5

115 14 1
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

                        *5*

*Yan Haske ina alfahari da ku, Haɗin kai kaunar juna tsantsar damuwa da juna uwa uba bawa juna shawawari babu kyashi ko nuna hasada kai abubuwan da yawa fa yadda kungiyar ta ke a Haske💡 haka zuciyoyinsu ya ke a haskake, ina sonku gaba dayanku Allah Ubangiji ya dawammar mana da farinciki basira kwanciyar hankali a ƙungiyarmu Allah ya kara mana haɗin kai ameen ya Allah ameen.*
____________________

Wani baƙin ruwa mai warin gaske ya ke fitowa a al'aurarta ai da gudu Almustapha ya fita a daƙin duk ya dimauce, yunƙurawa Maryam ta yi domin abin ya yi matuƙar ba ta mamaki ta shiga leka kasanta ba ta ga komai ba, haushi ne ya rufeta wannan ai rashin mutunci ne ta fada a bayyane mtsss ta ja dogon tsaki ta yi kwanciyarta nan da nan barci ya saken yin awan gaba da ita.

Almustapha ya na kai falo ya ja ya tsaya saboda bai san me zai ce musu idan sun ganshi a hargitse, ajiyar zuciya ya sauke lamarin ya wuce tunaninshi yanzu ba zai taba samun kwanciyar hankali a wannan ƙaddararren auren mai tattare da kaluɓale iri daban daban, ba dan kada iyayensa su yi fushi da shi da ya saki Maryam a yau ba sai gobe ba, haba ya ga ji ya ga ji kusan shekara uku ana abu ɗaya? Da haka ya yi sallama ya shiga falo ya samu guri ya zauna, amsa masa sallamar aka yi duk da ya na kokarin ɗanne damuwarsh sai da mahaifinsh ya ga ne Akwai matsala tambayar duniyar nan ya ki sanar dasu komai da su ka dameshi ma kuka ya fashe musu da shi,

subhanallah! Almustapha ya haka? Inji mahaifin Maryam, "Abba ɗan Allah ku raba mana wannan auren..." Bige mishi bakin da aka yi shi ne ya katse mishi sauran maganganun da ya ke shirin yi, ya ɗago fuskarshi da sauri domin yaga waye ya mishi wannan aika aikan ido biyu suka yi da Abban shi ya tsunkuyar da kanshi kasa bai ce komai ba. sai  wani bakinciki da ya ke turnuƙe shi a kasan zuciyarshi idanunshi sunyi ja sosai.

"Dama baka da hankali Almustapha? Ina maka kallon mai wayyo da sanin ya kamata ashe ba haka bane? Idan na kuma jin kalmar saki ta fito daga bakinka zan saba maka wall..." A'a Alhaji kada ka yi rantsuwa don Allah ka daina mishi sawa da kuma fada, dai-dai gwargwado yaron nan ya yi hakuri shi fa ba dutsi bane ba kuma katako bane an shiga hakinshi da yawa shekara uku ba kwana uku ba ne Alhaji. Inji mahaifin Maryam ya rungume Almustapha ya na shafa bayanshi har ga Allah ya na ƙaunar yaron da zuciya ɗaya natsuwrsa da kuma ladabinsa su ke burgeshi. Tsayin minti ɗaya suna tsaye ɗaga bisani ya zaunar da shi kusa dashi ya shiga bashi hakuri akan ya bari idan malam ya zo yau matsawar babu wani cigaba da kanshi zai raba auren, sai a lokacin wani irin kunya ya lulluɓe Almustapha ya tsunkuyar da kanshi bangare guda na zuciyarsa son matarshi na nan daram. Shi dai Alhaji Mahmud bai kara cewa komai ya zuba musu idanu kawai. Suna tsaka da hira sai ga malam yayi sallama a baƙin falonsu tare ya ke da wasu almajiran shi guda uku, amsa masa aka yi tareda bashi wajen zama. Sun gaisa a mutunce ya fito da wani ɓido cike da ruwan rubutu tareda wasu maganunan da za ayi turare da su, ya  umurci a kira mishi Maryam ko barci ta ke a tadata ta yi tsarki da wannan maganin ya miƙa ma mahaifiyarta ta kuma yi alwala ta zo. Haka ko akayi da taimakon mahaifiyarta ta yi komai ta sanya wani dogon riga marar nauyi da bakin hijabi har ƙasa suka fito a tare, ko inda Almustapha ya ke ba ta kalla ba iyayenta da na Almustapha kawai ta gaisar ta zauna a gaban malam. Nan malam ya umarci almajiran shi su rirriƙeta tamau haka ko akayi Almustapha ya na ji ya na gani saɓar bakin ciki bai san lokacin da ya runtse idanunshi, malam ya na la'akari dashi da duk wani abinda ya ke. Kanshi kawai ya girgiza ya fara karanto ayoyin Alkur'ani mai Sarki masu halaka aljani komin taurinkanshi fiske fiske Maryam ta farayi ta na gurnani malam ya cigaba bai daina ba falon ya yi tsit baka jin komai sai karatun da malam ya ke da kuma gurnanin da Maryam ta ke yi wanda ɗaga ji ba ita ba ce. Malam ka tsaya zanyi magana ka tsaya don Allah ina malam bai sauraraba sai karatunshi yake, malam... Ya ja sunan cike da azaba wallahi zanyi magana zanyi kana konani malam. Gara na konaki azallumi macuci ko kunya ba ka ji kana hadani da Allah Alhalin kai baka sanshi ba. Mallam wannan karan ashirye nake da na amsa maka tambayoyinka Ni dai kawai ka kyaleni haka ka daina konani ya karasa maganar cikin jin azaba da mawuyacin hali.
To naji zan saurara maka, tambayata ta faro ta yaya ka shiga jikinta ma'ana a ina ka hadu da ita? Me ya sa kake cutar da ita ka hanata zaman lafiya a daƙin aurenta? Shi kuma mijin meye laifinshi na gana mishi azaba da kake? Meye gaskiyar maganar da kake ikirarin kunada yara tare? Ina so ka amsa min wa'innan tambayoyin sannan ka min alkawarin fita a jikinta fita na har abada, idan kuma kaki na rantse da girman Allah zan konaka kurmus.

KUNDIN HASKE💡حيث تعيش القصص. اكتشف الآن