Shafi na biyu

1.8K 196 12
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-KALUMAN MARUBUTA...*

*NA KUNGIYAR...*
     _HASKE WRITERS ASSO_

*TARE DA AL-K'ALAMIN...*

*HAFSAT RANO*

*WAYAR MIJI*

*BABI NA TAK'WAS*

        *Shafi na biyu*

☆☆
*B*abu irin lallashin da Idris beyi mata ba akan ta fad'a masa taka mai-mai me yake faruwa, duk yabi ya dami kansa, yanayin da yake ganinta kad'ai shine yake d'aga masa hankali, gashi duk wani hakkinsa na aure tana kokarin taga ta sauke masa.
  Kofar d'akin ya tura bakinsa d'auke da sallama, yau ko za'a hau sama a fad'o sai ta sanar masa komai. Kwance take fuskarta rufe da littafin hisnul muslim wanda daka gani kasan azkar ta gama. 'Dan janye littafin tayi kad'an gami da amsa sallamar tasa, sannan ta maida kanta yadda yake da.
"Na'ima." Ya kira sunanta kai tsaye.
"Na'am." Ta amsa a hankali.
"Inason ki tashi zaune muyi magana a matsayi na na mijinki." Ba musu ta tashi gami da zuro kafafunta kasa. Numfasawa yayi sannan yace;
"A matsayi na na mijinki, idan har na isa dake, inason ki sanar dani me yake faruwa don Allah." Kasa ta k'arayi da kanta don ba karamin nauyi had'a ido dashi yake mata ba tun sanda abin ya faru.
"Ina jinki, wannan shirun naki yana kashe ni, kice wani abu, in ma duka na zakiyi gwanda ki dakeni, ko ki zageni, amma banda shirun nan naki. Masifa ne a tattare dani." Cikin nutsuwa ta soma magana muryarta na d'an rawa;
"Inason na fara da baka hak'uri bisa ga binciken da nayi maka, wanda ko a musulunci bincike haramun ne, ina rok'on daka yafe min. Son sanin dalilin kaffa-kaffa da wayarka ne ya jawo har shed'an ya ingizani."
"Na yafe miki Na'ima." Ya fad'a a gagauce, tabbas tunaninsa ya zama gaskiya, Hirar banza da yake da Linda Na'ima ta gani. A take kunya ta kamashi gami da tsantsar fargaba da tsoron hukuncin da zata yanke masa
"Nagode."
"Abu na biyu; inason kaji tsoron Allah, ka sani tabbas zina tana da reshe da yawa, akwai hadisa da yake magana akan kusantar zina,  (kada ku kusanci zina) anan basai mutum ya d'auki kafarsa yaje ya aikata zina shine yayi zina ba, a'a, abubuwan da suke faruwa a wannan zamanin duk zina za'a kirasu dasu. Kallon hotunan batsa, maganganun batsa, da sauransu. Ka sani bakayi wa Na'ima laifi ba, in ma kayi mun be wuce na banzatar da martabata a matsayina na matarka. Saboda haka ina baka shawarar ka gaggauta tuba ka nemi yafiyar ubangiji." Tun data fara maganganun nan Idris ya fara hawaye. Hawaye ne masu tattare da nadama da tausayin Na'ima, lallai samun mace kamar ta a zamanin nan sai an tona. Shi kuwa wanne irin rashin tunani ne ya kaishi ga aikata irin wannan mummunan aikin, tabbas yasan akwai mutane da yawa da zasu karyata hakan in aka ce musu yayi, duk sharrin wannan kafafen sadarwar ne ya kaishi ya baro shi. Daidai kafafunta ya durkusa ya rik'e hannayenta.
"Tabbas ni cikakken butulu ne Na'ima, baki dace da irina ba sam, na cutar dake, na hanaki barci, na saki zubar hawayenki masu tsada. Amma duk da haka baki nemi rabuwa dani ba, duk wani hak'k'ina kin sauke, ni kuwa da wanna irin ido zan kalleki?." Zamawo tayi kasa tana Kuka
"Ka tashi ni dai, banaso." Ta fad'a tana jan hannunsa. K'in tashi yayi sai ma rik'e ta gam da yayi ya cigaba da kuka.
"Ki yafe mun don Allah, wallahi sharrin shaid'an ne. Nayi miki alk'awarin bazan sake ba."
Kasa magana tayi sai kuka kawai, sun d'au wajen awa guda a wajen yana nuna mata tsantsar nadamarsa, ba laifi ta fuskance shi sosae kuma tayi masa uzuri. Anan ta d'au aniyar dunga tunasar dashi lokaci zuwa lokaci.

☆☆
Bangaren Khairat kuwa, Jabir na fita tabi bayansa da sauri har tana tuntu'be. A zaune ta sameshi yana kok'arin d'aukar remote. Da sauri ta rigashi kai hannu tana karkad'a jiki.
"Don ka maidani banza shine muna magana zaka wani zo ka kunna tv(talabijin) ko? Aikuwa wallahi baka isa ba, sai ka amsa min tambaya ta."
"A wane dalilin kake chatting da Bilkisu, har kana mata maganar aure, ehe?" Kin amsa mata yayi, masifa ta shiga yi tana yarfe hannu, sai data yi me isarta yana kallonta kunnensa sak'ale da earpiece yana jujjuya kai.
"Kin gama?" Ya tambaya a gadarance.
"Oho." Ta bashi amsa tana yatsine.
"Toh ga amsarki; "Bilkisu kawarki aminiyarki tun yarinta, ita zan aura, ko kina so ko ba kyaso, in kinga dama ki mutu." Yana kaiwa na ya fice had'e da bugo mata kofa. Ihu ta fashe dashi ta shiga surfo masa ashar tana kuka wiwi.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now