4

377 42 1
                                    

*KUNDIN HASKE*

Alk'aluman marubutan Haske

_Babi na goma sha tara_

_HASKE  WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers

☆“☆ª☆_☾'☆•'☆´-'☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** '☆´-'☆´-

Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*

” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 04 qarshe da yardar Allah☆😂

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU 22*

*Yau dai na sauke nauyi na huta da yawan tambaya*

Yanzu har ƙofar gidan nasa ya kaisa, yako masa kyakkyawar biya, sanda ya buga ƙofar gidan sosai sannan baba me aikin nata ta fitto bud'e mai, daga ciki tace "waye ne haka, yace "me gidan ne, tana jin hakan gabanta ya fad'i, nan dai ta bud'e mai jiki a sanyaye, ya shiga da rufe gidan...
A tare suka jero dan shiga ciki tana mai sunnu da zuwa, ya amsa ba yabo ba fallasa, kana yayi shashinsa yana sak'a abubuwa da dama, wanka yayi da canja kaya yayi sallah  kana ya fitto falan, tsohuwar nanan inda ya barta, dan hankalinta ba qaramin tashi yayi ba, tana da waya amma ba kud'i a ciki, dan ita Sam bata saka kud'i a waya tunda ba kowa take kira ba, bare ta kira Safinan ta gaya mata megidan nata ya dawo, dan tasan me  zata ce mai idan ya tambaye ta ita, dan tasan dole zai tambayeta, toh yama za'a ya dawo gidansa bai tambayi matar sa ba...

Aiko katse mata tunanin nata yayi wajen cewa, "Har tsawan wane lokaci Safina ta d'auka tana fitta kwana a waje wajen tarewa da wasu mazan.

A furgice ta kallesa, yako d'aure fuska alamar babu wasa cikin tambayar da yayi matan.

Cikin in i na, tace "Allah ya wucci ranka uban gidana, gaskiya bazan iya tunawa ba, amma nasan, dai Salim da Halifa yaranka ne, dan bayan yaye Salim d'in ne abubuwan suka fara canjawa..

Yace "Me yasa baki tsawatar mata ba, Sannan baki gayamin ba, tace "Afuwa ranka ya dad'e nifa a qarqashinta nake, yin hakan gareta shish shigi ne, baya ga hakan ta qara min albashi, kuma anan kad'ai nake samun biyan buqatata na yau da kullum..

Yace "Wannan ba Hajju bace, Safina da yaranta dani kaina duk amana ne tsakanin mu, kinci amanata kin kuma ci amanar ita kanta Safinan,  wai ina kwad'ayi da san zuciya zasu kai mutane ne...
Ba irin abun da bana miki a rayuwa, amma saboda kwad'ayi da buri kin manta haka kin tsaya duba qarin d'an abin da tayi miki, wanda na tabbatar ba abun kirki bane, wai shine yasa ki qin tsawatar mata.

"Kayi hakuri ranka ya dad'e, insha Allah bazan qara aikata wannan kuskuran ba..
SA'EED ya tab'e baki yace "Ai da gaske kam bazaki qara aikata hakan ba, kin kira Safinan ne shigata ciki, tace "aa wallahi, dan wayar tawa babu ko sisi, yace "Ok, bani aran ta zuwa gobe, dan nima ba kwana zanyi a gidan ba, ina dai cikin unguwar, dan zan aiwatar da wani binkice ne, ya kai ƙarshen zancen da tashi, saita miqa masa wayar tata jiki a sanyaye..
Bayan ya karb'a shashin yaran nasu yayi, suna bacci hankali kwance, duk saiya manna musu kiss ya qara gyara musu kwanciya daja musu bargo, kana ya fitto yana ce mata suje ta kulle gidan..
Tace mai toh duk jikinta a sanyayen.
Wata motarsa yahau ya ficce ita kuma ta kulle gidan kamar yanda ya umarceta, mamaki take akan me yasa ya karb'i wayarta. "Allah dai ya nuna mana gobe naga mezai faru. Ta faɗi hakan abayyane.

Shiko dalilin dayasa ya karb'i wayar tata shine, baya san ta kira Safina ne ta gaya mata dawowar tasa, wannan yasa ya karb'i wayar tata, duk da yaji tace ba ko sisi acikin ta, zata iya fitta ta nemi yaro ya siyo mata kati ta kira ta idan taga ya fittan, wannan tunanin da yayi ne yasashi ce mata zaiyi bincike a unguwar tasu, dan ma karta fitto ta nemi wata wayar ta kirata...

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now