Shafi na uku

1.6K 158 4
                                    

KUNDIN HASKE

AL-KALUMAN MARUBUTA...

NA KUNGIYAR...
     HASKE WRITERS ASSO

TARE DA AL-K'ALAMIN...

HAFSAT RANO

WAYAR MIJI

Babi na takwas

Shafi na uku

Khairat ce ta kasa hakuri sai ta da magantu

"Bangane ba fa ya Hajja, wai dama wayar daddyn ihsan ce ko kuwa dai taki ce?"
Dariya yaya Hajja tayi kadan sannan ta kalli ihsan tace.
"Dota jeki wajen Daddy ki zanyi magana dasu Anty Na'ima."
Da d'an gudun ta fice sannan ya hajjan ta maida kallonta wajen su Khairat.

"Kunyi mamakin ganin wayar Uncle a wajena ko? Duk ba wani abu bane illa sawa rai salama. Kun ganni nan, babu ruwana da binciken wayarsa, ko da xata kai daka yau zuwa sati d'aya a wajena bazan taba ketare abinda na karba don yinta ba. Ba wai don ina da karfin zuciya da jarumtar ba, sai don gujewa tashin hankali da dana sani. Musulunci ya hane mu da bincike, da shiga abinda babu ruwanmu. Sau da dama nakan ji zuciyata tana rayan na shiga mana nayi dube-dube, amma sai na yak'e ta na danne ina tuno kar nazo nayi abinda zanxo ina wayyo Allah."

Shiru sukayi gaba daya kowa da abinda yake sak'awa.

"Amma kuma me yasa su mazan suke abinda zai sa mutum yaji son dubawa musu wayar, misali sai kiga namiji yana ta kaffa-kaffa da wayarsa, kai kuma sai kaji kana son dubawa."
Khairat ta tambaya

"Tabbas da wannan don wannan, amma sai ka basar ka cire wa ranka. Kayi rayuwar ka ba tare da ka sawa kanka son ganin me suke aikatawa ba. Shi namiji baka isa ka sashi yayi ko yak'i yi ba, daga lokacin da kake takura masa, daka lokacin yake jin k'aimin sake aikata abinda yayi niyya."

"Haka ne." Na'ima ta furta a hankali zuciyarta na nuk'urkusar ta. Sirrinsu ne tsakanin ta da Idris bazata iya kwance masa zani ba. Sai ta ja baya ta jingina tana ci gaba da jin ya Hajja tana yiwa Khairat fad'a akan abinda ta aikata wa Jabir. Kamar taji fad'an har da kukanta na nuna nadama.

Shinkafa da wake ya Hajja ta kawo musu bayan ta sallami Uncle ta dawo suka shiga ci. Khairat hannu baka hannu k'warya, saboda tun lokacin da abin ya faru, bata samun isasshen abinci da k'wanciyar hankali balle uwa uba barci wanda ya zama abokin buyanta.

Na'ima kuwa kawai tsakura take amma bata da walwala sam. Ya Hajja na lura da ita, amma ganin bata ce komai ba kamar yadda Khairat ta sanar mata matsalarta, sai kawai ta kyale ta ba tare da ta tambaye ta ba.

Sai bayan la'asar sannan Khairat ta fad'a wa Ya Hajja, bada izinin Jabir ma ta taho ba, fad'a sosai ya Hajja ta shiga yi mata, ta umarce ta dauki hanya ta koma d'akin mijinta don nan ne rufin asirinta. Bata so ba haka ta fito, duk iya kar fad'an da ya Hajjan tayi mata be sa taji zuciyarta ta russuna ba, bacin ran Bilkisu da cin amanar da take ganin anyi mata, ba zai sa tayi saurin saukowa ba. Ko da ta shiga d'an sahu sai ta shiga lissafin yadda zatayi ta raba Jabir da Bilkisu. Da haka har ta isa gida bata samo mafita ba. Lokacin da ta isa bata tarar da Jabir ba, sauke mashkoor tayi ta shiga kitchen(d'akin girki) ta dora ruwan taliya. Sai ta dawo falon da mik'e kafarta kan kujera ta fad'a tunani, dama Mashkoor tun a hanya yayi barci.

Bayan ta gama girki ta zuba a flask wanda saboda tsabar bata cikin nutsuwarta, taliyar sai ta da dafe. Ko a jikinta ta ajiye masa tayi shigewar ta d'aki shi ma saboda ya Hajja tace lallai tayi girki in ta koma shiyasa ma tayi, gani take ai babu wani sauran abinda zata iya yi masa tun da shi maci amana ne.

Tana k'wance cikin net data d'aura shi tun magriba ta shige ciki saboda d'an banzan sauro tayi kasak'e tana jiran dawowar Jabir.

Tun tana sauraron dawowar sa har ta fara k'wallar bakin ciki. Tuni zuciyarta ta fara aiyana mata munanan abubuwa akan Jabir, zargin sa take sosai har ba ta jin sauran soyayyar sa a zuciyarta. Shaid'an ya sami abun yi, ai sai ya shiga hasaso mata Jabir na tare da Bilkisu. Take taji kwanciyar ta gagare ta, ba shiri ta mik'e ta fito daka net d'in kamar kurkuku😅 ta shiga zagaye d'akin zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito.

"In kasan wata baka san wata ba wlhi." Ta furta kamar zararriya. Sai ta fito harabar gidan da sauri ta saka sakata ta ciki da rufe kofar wanda dole in dai har ya dawo bazai iya budewa da mukulli ba. Murmushin mugunta tayi ta dawo cikin net ta kwanta tana sauraron sa.

Sai wajajen sha d'aya taji yana ta kokarin sa key.

***
Tafiyar Khairat ya bawa Ya hajja damar kad'aicewa da Na'ima. Sai kawai ta sa mata kuka, bata ce mata ta tafar balle sauke ba, har sai da tayi me isar ta. Ganin tayi shiru tana ajiyar zuciya yasa Ya Hajjan dawowa kujerar kusa da ita ta dafa ta.

"Dukkan tsanani yana tare da sauki Na'ima. Kuma duk macen da kika gani a gidan aurenta toh baza'a rasa ta da wata yar matsala ba. Hakuri da juriya shine yake zaunar da mutum. Bana son jin dalilin hawayenki, ki cigaba da hakuri sannan ki zama me rik'e sirrinki dana mijinki." Sai ta hau kad'a kanta a hankali kafin tace

"Nagode sosai da shawarar nan Ya Hajja, na yarda da hakurin nan da ake jaddada maka tun kana gida, ashe haka dama hakurin yake?"

"Da wahala da ciwo, sai ka daure." Ya hajjan ta k'arasa mata.

"Tabbas akwai wahala, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu."

"Ameen." Ta amsa suka shiga kitchen don d'ora abincin dare.

Sai bayan sallar isha sannan Idris ya dawo bayan ya tsaya a masallacin Usman bn Affan dake gadon k'aya in da ake karatu duk ranar jumma'a bayan sallar magrib zuwa Isha.

Yana d'aya daka cikin ak'idun Idris da yake k'ara narkar da Na'ima cikin kaunar sa da yarda dashi ada. Baya taba fashin halartar karatun duk satin duniya sai dai in da wani uzuri k'wakk'wara.

Har ciki Uncle yayi masa iso, sai suka zauna suka dasa sabuwar hirar siyasa tare da cin abinci. Kalle-kalle ya dinga yi yana neman ta ina zai hango Na'imar tasa, Ya Hajja na lura da shi lokacin data shigo da tray dauke da kayan abincin. A ranta ta k'ara gaskata lallai akwai yar matsala ta da had'o su,amma babu komai zata taya su da addu'a tun da dama shi zaman tare zo mu xauna zo mu sab'a ne.

Sai wajen tara sannan sukayi musu sallama suka tafi.

A hanya yana ta kokarin yaga ta saki jikinta, ba laifi tana d'an ta daurewa tana amsa masa cikin sakin fuska sai dai k'arancin walwala.  Komai jinsa take sabo, sai take ji da ganin kamar duk wani abu da zatayi bazata taba burge shi ba, tun da har yasan ya kula su linda wanda su ba kunya ce dasu ba. Wannan tunanin yakan saggar mata da guiwa yabi ya take duk wani farinciki da karsashi da take dashi.

Har suka iso gida be k'ara gane kanta ba, duk kokarin son taga ta danne amma ta kasa, labarin zuciya hausawa kan ce a tambayi fuska. Sam fuskarta babu walwala sai wadda ta aro ta yafa wanda sam bata samu zama a kan fuskarta ta ba.

"Bby sauko kici abinci." Ya katse mata tunanin yana bud'e ledar hannunsa.
Sai ta zamo k'asa a hankali ta xauna ba tare da ta furta komai ba.

"Ya Allah." Shine abinda taji ya furta a hankali yana kallonta. Sai ta saki murmushin yak'e ta dau ledar ta juye abincin akan plate d'in daya d'auko. Sai kawai ya bita da ido ta shiga ci a nutse tana d'an basarwa. Abincin ya mata dadi sosai dama ga yunwa dake nukurkusarta. Dama ita chan ba me yawan cin abinci bace, amma kuma faruwar al'amarin nan ya sa ta k'ara rage kaso 70 cikin 100 na cin nata. Cike da tausaya wa yake kallon yadda take cin abincin, shine ummul aba'isin komai, sam be kyauta musu ba daka ita har shi, babban ciwo shine ka yarda da mutum d'ari bisa d'ari sai kuma yazo yayi abinda zai fatattaki wannan yarda ba tare da ya bar ko da kankani ne ba. Har ta gama ta kwashe kayan ta shirya cikin shigar bacci yana girke a inda ta barshi rik'e da karamar wayarsa da ya sawa earpiece yana sauraron shirin siyasa saboda gabatowar zab'e.

"Zan k'wanta... Sai da safe." Ta furta muryarta na d'an rawa tare da shigewa d'aki harda d'an saurinta. Wani irin abu ne ya dakin masa zuciya. Yau Na'ima ce take masa abubuwa kamar ranar suka fara sanin juna. Duk soyayyar da suka gina tsawon lokacin da suka dauka tare na neman guduwa, a da babu yadda za'ai daya ya tafi ya k'wanta ba tare da d'aya ba, sai gashi yau Na'ima na fito mishi da salon horon da zai yi masa wuya ainun. Da azama ya kashe wayar ya jona ta jikin socket yabi bayanta da sauri.

*Rano*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now