4

120 23 2
                                    

*KUNDIN HASKE*💡

*ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *home of expert and perfect writers*)

    *ƁOYAYYEN SIRRI*

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

    *NA* *RAHEENAT* ( *MRS❤️*)

                        *4*

Dukaninsu sun sadaukar cewa mutuwa za su yi cikin Ikon Allah tareda Addu'o'in da malam ya ke yi  motar ta tsaya cak, ajiyar zuciya suka sauke atare a hankali suka firfito Almustapha kawai ya rage a motar, Alhamdulillah Allah shi ne abin godiya, shi kam Alhaji Mahmud Sai tari ya ke ya na dafe da kanshi da ya ke matuƙar ciwo.

"Alhaji bamu da isasshen lokaci ku shiga Mota mubar wajen nan tun kafin wani lamarin ya kara faruwa, wannan dai Allah ya takaita mana da izinin Allah zai cigaba da tsaremu har mu isa gida lafiya." Inji malam. Hakan ko akayi dukaninsu su ka shiga Mota dirba yaja motar suka bar wajen.

Da isarsu gida suka sanar da Hajiya A'isha abinda ya faru ta yi mamaki sosai tareda al'ajabin wannan lamari, a tsakiyar falonsu aka shinfida Almustapha malam ya bukaci ruwan zam zam aka kawo mishi da ɗan kofi ya juye ruwan zam zam ɗin ya shiga tofa Addu'o'i cikin ruwan akalla ya dauki awa biyu kafin ya gama ya shafa ilahirin jikin Almustapha da ruwan bayan ya gama ya kalli Alhaji Mahmud ya ce,

"Alhaji ina so ka bani hankalinka, kamar yadda na sanar dakai Aljani ya saka mishi ciwon amma baya jikinsa, hakan yana faruwa sosai mutum zai samu lallurar ciwo rana saka ayi ta magani amma shiru a rasa gane ma ciwon, idan an haɗu da likitoci nagari nan ta ke za su ce ciwon ba na asibiti bane idan an hadu da macuta kuma za su yi ta amsar kuɗaɗe da zumar marar lafiyar zai samu sauki ashe duk karya ce su da kansu ba su san takamaiman meye makasuɗin ciwon, na takaice maka zance wa'innan mugayen aljannun aikinsu kenan su sakar ma mutum ciwo su tafi bawai sun bar mutum kenan ba A'a za su ɗan koma gefe suga yadda al'amarin zai kasance idan sun fahimci mutumin ya fara samun sauki za su kara dawowa domin saka mishi wani ciwon, kaɗan daga cikin ciwukan da suke sakar ma mutum: Ciwon kai, ciwon ciki marar jin magani, ciwon kirji rikicewar al'ada, ciwon mara ciwon qafafu...da dai sauransu bawai ina nufin duk wanda ya kamu da ɗaya ɗaga cikin wannan ciwukan da na lissafo aljani ne ya sa ka mai a'a wasu kawai ciwo ne na yau da kullum, amma idan har qunbi sharuɗan da zan fada maku da izinin Allah Almustapha zai warke, da farko ku daina kwana babu Alwala shi ƙanshi Almustapha ku mishi alwalal duk dare ku kunna mishi karatun Alqur'ani ku ajiye rediyon kusa da kunnenshi yadda zai ji karatun da kyau, ku yawaita sadaka Alhaji kuma sadaka yana kare mutum tattare da duk wani bala'i da musiba, akwai wani rubutu da zanyi da kaina na kawoshi jibi idan Allah ya kaimu zaku dinga shafa mishi ajiki sai ku ɗan bashi ya sha, idan har mun dage da wannan nan da lokaci kaɗan zai farfaɗo In shaa Allah." Godiya sosai suka mishi ya bar gidan.

Alhaji Ni dai wannan lamarin ya fara bani tsoro. Ni kaina Aisha abin ya wuce duk yadda muke tunani amma In shaa Allah komai zai zama tarihi da haka suka cigaba da tattaunawa ƙan abubuwan da suke damunsu.

Maryam.
Duk ta koɗe ta yi muguwar rama kullum cikin kuka ta ke da addu'a ubangiji ya kubutar da ita, yanzu azaba kawai ya ke gana mata da ya fahimci ba za ta taba sonshi, shi ne fushinsa ya hau kanta, duk da ya saka ma Almustapha ciwon da ya ke gani da wuya ya warke zuciyarsa ba ta yi sanyi ba, ya so ya kasheshi ne sai abin ya faskara. Cikin fushi da tiririn zuciya ya finciko Maryam ya yi sama da ita, tafiya suke cikin sararin samaniya sabar yunwar da ya ke damunta maganarta ma bata fita tafiya suka yi mai nisa sosai sai ga su a kofar gidanta, gidan Almustapha gidan da ba zata taba mantawa da ita ya jefar da ita kammaninshi babu kyan gani zara zaren yatsunshi ya zura mata a gabanta ta kurma wani uban kara ta fadi a kasa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now