2

53 2 0
                                    

*~AYUSHA~*


©️Fertymerh Xarah💞

2

Ƙarar wayar shi ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, har ta gama ringing ya kasa ɗagawa, baa daina kiran wayar ba kusan sau uku a jere amma ya kasa ɗaga wayar saboda tashin hankali daya sami kansa aciki, ko a labari bai taba jin wannan halittar ba yau gashi mai ɗakinsa ta haifa masa,me xasu cewa duniya, ya xasu kira wannan jinjirin sannan ya rayuwar wannan jinjirin xata kasance ?

Ina ta kiran wayar yazeed bai ɗaga ba, Allah yasa lafiya Alhaji Abdallah ya faɗa cikin damuwa da alhini yana kallon matarsa Mariya.

Tabe bakinta kawai tayi a ranta addua take Allah yasa abunda aka haifa ya mutu kowa ma ya huta,mtsew taja tsaki qasan ranta tana tauna cingam a hankali,

Alhaji Abdallah ya girgiza kansa kawai ya fice daga falon yana mai qara dialling number ɗan uwansa cikin damuwa.

Alhaji duba kagani yana da qafafu naga sun rufe qafafun jaririn da zani, sai a lokacin ya maida idanunsa kan qafafun jaririn da sauri ya soma dubawa, qafafun lafiya haka suka dinga duba komai na jaririn babu inda yake da wata matsala mutum ne kamar kowane ɗan adam mai rai sai dai shi yaxo da abun al'ajabi da mamaki wato halitta biyu a duniya.

Menene laifin mu sadiya meyasa aka jarabce mu ta wannan hanyar k....tayi saurin toshe masa baki da hannunta tana girgixa kanta idanunta shar da hawaye.

Kayi gaggawar tuba ga Allah domin shi kome yayi dai dai ne kuma shine mai halittar kowane mai rai a duniyar nan, ba dole sai kayi laifi Allah xai jarabce ka ba, kana ina ake haihuwa abun bai zo da rai ba, ake haihuwar jinjiri ba ido,ake haihuwar jinjiri ba qafa ko hannu, wani baya ji, kowa da qaddarar sa wannan itace tamu mu godewa Allah ya karbi addu'ar mu da mu ke barci a zaune muna ibada domin samun haihuwa, wasu har yanxu suna can suna neman haihuwar basu samu ba ko ta halin qaqa?

Astaghfirul-lahal-lazee la ilaha illa huwal-hayyul-qayyoomu wa-atoobu ilayh. Ina neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi. Na tuba Allah ka yefemin da furucina na karbi wannan kyautar da kayi min yau da hannu biyu, kuma nayi alqawarin kulawa da tarbiyantar da shi kamar yanda addini ya koyar da mu idan har ina numfashi a doron qasa. Suka rungume juna suna kukan farinciki...qarar wayar sa ya ankarar dasu daga halin da suke ciki wannan karon da hanxari ya ɗaga wayar cikin sanyin murya

Yace yaya...
'Haba yazeed ina ka ajiye wayar duk ka ɗaga hankalina ina ta kira baka ɗauka ba, lafiya an haihu?
Yace an haihu yaya ya faɗa cikin murmushi yana sumbatar baby dake ta barci.
'Masha Allah ƙanina ina taya ka farin ciki insha Allah gobe xamu shigo.
Yace Allah ya kawo ku lafia yaya.
'Amin, a gaida halimatu kafin nazo, me aka haifa ne?

Jim yayi gabansa na faɗuwa domin rashin sanin me xai ce, ya tsurawa babyn ido.

Me aka haifa ne yazeed? ya qara tambaya a karo na biyu.

Macece ya faɗa batare da tunanin komai ba, sadiya ta tsura masa ido cikin mamaki dalilinsa na ƙin faɗar gaskiya ga ɗan uwansa.

Masha Allah Annam ta sami qanwa nasan zatayi farinciki sosai da hakan, Allah ya raya mana.

Amin ya faɗa yana mai tsinke wayar.

Meyasa baka gayamasa gaskiya ba Alhaji?
Yace kina so na tona asirin abinda muka haifa ne, kina so duniya taji mu zama abun nunawa duk inda muka shiga, yaron mu ya zamo abun ƙyama da hantara acikin abokansa, al'aurar mace ko namiji Allah yayi ta domin ta xama abun boyewa ga kowa sai muharraminta kuma a suturta ta, ni ina son haihuwar mace na samu kuma mace ɗin Xa'a barta, ki boye sirrin y'ar da kika haifa halimatu ko ɗan uwa kada ki sanar dashi, zamuje tare dake muga likita mu nemi sani game da irin wannan halittar.

Ta gyaɗa kanta cikin gamsuwa tana kallonsa.

*

Wannan halittar ba baquwa bace a gurin mu, mun saba ganin cases makamancin irin wannan,a zahirin gaskiya irin waɗannan mutanen kala biyu ne,

Na farko akwai waɗanda ake haihuwa da al'aura guda biyu dana mace dana namiji musamman a qasashen turawa an fiye samun su, ana kiran su da HERMAPHRODITE, mutum ɗaya ne mai halitta biyu wani halittar mace xata fi qarfi a jikinsa wani kuma halittar namiji xata fi qarfi a jikinsa.

Na biyu shine wanda ake haihuwa namiji amma Hormones ɗinsa na mace ne,gashi namiji cikakke a idon mutane amma halittar shi baxata iya bada kwayoyin haihuwa ba saboda na mace ne shi, irin sune kuke jin ana faɗa ace baya haihuwa ai yana da matsala baxai iya haihuwa ba, da sauran su to wannan shi ake kira da namiji mai halittar mace.

A qasashen turawa zaka ga namiji ya maida kansa mace, zai je ayi masa allura hormones na mace su bayyana a tare dashi, xai yi qirji kuma xai iya ɗaukar ciki ya haihu amma kuma namiji ne.

So kada wannan ya ɗaga hankalin ku, naku mai sauqi ne domin jinjirin yaxo da halitta biyu xaa iya aikin ɗaya a raba shi da ɗaya, Dr Wahab ya faɗa yana kallon su cikin tausayawa yanda yaga duk sun damu.

Doctor idan akayi aikin aka cire ɗaya baxaa samu matsala ba ma'ana baxaa rasa jaririn ba? Alhaji yazeed ya tambaya.

Insha Allah lafiya xaa yi aikin ya rayu, dama rayuwa da mutuwa duka suna gurin Allah ne, namu muyi qoqarin ceto rayuwar jaririn ne.

Su kayi ajiyar xuciya shi da halimatu,
Yace doctor yanxu xuwa yaushe ne za'a yi aikin ni ko miliyan nawa ne a shirye nake dana bada domin wannan jaririn koda duk abinda na mallaka ne, ka sanar dani nawa ne kuɗin aikin na biya a yanzu.

Ka kwantar da hankalinka Alhaji yazeed wannan aikin bana gaggawa bane, a gobe ko jibi ko yaushe kake son aiki za'a iya maka shi amma a shawarce ka bari jinjirin ya girma koda shekara biyar zuwa sama ne mu gani.

Meyasa za kace haka? Yazeed ya tambaya a firgice yana kallonsa, saboda me zaka ce bazaa iya aikinsa ba a yanzu bayan na gayama ina da kuɗin ko nawa ne a shirye nake na bada akan wannan jinjirin, halimatu ki ji wannan likitan da maganar banza shekara biyar fa kace? Cikin bacin rai da kakkausar murya yake wannan maganar yana kallon doctor.

Murmushi wahab yayi a matsayinsa na cikakken likita daya jima akan aikin sa ya saba da ganin ire iren irin waɗannan mutane idan ransu ya baci, ya saba da jin kalamai masu zafi da raɗaɗi fiye dana yazeed daya kirasa banza a yanzu.

Yace Alhaji idan kana so ayiwa jinjirin aiki ba wani abu bane za'a yi amma rashin ƙin ɗaukar shawarata zai iya haifar da matsala nan gaba kuma kada kayi kuka dani, xan baka form yanxu ka cike har kuɗin aiki yana ciki kaje ka biya.

Wace irin matsala ce doctor? Halima ta tambaya tana kallon likita a sanyaye, dan Allah kayi mana bayani yanda xamu fahimta.

Kallonta Doctor yayi kamar baxai yi magana ba sai yace matsalar da xaa samu bafa qarama bace kuma ba babba bace, dalilina na cewa ku bari abinda kuka haifa ya qara girma domin a tantance wace halitta ce a jikinsa tafi qarfi shin ta mace ko ta namiji, yanxu xaku iya faɗar ra'ayin ku cewa kuna son ya kasance namiji azo ayi masa aiki a fitar dana mace ya girma ya taso da alamomin mace ku ganshi da gashi,qirji ko mazaunai duka irin na mace ka same shi da hormones na mace murya da fuska duka na mace amma kun riga kun maida shi namiji ya xaku iya gyara wannan kuskuren, ko kuma kuce kuna so ta zama mace yarinyar ta taso da halitta irin ta maza babu qirji ba gashi, muryar maza da sauran halittu irin na ɗa namiji taya xaku bi ku gyara kuskuren da akayi wannan dalilin ya saka nace ku haqura ku bari ya girma ayi masa gwaje gwajen da suka dace domin sanin wace halitta tafi qarfi a jikinsa da za'a barshi da ita acire ɗayar halittar.

Ajiyar xuciya suka saki lokaci ɗaya cikin nuna gamsuwa da bayanin likita, yace kayi haquri doctor kaine bakayi mana bayani da kyau yanda zamu fahimce ka ba, amma yanxu da muka ji mun fahimta kuma zamu haqura da aikin har zuwa lokacin da kace in har muna raye.

Yace babu komai kada ka damu dama a aiki irin namu mun saba da challenges iri iri, kuyi haquri da jarabawar ubangiji kuyi addu'a insha Allah za'a dace.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now