Shafi na uku

1.7K 168 4
                                    

*KUNDIN HASKE:-*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

*K'UNGIYAR*:-
   *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
*Zaynab bawa (zeeyybawa)*
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA UKU*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Gidansu humaira*

Zaune humaira take kamar kullum bayan tagama aikace aikacenta nagida, ranar takasance bbu islamiya,  tafita talla kuma harta dawo,

Sallama yaro yayi ta amsa tana kallon yaron,

Wai humaira tazo,

Inji waye?"
Humaira tatambaya tana kallon yaron,

Inji mlm yahuza yabata amsa, har dabur bur cewa takeyi wajan bada amsa tace" kace masa inazuwa,

Dasauri tatashi tashiga d'aki tana fad'in umma kinji mlm yahuza ne yake kira a waje,

Murmushi umma tayi sannan tace" toh kisanya hijabinki saiki fita,

Hiijab ta d'auka ta sanya ajikinta tafito tsab,

A bakin babur d'insa taganshi tsaye, sanyeda jamfa, wanda tazamo al'adarsa a kullum takarasa cikin takunta na nutsuwa, gaidashi tayi shima ya amsa cikin fuska mai cike da damuwa,

Ganinta da yanayin nutsuwarta yaqara tayar masada mikin sonta,
Gani yakeyi kamar yayi babbar asara wanda zaiyi wuya ya maida kamarta,

Wata nauyayyar ajiyar zuciya yasauke kallonta yayi kanta yana qasa kamar kullum sai wasa takeyi da yatsun hannunta, shikuwa mlm yahuza yatsura mata idanuwa yakasa furta koda kalma d'aya,

Itakuwa ta qagu taji ko kalma daga bakinsa tanaso tasan mai yake faruwa, amma yayi shiru baice komaiba,

Shirunda yayi baqaramin sanyata cikin tashin hankali zullumi dakuma tuanani yayiba,

  Ganin idan zasu shekara a haka humaira bazata furta kalma ba bayan gaisuwa yasanya ahankali yakira sunanta Aisha!

D'agowa tayi dasauri tadubeshi jin ya ambaci ainihin sunanta duk da kasancewar sunan mahaifiyarsa ne,

  Aisha inaso nafad'a miki wata magana amma narasa tayaya zanfara fad'a miki ita, wannan magana itace dalilin dayasa nakasa zuwa wajanki tsawon kwanaki, domin bansan tayaya zaki d'auki maganarba,

A zaharin gaskiya maganar tanada nauyi sosai, zatayi wuyar fahimta a ma'auni, inaso kitsaya kiyi amfanida hankali uwa uba ilimi dakuma imaninki wajan fahimtar  wannan magana,

Sannan kiyi imani da qaddara domin ita qaddara dole takasance mutum yayi imani da ita koda mai kyauce kokuma akasin haka,

Jikin humaira yagama yin sanyi, kalamansa sungama kashe mata jiki, ynzu tafara fahimtar yanda kalamansa suka dosa dole akwai matsalane babba,

  Aisha yasake kiran sunanta, wannan karon takasa d'agowa domin bbu wani sauran dauriya tattareda ita,

  Aisha inaso kisani inasonki, idan kikaga na rabu dake bason raina bane,

Kaddarace daga wajan ubangiji,

Humaira tunda taji ya ambaci kalmar rabuwa tace shikenan anzo wajan,

Humaira ina ganin alaqata dake daga yau taqare bbu saura, amma ina baqin cikin rasa kamilar mace irinki,

Nagode kawai tafad'i had'eda juyawa tanufi gida batareda taqara cewa komaiba,

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now