Shafi na biyu

2.3K 243 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)


*MUTUNCIN MACE............*

*TARE DA ALQALAMIN*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

        0⃣2⃣

      Cikin qanqanin lokaci aka kammala farfesun kifin kowacce ta dibi rabonta bisa jagorancin daya daga cikin matan wato lariya,wadda take kaman itake bada order da control na dukkan macen dake kai kawo a gidan,nan suka baje kowacce na kaiwa baka hira ta sake daukan sabon salo.

     Duk da yadda wasu daga cikin matan ficewa zuwa gidansu da d'ai da d'ai da d'ai d'ai hakan bai ankarar da badariyya ba har sai misalin biyar da rabi na yammaci sannan ta farga,cikin hanzari ta miqe taba saba yarinyarta a baya,sai a sannan ta tuna da ko abinci bata girkawa abban khairat ba,gwara yaranta sunci a nan gidan lariyar,sauqinta d'aya ma tasan auwal ya gyara mata gidan dakin maigidan da abinci kawai zata dora,sallama ta yiwa sauran matan da sukayi shigowar yamma cikin gaggawa ta fice.

       Saidai me?,Kaca kaca ta tadda tsakar gida zuwa kitchen din,wanda tuni auwalu ya gama abinda zaiyi ya fice ya bar yaran,wanda hakan ya basu daman shan shagalinsu abinsu,kayan wasansu ko ina kaca kaca,sam ta mance ma da yau suna da islamiyya bare tayi tunanin turasu,hannu ta sanya ta dafe kanta tana dubansu tamkar zata saki kuka,sannan ta sauke hannun ta qaraso cikin hargagi ta soma qunduma musu zagi cikin bacin rai,sai data gama zaginta mai isarta sannan ta soma tattare tsakar gidan da kitchen din wanda hakan ya dauketa a qalla mintuna talatin duk da cewa ba wani fita fes yayi ba,sai shida da rabi sannan ta tsaya a kitchen din da niyyar dora girki,ta tuna ashe gas din nata na gidan lariya,cikin hanzari ta figi mayafinta tana salati ganin duka duka mintuna goma zuwa a shirin suka rage kiran sallar magariba dama dawowar abban khairat baki daya.

      A hanzarce ta dora dafa dukan taliya saboda rashin isashshen lokaci dama gas din data fuskanci ya kusa qarewa,da sauri ta janyo zobon data jiqa shigowarta ta zuba masa tiara ta tace ta saka a jug sannan ta nufi fridge da shi,sai data bude fridge dinma sannan ta tuna mitre din gidan a kashe take kasancewar bata wuni a gidan ba,sam babu wani sanyi a fridge din haka ta cusa jug din ta koma kitchen.

       Qarar horn da bude garejin gidan ya sanyata rugawa zuwa dakin girkin ta sauke ruwan dafa dukar ta dora ruwan zafin da zai sha shayi,ganyan shayi kawai ta jefa a ruwan saboda sauran citta da kanunfarin nata da ita suka dafa kifin dazu,hanjin cikinta ya kada sanda taji baban nasu na tambayarsu
"A'ah....husna...ya haka?....ke khairat ban hanaku fita wasan qasa ba?,ko a qasa kuke zama a islamiyyar?,dubi jikinki kaman wadda baki wanka ba"
"Laaaa Allah abba munyi waka,auwalu ne ma yayi mana", cak ya tsaya da abinda yake yi yana duban yarinyar,wani zallar bacin rai na shigarsa,baisan sau nawa ba zai maimaitawa badariyya ba,baisan sau nawa takeso ya gaya mata ba,don me zata dinga sanya almajirinta namiji yaron da ya kusa shekara sha biyar yana kama yaransa mata yana musu wanka?,hannun khairat kawai ya kama husna na riqe a hannunsa suka bulla tsakar gidan ta wata qaramar qofa.

      Kallo d'aya tayi masa ta karanci zallar bacin rai daga fuskarsa,sai ta kasa samun qwarin gwiwar yi masa sannu da zuwa ta bige da duba ruwan zafin dake kan gask,yayin da shi kuma ya isa ga qaramar diyarshi dake rarrafe zuwa wajensa ganin shigowarsa tana bangale masa baki,sauke husna yayi ya isa gareta ya dagata yana dan cilla ta sama tana sakin dariya,yana matuqar son yaransa saboda yasan bashi da wani abu mafi kusanci da zuciya da gangar jikinsa irinsu,sai a sannan ta samu qarfin halin yi masa sannu da zuwa,ya amsa ciki ciki wanda ba don ta kasa kunne ba mawuyaci ne taji amsawar tasa,sauke meenal yayi sanda yaji an soma kiran sallah,ya jawo ledar daya shigo da ita ya fiddo lemon zaqi ayaba da kankanar daya shigo da su ya mimmiqa musu sannan yayi addu'ar buda baki ya soma sha shima,addu'a take Allah yasa kafin ya gama sha ya daura alwala ruwan zafin ya juya ta miqa masa,don tasan qa'idarsa tea yake fara sha sannan yayi alwalar ya fice,saidai har ya kammala alwalarsa ruwai bai juya ba.

     A gaggauce ta dure ruwan cikin flask din ba tare daya kammala tafasa ba kaman yadda yake so,ta kai falon ta ta ajjiye hade da cup  da sauran kayan tean,sannan ta koma a gurguje ta maida ruwan dafa dukan,sanda  ya dawo daga sallar da ruwan shayinsa ya shigo,haka ya ja cup ya juye abinsa ciki ya dauki bread din dake aje gefe ya hada da shi ba tare da yace mata kanzil ba,sai kai kawo kawai take tana satar kallonshi,shirunsa ko rashin shan naga shayin bai dameta wani can ba,fatanta d'aya shine kada yayi mata fad'a,buqatarta ta biya kuwa,don har ya gama ya sake ficewa sallar isha'i bai tanka mata ba,bai sake shigowa ba har ta samu ta gama dafa dukan taliyar ta shiga bayi tayi wankan da tun safe bata samu yi ba,sam ta mance ma cewa kayan jiya ne a jikinta.

      Yana zaune ta gabatar masa da abincin yayin da yake binta da kallo cikin takaici,ko wani bai gaya masa ba yasan cewa ta sake komawa 'yar gidan jiya,yawon gidan maqwabta,ya rasa uban me take samowa a can din?,wanne d'ad'i yawon yake mata,bayan bai rage ta da komai ba,dukkan wani haqqi da Allah ya dora kanshi nata dana yaranshi ya sauke mata,zai iya dukan qirji ya kuma yi alfaharin kaf layin babu wanda gidansa ke da rufin asirin da shi yake da shi,ya maida idanunsa kan khairat da husna da qaramar qanwarsu islam dake yashe gefe bacci ya d'aukesu cikin rashin gyara,zuciyarsa ta sake quntata,ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake,cikin kaffa kaffa tace da shi
"Abban khairat bismillah" abincin yabi da kallo cikin takaici,ta riga data sani cewa babu abincin da yaqi jini irin dafa duka,dafa dukan ma ta taliya,ko a sanda yake saurayi yakan haqura da abinci indai dafa dukan taliya ce bare yanzu da yake da 'yancin cin gashin kansa
"Ina kifin?" Ya tambayeta kai tsaye.
"Wanne kifi kuma?" Ta tambayeshi tana dubanshi,kasancewar har ga Allah ta mance yace mata farfesun kifin yakeso yaci kafin ya fita
"Kifin dana ce a dafamin kafin na fita" ya tunasar da ita ranshi na suya,sau ta hau kame kame
"Kifin?.....kifin na soya,na barshi a kitchen khairat da husna suka cinye".ranshi ya kai maqura wajen 6aci,ya tabbatar da cewa qarya ce kawai take shirya masa,kifin yafi qarfin cikin khairat husna dama mamarsu
"wato duk abinda zan gaya miki badariyya ba zaki ji ba kenan?,mutumin banza kika d'aukeni ko kuma wanda baisan ciwon kansa ba?",zuciyarta ta soma raurawa taso karyewa,sai kuma ta samu qwarin gwiwa tashin farko data tuna kalaman rakiya na yau
"baka taba nunawa namiji ka gano laifinka koda kaike da laifi,idan ba haka ba zaita amfani da wannan raunin naka ne yana mulkarka yadda yaga dama,gaba koda kece keda gaskiya baki da bakin magana,ki tsaya kawai kuyi fito na fito,to koda ace kece da laifi zaiji shakkar tararki a gaba". Tuna wannan yasa ta qanqance idanu tana dubanshi
"me kuma akayi?"
"Ke zan tambaya,jiya jiya na miki iyaka da  shiga maqota barkatai,bama ni ba hatta malam wannan karon ya shiga maganar amma ya tashi a banza kenan?....."
"Kaga abban khairat dakata don Allah,haka kuma zaka koma mai zargi?,ina akace maka naje?,kazo gida baka sameni bane ballantana kace na fita?,ko zaka iya rantsewa da Allah kan cewa na fita?" Cikin wani matsanancin bacin rai ganin tana neman maidashi wani sauna yace da ita cikin kausasa murya
"Yimin shiru badariyya tun kafin na qarasa tunzura,shin ni din qaramin yaro ne?,ko mahaukaci ne ni,koko makaho da bani da ido?"
"To wallahi saidai idan hasashenka ne bai gaya maka gaskiya ba amma ni cikin gida na wuni ehe" ta fada tana gyara zamanta sosai kan kujera tare da juya masa baya,duk da tana d'ari d'ari amma ta dake zuciyarta hudubar rakiya na mata amsa kuwwa shed'an na kada mata gangarsa.

*mrs muhammad ce*👑

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now