2

9.3K 489 6
                                    

*KUNDIN HASKE*

_Al K'ALUMAN Marubatan HASKE_

KUNGIYAR:-

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

AL 'KALAMIN✍🏼
*NANA DISO*

*DARAJAR MUTUNCIN MU.....*
_('yan zamani)_


BABI NA DAYA
Shafi Na Biyu...

Fatima ce tayi wani dogon murmushi tare da fad'in ni kaina bazan so ki tuna baya ba dan haka barin zancen yafi Alheri...

" fati kenan ai hankakane baya waiwaye Inada abunda zanyi yanzu.

"Hajjaju ce tace walida dazu anty makociya tashigo sai faman masifa takeyi tana nemanki Allah dai yasa ba wata maganar zaki dakko min ba...

" walida ce tayi bazawarar dariya tace Ai magana tun kan ahaifeni akeyin ta kinga kuwa banga ranar daina yinta ba.

Da sallamarta tashiga cikin gidan dakyar Anty ta amsa sannan tace mara kunya fitsararriya ballagaza uwar bin maza ko bunsuru yaganki ya bark'i...

" Ke anty iya bakin ki wallahi baki'isa ba ko kudi ne dake bak'i isa kina zage na ba, ballantana babu ce take dawainiya dake to bari ingayamiki bunsuru yana can nema bunsura kuma gata muna magana, ballagaza kuma yarinyar ki waccan dakike sata tayi kwalliya tafita dan tasamu ma shin-shini baniba.

" Anty ce ta taso tana huce tare da fadin kada ki zageni wallahi...

" Walida ce tace Ana fadin masu kudi basason gaskiya ai har talakawan ma kowa kansa yasa kuma gaskiyar ce bakwaso, ko kin manta ance musulmi dan uwan musulmi ne naga yarinyar ki tafita taci kwalliya amma tana giftawa sai wari da tsami ga bakinta dake faman tashi sai a dinga fakewa da talauci, Ai daku saiwa yara hoda da janbaki gwara ku siya musu abun asken hammata da turaren hammata kokuma alumun, banga amfanin cin kwalliya hammata na tashi ba? Janbaki har janbaki abakin yarinya sai tayi maka magana kayi tunanin kwasar kashi akeyi...

Brush komai rashin tsadarsa ai brush ne ko babu man goge baki ai akwai gishiri ko gawaye sai mace ta wanke bakinta,Ai kazantar da karaina wataran ita ke zama babba bazaku gyara yaranku ba kuma bazaku so agaya muku gaskiya ba...

" Anty ce tayi shiru tana fadin to ai ni bahaka tace min ba shiyasa rai na yabaci Amma...

" walida ce tace kinga rik'i Amma... dinki banzo nan dan naburgeki ba, Gaskiya ce sai dai banganta ba Amma ace ga gurin da yakamata kukula da yaranku kwata kwata bakwa kulawa, kwalliyar janbaki da hoda ai asarar kudi ne akwai lokacin su Amma sai anfara gyara ciki kafin ayi tunanin waje mace mace ce kuma duk muninta mai kyau ce.

ki kula da pant dinta da bra tana wanke wa akan kari saboda infection dinnan sai yakama yara tun suna kanana arasa yadda za'ayi gaba, ki koya mata aske gashin mara da na gaba da wanke tafin kafarta yarinya fa idan har bata wari duk inda tashiga sai kiga ansota amma tana shiga ana fargaban zama kusa da'ita.

Daga karshe ace cuta ce nan kazantar ka ta jawo cuta, idan kin gyara kanki in baki gyara ba zaki gani gaba sai anjima...

" Anty ce tace tabbas kallon banza akeyiwa walida Amma yarinya ce wacce Al'umma ke son irinsu sannan tace nagode, anty tace kinji masu son ku gyara wanda suka san darajar mutuncin ku wannan maganar da fad fada Ni kaina naga matsalata aciki zangyara inshaaAllahu...


Walida tana fita ta tarar da minister a bakin mota sai kallonta yakeyi...

" kai Alhaji irin wannan kallo haka sai kace kaga zinare??

" Darling ai kinfi zinare!

" A'a gyara kalmarka walida not darling!

" Ayimin afuwa please? " gefe tayi da fuskarta tace anyi...yanzu sai ina??

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now