14

1.9K 224 23
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


14


Sallama yyi mata daga daya bangaren ta amsa a sanyaye, yace "Kin tashi lafiya dear?" tace "Alhmdlh" yace "Sorry you called yesterday, usman ya mance ya tafi da wayata gida sai yanxu muka hadu kasuwa ya bani" tace "Toh" yace "Ya su Ammi?" Tace "Alhmdllh" yace "Maa sha Allah" bata kuma cewa komai ba yace "Hope kinyi break?" Ta gyada kai tace "Uhm" har lkcn ita dai ta kasa yrda Elbasheer bai nuna masa hotunan ba, ko da yake tasan Umar da xurfin ciki may be kawai he is pretending, hakan yasa hawaye ya cika idonta, shirun shi ma yyi na d'an wani lkcn kafin yace "I will call you later dear, xan dan yi abu ne ynxu" cikin sanyin murya tace "Toh" ya mata sallama snn ya katse wayar. Da yamma Fatima na xaune tsakar gida tana duba girkin da Ammi ta daura kasancewar ta fita kasuwa, ita dai har lkcn hankalinta ya ki kwanciya ta rasa dalili, tayi nisa cikin tunanin da take taji sallamar yayan mahaifinta, tashi tayi ta d'an yi murmushi tace "Sannu da xuwa Abba" yace "Yauwa sannu Amira" tabarma ta shimfida masa ya xauna sannan ta gaishesa ya amsa yana tambayarta Ammi, tace "Yanxu xata dawo taje kasuwa ne" yace "Ke me ya hanaki karban sakon kije ki siyo" shiru tayi bata ce komai ba, dai dai nan Ammi ta shigo gidan, suna gaisawa da w'an late mijinta Fatima ta debo masa ruwa ta ajiye sannan ta wuce daki, bayan sun gama gaishe gaishe yace "Kina jina Amina" Ammi tace "Ina ji yaya" yace "Daxu da rana ina xaune nayi baki daga cikin garin Abuja, amma kuma Amina ai ba sai kin nuna mana kusan kin fi mu iko da Fatima ba, tabbas mu ma muna da hakki a kanta, kar kuma ki ga kamar don mun sakar maki yaran gaba daya ko ba ma son su ne ko wani abu, A'a... kawai mun yi hakan ne don mu bar ki kiji da xafi daya, ba ma son ko sau daya kiyi kuka da mu, nan bbu yanda Yahansu bata yi xata tafi da Ummi Kaduna ba muka ki yarda duk don kada ki ga xa mu raba ki da ita, kin taba jin labarin? gaskiya ne bama wani bada taimako, to amma wa kika ga yana da shi bai yi ba Amina, xuwan da muke duk bayan wani lkci shi ma wani abu ne" Da mamaki Ammi ke kallonsa, cikin rashin fahimta tace "Yaya ni ban gane komai ba wllh, wani abu ya faru ne?" Yace "Wasu manyan mutane ne suka xo daga Abuja wai neman auren fatima, kuma ni naga baki taba sanar da mu komai a kai ba kuma ko satin da ya wuce Jibril ya xo nan" Ammi da ta saki baki tace "Daga Abuja kuma Yaya, fatima bata da wani dake nemanta da ya wuce wnn yaro Umar" Shiru yyi yana kallonta shi ma da d'an mamaki, can yace "Toh su kuma wa enda suka xo min su waye?" Tace "Wallahi ban sani ba" yace "Kira fatimar" Ammi ta kirawo Fatima dake daki ta fito ta durkusa gefensu tace "Gani Ammi" Kawunta yace "Ke su waye kika turo min daxu?" Kallonsa take da confusion tace "A ina?" Ammi tace "Yaya nace maka bata da kowa banda Umar fa" sosai gabanta ya fadi tana kallon Kawun nata, yace "Ikon Allah, har fa gaisuwa sun bada an yanke sadaki" Ammi ta mike da sauri tace "Inaaa, wllh yaya ba mu san su a mayar masu da kayansu" Ha6a ya rike shi ma da mamaki yana kallonsu, Fatima da tuni hawaye ya cika idonta tace "Kawu ni wllh ban san ko su waye ba" yace  "Tashi ki je" ta mike tana share hawayen dake sakko mata a sanyaye ta koma daki, kawu yace "Ikon Allah, to kilan kawai irin mutanen nan ne da basa ma yarinya magana sai sun iso gun magabatanta gasu fa manyan mutane wllh, don ni da farko ganin irin motocin da suka xo da shi na xata wani maganan Garba ya kwaso mana aka xo tafiya da ni" Ammi tace "Toh gaskiya yaya kusan abun yi, kuma fa tana da yaron dake nemanta da aure" shiru yyi yana jinjina kai, can yace "lallai kam Ikon Allah, kuma rashin samun layin ki da ban yi bane a lkcn don suna xuwa rai na a bace na kira ki bayan na kira su Jibril da Usman sun taho" Tagumi Ammi tayi, ya mike yace "Bari dai in je ba xancen xama" ta bi sa da ido har ya fita, ta mike ta shiga dakinsu Fatima ta ganta xaune ta takure gu daya tana hawaye, tana kallonta tace "Ki fada min gaskiya ke kika tura mutane can gidan?" Da sauri tace "Wllh A'a Ammi" Ammi ta fi minti biyar tsaye a dakin kafin ta juya ta fita, fatima ta hade kai da gwiwa tana xaman xamanta Husnah ta ja mata a rayuwa, don tasan ba kowa ne yyi haka ba banda Elbasheer, hw did he knw where her relative live? Mikewa tayi ta leka tsakar gida taga Ammi a bakin xaure xata fita, ta koma da sauri ta dau wayarta ta shiga dialing number Elbash, katsewa yyi ya kirata, tana dauka ta sakar masa kuka, ya kashe wayar, ta kuma kira ya ki dauka, ta kira ya fi sau uku bai dauka ba, can sai ga text dinsa ya shigo ta bude test, "I warned u kar ki sake kirana kina min kuka a waya, ki bari ki gama kukan then you call me back" content din message din knn, ta hade kanta da gwiwa tayi kukan me isarta, taji ita da xa a bata wuka da fa xata iya kashe Elbasheer ta kashe Husnah. Har dare Fatima na ta jiran kiran Umar amma shiru bayan daxu da suka yi waya da safe ce mata yyi anjima xai kirata, kawai ta ma san Elbasheer ya nuna masa hotunan da yyi mata a gidansa ne when she was unconscious. Ummi ce ta shigo dakin ta sanar da ita Ammi na kiranta, ta mike a sanyaye ta fita xuwa dakin Ammi, Ammi ta bi da kallo har ta xauna, a hankali tace "Ga ni Ammi" Ammi tace "Fatima" amsawa tayi ba tare da ta kalleta ba, tace "Mutumin da ya kawo kayan abincin can, baki masa maganar da na ce ki masa bane" ta girgixa kai tace "Na masa Ammi, ce min yyi sabida Allah yayi" Ammi tayi shiru Kafin tace "Kin taba gaya masa inda gidan su kawunki yake ne?" Da sauri tace "A'a wllh Ammi" Ammi bata kuma cewa komai ba, bayan wani lkci tace "Ki je ki xuba abinci ki ci" ta fadi hakan ne sanin tun rana bata ci abincin kirki ba, Har fatima ta kai kofa Ammi tace "Umar yyi tafiya ne?" Sosai gabanta ya fadi, ta juyo a sanyaye tace "Ehh" sannan ta fita, kadan ta debi abincin ta koma daki, kasa cin abincin tayi sai jujjuyawa take, ita dai tasan in har asirinta ya tonu a kan waye Elbasheer shikenan ta shiga uku, kuma har abada Ammi xata juya mata baya, tunanin hakan yasa taji komai na duniyar ya isheta, wayarta ne ya fara ring ta dauka da sauri a xaton ta Umar ne sai ta ga akasin haka, lkci daya ranta yyi mugun bacci ganin me kiranta, hawaye ya kawo idonta, dagawa tayi ta kai kunne cikin rawar murya tace "In sha Allah sae Allah ya ruguje plans din ka a kaina, kuma hakkina da kke shiga ni ba yafe ka xan yi ba, sae Allah ya saka min, ko a mafarki kada ka kara saka ran aurena don na fi karfin ka wllh, I am sure tun da na fadi ma parent dina ni ban sanka ba baxa su taba min dole ba ko da kuwa central bank xaku ajiye kofar gidanmu......" Dakatar da ita yyi yace "That's idan ban gaya masu yanda kika kwaso kafa tun daga Suleja kika shigo garin Abuja kika taho gidana ba, ni bana karya don haka bbu abinda xan boye masu da ya faru tsakanina da ke and ke kika kawo kanki, kinga kuwa auren ki da nake son yi tamkar taimako ne xan maki, did you knw what it takes to marry a girl da xata iya barin gidan iyayenta tayi tafiyar kusan awa daya xuwa wani gari gun namiji? Did u knw this reveals that dama can kin saba xuwa gidan namiji knn, don haka wllh i am doing you a favor, Cikin 10% baki cikin class din matan da na so in aura, shi kansa saurayin naki da kike takama da baxai iya jihadin da xan yi ba wllh, and mind you kika sake gaya min maganan banxa a waya billah I will give you the shock of ur life, just dare me...." Yana kai wa nan ya katse wayar, kasa motsawa tayi daga inda take, can tayi wani murmushi tana goge hawayen dake sakko mata a xuciyarta tace duk sanadin Husnah.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now