Shafi na hudu

1.9K 206 11
                                    

*MUTUNCIN MACE............*

*TARE DA ALQALAMIN*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

        0⃣4⃣

   Kai tsaye 'yan matan qofar gidan maman rahama suka durfafa suka soma qwanqwasa,ba jimawa aka soma tambayar waye sannan qofar ta bud'e.


     Maman rahama ce ta bayyana,tayi kyau cikin yadi ruwan madara da akayi masa adon brown,bayanta yaranta ne biyu rahama da abdur rahman ke biye da ita dukkansu tsaf cikin qananun kaya,baki d'aya idanunsa na kanta kowa da abinda yake kallo a jikinta,yayin da ita sam bata ma lura da su ba hankalinta na gun 'yan uwanta da take yunqurin basu hanya su wuce fuskarta washe da fara'a,sai da suka gama shiga tana yunqurin maida qofar ta rufe zubaida tace
"Haj maman rahma,ko magana babu?" Boyewa tayi a bayan qofar tana leqo da iya kanta bayan ta zare mayafin d'aya daga cikin 'yammatan ta lulluba saboda kada bisa kuskure wani yazo wucewa
"Ah,ai ban ganku ba maman hamza,ina yininku mun tashi lpy", karb'a kowa yayi banda badariyya data d'auke kai cikin takaici,ganin irin kayan da abban khairat ya kawo mata su jiya cikin kayan sallarta a jikin maman rahaman,har yake gaya mata kud'insa ya kusa dubu goma,sak kala ce kawai ta banbanta,haushi ya cikata,taci aniyar yau zata sanya abban khairat ya canzo mata wanda yafishi kyau da tsada,ko bai sauya mata ba sai ta saida ta sayi wani,don ba zata yarda ta rigata sakawa ba sannan a ganshi a jikinta daga baya,sam maman rahama ba mace bace mai d'aukan kanta da zafi,hakanan bata iya gaba ko qullaci ba,bare ma tasan a zahiri babu abinda ya shiga tsakaninta da badariyyan saboda haka ranta da fuskarta sake suka gaisa da su ta koma gida ta maida qofarta ta rufe.

      "Qannenta ne fa wadan nan,wai ko suma masu arziqi ne?" Inji lariya tana duban badariyya wadda tasan sun d'an jima tare
"Oho,burga ce kawai" ta fad'a wanda ita kanta tasan ba zata nunawa maman rahmar komai ba,koba komai ita d'in mai dogaro da kanta ce,ba cima zaune ba sai abinda aka samo aka bata,hakanan bata raina sana'a sabanin ita da take ganin tafi qarfin qaramar sana'a kamar d'inki da sauransu
"Kunga mu wuce don Allah sa taho kawai tunda sunsan gidan" cewar badariyya,haka suka d'uru suka wuce,suna tafe suna hira,duk inda suka ratsa baka jin komai sai tashin hirarsu.

      A qofar gidan amaryar da aka kawo wancan watannin suka tsaya suka wuce tare,itama mijinta matafiyi ne baya wata a gari,duk da bata kaisu fice fice ba amma kusan kullum ita d'inma tana maqota,saidai ita saita gama komai take fita,kuma iyakarta duk inda akayi la'asar ta koma gida,a haka aka shiga aka d'ibga mata sata itama har kayan lefanta amma hakan baisa ta saduda ba,saita yiwa mijin nata qaryar cewa b'arayi ne suka shigo tana cikin gidan,a yanzu haka laulayi take amma wannan bai sanyata zama cikim gidanta ta samawa kanta salama ba.

      Sanda suka isa gidan amaryar sun tadda 'yan uwanta mata uku maza biyu suna karyawa,suka gabatar da kansu a matsayin maqotanta,hakan ya musu dad'i suna fatar 'yar uwarsu ta samu maqota na gari,suka yi musu tayin tea bread chipa da qwai da suke karin da shi,basuyi qasa a gwiwa ba kowacce ta saki ciki da baki ta soma loda,amarya shafa'atu ce kawai tace ta qoshi,badariyya batayi qasa a gwiwa ba ta kwanto goyonta ta soma ci haiqan,duk da cewa tabar duk irin wannan kayan a nata gidan,amma ganda ta hanata tsayawa ta girkawa cikinta da yaranta,hakanan saboda tsabar zumudin son ta fita dama bai barta ta karya da ruwan shayin da biredin data barwa yaranta ba.

       'Yan uwan amayar sun d'anyi mamaki,amma sai suka share ganin yadda suka hau tayasu aikin jere tuquru,saidai yadda suka ga komai suka gani sai sun tanka sai ya soma d'aure musu kai,qauyanci ne ko ko tsabar sanya ido ne?.

      Har kusan azahar ana abu d'aya,saidai me?,d'aya daga cikin 'yan uwan amaryan ne ta fito falon ta soma shelanta b'atan sarqa da d'an kunnen gwal na amaryar wanda ke cikin kayan lefanta,take kowa yayi tsuru tsuru aka koma kallon kallon,maganganu suka soma tashi da sallallami,sannan aka fara dube dube cikin gidan.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now