani saifullahi amma wallahi nasan kabir zai aikata, ai wannan ba shine na farko ba, kwanaki haka aka kawo min kararshi shida wani abokinsa sunyiwa wata yarinya fyade wallahi dakyar Na kashe maganar nan, yanzu kaima hakuri zaka yimin kaddarace tana kan kowa babu abinda zanyi bayan in baka hakuri sai kuma shi wancen mijin nata abashi hakuri akuma duba idan cikin nan bai kai wata biyu ba azubar dashi" saifullahi ya dafe kansa Na minti biyu sannan ya dago yace "yanzu nake son haduwa da yaron in masa bayani bazan cuceshi ba bakuma zanga laifinshi ba Dan ya fasa dole ne yaji, nikaina hankalina zaifi kwanciya idan kabir din ne, ina jin tsoron taje ta auri wani ya wulakanta min ita" sosai Alhaji ya tausaya masa sai yace "yanzu kaje gida insha Allahu komai zai zo da sauki zanzo har gidan in sameka, Allah ya shirya mana zuria" dakyar ya amsa da ameen yafita daga palon, a hanya ma saida yayi tafi mai Dan nisa sai yayi parking ya dafe kansa dake masa ciwo sosai, wayarsa tayi kara yaduba yaga Abdullahi ne yake kiransa, dagawa yayi murya a sanyaye yayi sallama ya amsa gaisuwar da Abdullahi yake masa yace "Abdullahi kana ina? Inason ganinka" sai yayi shuru yana sauraren Abdullahi dake masa zancen gidansa daya kammala aje agani, "mu hadu a kofar gidana yanzu" haka kawai ya fada ya kashe wayar.
Kusan lokaci daya suka isa Abdullahi yazo da sauri yana kallon yanayin Abbansu Nana, jikinsa yayi sanyi yayi tsaye yana kallon kasa, saifullahi yace "Abinda yasa Na kiraka magana CE akan khadija. Abdullahi yanzu kafi karfin khadija Sam batayi dace da samun miji kamar ka ba, yau din nan akan rashin lafiyar da take Na kaita asibiti, abin mamaki wai khadija ce da ciki, nikuma bazan cuceka ba shiyasa Na sanar dakai Na kuma fasa baka aurenta, zan hadata da abokin lalacinta can su karata, kai kuma kaje idan Na gama da matsalar ta zanyi magana da abbanka zan kuma neme ka" tunda ya ambaci ciki ajikin khadija jikin Abdullahi yake rawa amma sai ya dake har seda yaji saifullahi yayi shuru sannan yace "Abbu wallahi ina sonta, irin son da bazan iya misalta maka shi ba, idan ka rabani da khadija saboda wannan baka yimin adalci ba, nayi alkawari bazan taba wulakanta ta ba, Abbu yanzu bazan saurareka ba zan tafi injira har lokacin da ta haihu. Cikin jikinta bazai rabani da ita ba, wata kila Abbu idan Kunyi bincike fyade ya mata batayi kamada mazinaciya ba" saifullahi mamaki ya kamashi, har yaushe Abdullahi zai bari soyayya ta rufe masa ido, baya tantama khadija ita takai kanta babu wani fyade saboda shegen rawar kanta, kafin ya gama tunaninsa sai jin karar mota yayi, Abdullahi ya tafi, amotar ma yakasa rike hawayen da suka taru a idonsa, yaji haushi saboda me khadija zata masa haka, idan bazata iya hakuri ba da ta fada shi ko cikin azumine sai ayi auren.

Kwana biyu ya kara a nageria ya koma Sudan yan gidansu babu Wanda ya fadawa wannan maganar sai mahaifinsa shima Dan yanaso ya sake lallashin mahaifin khadija ne yasan yana jin maganar Abban nasa.

Saifullahi yau koda ya dawo aiki sai ya samu an raba masa filin gida biyu anja sabon gini, mamaki ya kamashi yashiga gidan da sauri sai yaga anrufe kofar korido din dake sadashi da part din juwairiyya babu wata hanya kuma da zai ganta, wani irin tashin hankali yazo masa da sauri ya zaga sai yaga an huda karamar kofa ta ginin baya, ya shiga yana kallon Wanda yake masa wannan Karen aikin, Gabansa ya fadi ganin Malam zaune akan kujera da Qur'ani a hannunsa yana karantawa, kafin yagama tunaninsa yaji Malam yace "ina jiran takardar sakin juwairiya daga yau zuwa karshen watan nan, kwana goma sha biyar kenan, sannan kuma Na haramta maka shigowa wannan sashen zatayi zaman yayanta kuma idan ta samu miji mai hankali da kamun kai zatayi aure taci gaba da zama anan gidan.

Tashin hankali goma da ashirin jikinsa ya dauki rawa yasan Malam baya magana biyu daya yakeyi kuma zaunanna.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now