Babi na 7 Zainab Bawa

2.6K 186 4
                                    

KUNDIN HASKE:-

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

K'UNGIYAR:-
   *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*💡
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA  AL-KALAMIN*🖋
*Zaynab bawa (zeeyybawa)*
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yaranmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA D'AYA*

*TSOKACI*
     Assalamu alaikum
Tallace-Tallace yakasance d'abi'unmu nayauda kullum wanda ake d'aurawa y'ay'anmu, yayyyunmu dakuma qannenmu,

Tallace-tallace bawai yakasance abu mafi muni bane Aa, Tallace-tallace wannan d'abi'une nayauda kullum wanda wasu daga cikinmu saidashi suke samu susanya abinci abakinsu, shine yake rufa masu asiri, shine kuma abun dogoro garesu, wannan tallace-tallace shine mutumci dakuma kimarsu, wannan tallace-tallace shine martabarsu, wannan tallace-tallace shine abunda yake rufa musu asiri sud'auke idanuwa daga roqon abun wasu, wannan tallace-tallace shine abunda yake hanasu kallon abun wani balle haryakaiga sunyisata, wannan tallace-tallace shine yake nuna dogoro dakai tafannoni dadama,
Amma kuma bahakan yana nufin cewa domin zamu d'aurawa y'ay'anmu kokuma y'anuwanmu tallace-tallace bawai yana nufin musakesu kamar tuhmakiba, bawai yana nufin musakesu kamar bamasonsuba, bahakan yaana nufin mubarsu kara zube bbu karatuba, wasu zaka kallii wannan tallace-tallace kawai suka sani, yaro zaifita talle tunda safe sai rana da rana yana dawowa zainufi tallan yamma, bbu arabi bbu boko,
Shinwai way'annan yarada Allah yabamu ba kiwo bane garemuba?"
Shinwai muna nufin Allah bazai tambayemu  akan kiowanda yabamu bane ranar alqiyama,
Kadafa mumunta duk wani abunda muke aikatawa yananan arubuce, Allah yana gani kuma zai tambayemu akai,
Meyasa idan yaranmu sund'auki talla sundawo bazamuyi qoqari wajan taimakawa rayuwarsuba?"
Kamata yayi yaro idanya dawo atalla saimu turashi makaranta, kokuma idan yadawo daga makaranta muturashi talla,
Wannan zamanin yazo mana dasauyi kala-kala, akwai makaranta ta safiya wacce yaro ko yarinya zasu iya zuwa da safe zuwa rana sundawo saisu d'auki talla sutafi, sannan sudawo sutafi zuwa makarantar islamiya,

Awannan zamanninne qatatuwar budurwa zata d'auki talla,
Sannan kuma zata dawoda kud'i fiyeda kud'in tallan amma kuma bbu bincike uwa zata sanya hannu taqarbe, ita duk tunaninta y'arta ta'iya talla."

Allah yasa mudace, Allah yabamu ikon kulada dakuma sanya idanuwa akan yaranmu."

******

  Yarinyace dabazatafi 13yrsba Tafe take tana d'an wake-wakenta kanta d'aukeda tire na talla, wani gida tashiga tana fad'in sallamadai ga tallan kayan miya, matar dake cikin gidan ne tace kawo, dasauri tashige tazube tiren tallan gaban matar,
Gabaki d'aya abunda yarage tallan baikai 50naira ba haka kuwa matar tasiyeshi tass,

   Tana fita dasauri-sauri tanufi gida tana shiga dasauri ta nufi band'aki domin dama ahannu take fitsari takeji, tundaga qofar band'aki bayan tafito da dukkan alamu ko tsarki batayiba domin bata shigada butaba, tundaga qofar band'akin take fad'in mama! mama!
Fitowa mama tayi tana fad'in haba suwaiba irin wannan kira haka?"
Hungo mama  ina gyadar take?" ynzu saina fita, tafad'i maganar tana sosai cinyarta wanda ta'alamu fitsarinda tayi bbu tsarkine ya addabeta,
Yawwaa  d'iyar Albarka mama tafad'i tana sanya hannu domin kar6an kud'in, irge kud'in tayi tace aikuwa suncika y'ar albarka, soke kud'in tayi saman zaninta tana fad'in barina shiga d'aki na d'auko miki gyadar kinga kafin kidawo nad'aura abinci ynzu wannan kud'inda kika kawo saina tura ayi cefene,
to mama niynzu bara natafi bangoma acikin kud'in, Aa suwaiba bbu wani gomanda zanbaki, idan kinyi ciniki kid'auka cikin kud'in,
Turo baki tayi ayayinda take d'aukan tirenda gyada amarau take ciki,
Kada kuma ki kuskura kid'auki fiyeda goma mama tafad'i,
Saiki hana suwaiba tafad'i alokacinda take tafiya,
Tana fita daga gidan tafara shiga wajan wajan tallanta,
Lunguda sako take shiga wajan tallanta, ba ita tadawo daga tallan gyadan nanba sai wajan la'asara data dawo abimci kawai taci sannan tayi bacci bbu zancen sallan azahar kokuma la'asar dabatayiba domin bata muwa sukayida yintaba,
 
Bata ita tatashiba saikusan magrib, dare kuwa yanayi tad'auki kunu tafice kasuwa dashi wajanda suke taruwa masu talla dayawa,

Bata dad'e datafiyaba baba yashigo zama yayi rashe-rashe yana fad'in mamar suwaiba ina tuwona?"
Tsaki taja cikin ranta wani haushi datakaicine yacikata mutum baya tsinana komai acikin gidansa saidai yaje yawo yadawo sannan yazo yanemi abinci kokad'an baisan cinta shanta dakuma suturarta koma yarantaba, saodai tanemi jari y'arta taje talla tadawo sannan susami abincinci shikuma yazo yawani zube yayi shame-shame yace" takawo masa abinci,
Tskai taqaraja akaro nabiyu sannan tad'auko tuwon acikin tire tatura masa gabansa tashige d'aki,
Shikuwa zama yayi yanarki tuwaonsa sannan yawanke hannu yaqara ficewa,

Saida dare yaraba sosai sannan suwaiba tadawo gidan lokacin tasamu mamanta da babanta gabaki d'aya sunyi bacci itama kwanciya tayi."

Washe gari dasafe

    Humaira! Humaira! Fitowa Wacce aka kirada humaira tayi, cikin nutsuwarta tana fad'in na'am umma,
Gashi nagama kidauka kikai zuwa jimawa kidawo domin zuwa makaranta koda baiqareba kidawo banaso kiyi latti amakaranta,
Toh umma tafad'i lokacinda take d'aukan qatoton tire mai d'aukeda shimkafa da wake dakuma maida yaji akai,
Sallama tayiwa mamanta cikin  nutsuwa take tafiya, adai-daita tatsara yakaita harzuwa tasha anan tazauna da kayan tallanta,
Cikin d'an qanqanin lokaci aka fara siya mata tallan domin nutsuwarta dakuma tsafta d'inta yasanya akeson siyan abun hannunta,
  Tana kallon shabiyu tayi dasauran tallanta wanda baiqareba tatattare takoma gida domin shirin tafiya makaranta,
Ba'ita tadawo daga makarantarba sai 4:00pm bayan tahutane umma take fad'in kinga kinyi latti makarantar islamiya garakiyi sauri ki shrya,
Bata dad'eba kuwa tataashi tanufi makaranta, tasami amfara tsaran latti
Gatada tsoron duka sosai haka dole tajira akayi mata dukan latti bbu ynada ta'iya tashiga cikin ajii,
Ba'ita tadawoba sai 6:00pm lokacin antashi amakaranta."

Bayan isha'i kusan qarfe takwas tana zaune cikin gida, wani yarone yayi sallama ta amsa wai humaira tananan?"abunda yafara tambaya kenan, eh tananan umma  amsa wacce take gefe tabada amsa,
Malm yahuzane yake sallama da'ita,
Jekace tana zuwa umma tafad'i, fita yaron yayi yafad'a masa abunda akace,

Bata 6ata lokaciba tafita, gaidashi tayi ya amsa yana fad'in dafatan bakiyi fushiba humaira, girgizakai tayi tana fad'in Aa kokad'an banyi fushiba aikinka kayifa, kuma laipy nane ninayi latti nasan dabanyiba bazaka ta6a niba, kuma idan baka yimun hukunciba hakan yana nufin bakayi adalciba,
Murmushi yayi gana qarason humaira kodan hankali irinnata, yarinyar tanada sanin yakamata,
Bata dad'eda fitaba yayi mata sallama ganin dare yayi sosai,
Sannan yasanarda ita cewa tasanarda umma akan iyayensa zasu shiga zancen,
Bayan takoma gida tasanarda umma, sosai umma tayi murna da wannan zancen domin dama burinta kenan ta aurarda humaira,
In sha gobe zantashi naje nasanarda qanin mahaifinki, umma tafad'a cikin murna,
Saisusan abunyi akai,
Dake dama ita humaira mahafinta yarasu itada mahaifiyarta take zaune su biyu, yayunta guda uku duka mazane sunyi aure, basa taimakawa mahaifiyarsu da komai,
Hakanne yasanya take qoqari wajan ganin ta kyauatata rayuwar yarinyarta, tallanda yarinyar takeyi shine rufin asirinsu, shine abunda yake taimakonsu, dashi sukeci sannan sukesha dakumashi suka dogara, shine yahana abun wani tsole musu idanuwa."

To be continued

Ur's zaynab bawa

KUNDIN HASKE💡Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum