10

1.8K 138 8
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 10
last page.


Kabir tsaki yayi yazauna daga gefen kofa yana tunanin yadda zasu kwana gidan bakomai sai kayan sawarsu, ganin babu mafita ya saka shi cema wasila ta fito da turmin atamfa daya daga cikin lefen khadija da basu  dauka ba, su shimfida zuwa safe ya siyo katifa, FIta yayi ya siyo musu abinda zasuci ya dawo bayan sunci suka kwanta.
Washe gari ya shirya ya fita aiki ita kuma yakaita gida da niyyar inya dawo zai dawo tare da ita sai su siyo katifa daga can da karamin gado.

Baisha mamaki ba sai da yaje shagonsu ya samu sababbin ma'aikata a ciki, kuma aka fada masa Alhaji yace ya bada makullin shago, haushi yaji yace "to sai me? Akan wani shagon banza" yajuya yakoma gida ya samu har wutar gidan an sauketa an kuma saka babbar padlock an kulle gidan haushi ya sake kamashi ya juya gidan abokinsa yana kiran wasila awaya ya labarta mata abinda Abba ya masa budar bakinta sai cewa tayi "dama kai matsiyaci kuma makaryacine? Ai kacemin gida da komai naka ne sai gashi nan Abba ya koreka daga gidan saboda kaci amanar yar mutane, to ka sani sai in ka samu wajen zama sannan ka neme ni" tsaki tayi bayan ta kashe wayar tana cewa "kamaci Sa'a ina sonka da sai dai kabani takardar saki".

Juwairiyya ta kira malam ta fada masa abinda ya faru, sai gashi basu dade da yin waya ba yazo gidan, lokacin khadija tana kwance kan kujera su Aisha sun tafi makaranta daga ita sai juwairiyya da Saifullahi.

Tunda ya shigo kallo daya tayi masa ta kauda kanta sannan ta rufe idonta, duk zaman da yayi har ya tafi bata juyoba sai hawaye da suke zuba daga idonta.

Murmushi yayi ya riko hannunta yana cewa " mai kuka kullamin tsakanina da jikata? Tunda na shigo bata kalleni ba, khadija" ya kira sunan ta a hankali, bata amsa ba saima sheshshekar kukanta daya fito, girgiza kai yayi yana cewa "khadija nine ko? Na cire hannuna a lamarinki? Kiyi hakuri naji zafin abinda kika yi shiyasa amma kiyi hakuri kinji malam bazai sake yiwa amaryarshi haka ba" ya kalli saifullahi yace "idan khadija taji sauki akai min ita har gida".

Rakoshi sukayi har waje sannan suka koma.

Fafutukar Neman gidan da zasu zauna kabir yayi a wunin ranar shida abokinsa Dan bayajin zai iya kwana daya babu mace ma balle ya dau lokaci mai tsawo. Dakyar suka samu gida mai daki daya da palo sai kitchen da toilet, gidaje sunyi tsada yanzu bashida wannan kudin.

"Kai ka matsa sai anyi auren kace ko cokali kar nazo dashi se yanzu iyayena sun gama sakin jiki zaka wani ce nazoda kayan kitchen. To kasani mu bamuda komai bamu shirya ba idan ka tanadi komai sai kazo mu koma" kasa bata amsa yayi kawai ya shiga kasuwa ya siyo kayan aiki kadan ya kawo gidan da katifa madaidaiciya, sai dare yaje dauko wasila yanajin gajiya sosai.

Tunda ya daukota yaga tana faman yatsina yadai share saboda yaji jiki, yayi alkawari aransa bazai bawa baba hakuri ba.

Juwairiyya taci gaba da kula da khadija sosai, a take ta dawo yadda take da ta murmure tayi kiba sosai.

Suna zaune a daki itada juwairiyya tace "ummee kinga na fara period ba pad, ko zan leka waje na bawa almajiri ya siyo min" gyada mata kai ummin tayi tace "amma idan baki samu ba bance kije da kanki ba" ta amsa da to sannan ta Fita bayan ta dauki kudi da hijabi.

A jikin kofar gate din ta tsaya jiran yaron ya dawo sai kawai taga mota a gaban ta tayi parking, gabanta ya fadi sosai ganin Abdullahi tayi saurin yin kasa dakai, se kuma ta shige gida, bai damu ba yabi bayanta bayan sun gaisa da mai gadi har ta kusa shigewa yakira sunanta, tsayawa kawai tayi bata juyoba ya matso kusa da ita yace "Dan Allah ki tsaya muyi magana, ni wurin Abbu ma nazo amma nasan baya nan kawai na kasa hakuri ne" a hankali ta juyo tana goge hawayen daya zubo mata tace "kashigo to" murmushi yayi ya bi bayanta sai da suka gaisa da juwairiyya sannan ya soma magana a gaban ta ma yana cewa "Ummi Ashe abinda ya faru kenan, Allah ya kiyaye gaba, sai jiya nakejin labarin mutuwar auren shine na kasa hakuri nazo" dariya kadan tayi sannan tace "babu komai ai Abdullahi komai ma yazo da sauki Allah ma ya taimake mu auren ya mutu ta sauki" daga nan suka Dan taba hira sannan ta basu wuri shida khadija, addua kawai yayi mata sannan yace da dare zai dawo.

Tunda saifullahi yaji Abdullahi ya dawo yaji dadi, da dare yana zuwa sukayi magana babu Wanda yasan abinda suka shirya sai su kadai.

Kayan dakinta ya saka a kasuwa ya siyar dasu ya siya sababbi ya ajiye a gidan malam.

Sai da aka sa date sannan Abba ya kira Khadija ko tana son Abdullahi, kanta a kasa ta kasa bashi amsa ganin tana murmushi yace taje kawai.

Tasha mamakin jin an saka date a sati biyu masu zuwa, a take aka soma gyaran amarya anty asabe batayi kasa a gwiwa ba kullum tana hanyar gidan har ranar da aka daura aure, walima sukayi da rana sannan washe gari asabar za a kaita.

Suna zaune Abdullahi yayo aika yace ta fito yana waje, koda taje yace "ki hada abubuwanki masu muhimmanci gobe da sha biyu jirmin zai tashi zuwa Sudan", kallonshi tayi da mamaki amma ta kasa magana sai daga baya tace " Abbu ya sani"? Yace "harda Ummi ma" yana gama fadin haka ya janyota jikinsa, duk da gabanta ya fadi amma ta kasa hanashi, sai da ya sake ta sannan ta bude motar da sauri ta fita.

Yan biki sun Cika gida ana labarin masu zuwa kai amarya sai ji sukayi ana cewa ai amarya ango yazo ya dauketa sun wuce Sudan.

Wata goggonsu tace " amma wannan angon Dan yine shine ko sallama bai bari nayi da jikar tawa ba" sukayi dariya.

Abdullahi sai rawar jiki yake bayan sun sauka shi ango, sai duk jikinta yayi sanyi, tana ganin kamar ma ta cuceshi, kwana tayi kuka aranar tana bashi hakuri shikuma duk duniya babu abinda ya tsana irin zancen, sai da ya share sati daya bai je makaranta ba sannan ya koma, waya ya siya mata saboda ta Dan rage mata kewa kafin ya Samar mata makaranta.

"Kam bala'i! Yarinyar nan aure tayi? Mtsw amma wallahi gayen nan ya yanke ni, mutum ma kwanciyar hankali ya gagareshi waccen banzar bata bari azauna lafiya".

" wace shegiyar kake Kallo" yaji wasila ta fada ya juyo ya kalleta yace "wacce ta Fiki amfani ce, ni wallahi se yanzu nayi Dana sanin sakin matata, yarinya mai hakuri na yaudareta naci amanarta yanzu gashi kinzamar min jaraba, duk zugar kice kuma munafuka mai kashin tsiya, aurenta babu abinda ban samu ba na alkhairi amma ina rabuwa da ita komai ya lalace sanadinki"

Seda ta kwada mai harara sannan tace "Kaine dai matsiyaci kuma abinda ka shuka shi kake girba ni na gaji da wannan mugun talaucin kuma khadija se kaje ka aurota ka dawo da ita tunda itace arzikin ka" tana gama fadin haka  sannan ta kwashi kayanta ta fita daga gidan.

Shi kansa yasan sunci kwakwa duk sun komade shida wasila, yanzu data tafi ta barshi ya kara gano yana cikin hadari dole ya tarkata yatafi inda baba yana kuka yana bashi hakuri ya gane kuskurenshi.

Baba ya kalleshi yace "tashi ka tafi Allah yasa ka shiryu da gasken, ka kuma sani kanada kanne mata zakuma ka haifi mata idan Allah ya yadda, ka daina zaluntar yayan mutane, bayan haka kuma ga Zainab can mijin ya korota wai baya son haihuwa ya zubar mata da ciki sau biyu na ukun taki yadda ko shima ya isa ya zama darasi a wurinka ka kuma je ka bawa malam saifullahi hakuri domin ka cucesu"

Gyada Kansa yayi yana hango girman kuskuren daya aikata.


Khadija saida suka yi wata bakwai sannan suka samu Hutu, ya daukota suka zo ganin gida, cikin jikinta wata bakwai, juwairiyya sai Murna take Zata samu jika, tace "amma se an haihu zaku koma ko"? Khadija tace " yace idan na haihu ko banyi arba'in ba zamu koma" juwairiyya tayi shuru kawai Dan duk abinda Abdullahi yakeso shi takeso.
Hakan kuwa ya faru ta samu baby boy kwana talatin suka koma Dan sun Dan ciyo kwanaki cikin lokacin makaranta.

Kabir kuwa kullum cikin bin account din Abdullahi yake yana cizon yatsa, dakyar aka samu wasila ta dawo Dan haushinsa takeji akan khadija.


*ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LABARINA ALLAH YASA MU AMFANA DA DARASIN DAKE CIKI AMIN*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now