15

2K 243 40
                                    

KUNDIN HASKE

Haske Writer's Association💡

(Home of Experts and perfect Writer's)

*SANADIN K'AWA*

NA

*khaleesat Haiydar*

BABI NA GOMA SHA HUDU


15

Washegari har karfe goma na safiya bata fito ba tana kwance, ta rasa gane xaxxabi ne, damuwa ne, ko tunani ne ya sa ta gaba, Ammi ce ta shigo dakin tana kallonta tace "Lafiya kike kwance har yanxu?" Girgixa kai tayi cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo..." Ammi tace "Kinga ni xa ki bari da wahala idan kika janyo ma kanki wata cutar, ki tashi kije ki dau abin karyawar ki, sannan ki sha magani, don ba ruwana" daga haka Ammi ta fita, mikewa tayi jiki ba kwari ta bi bayanta, wanke baki tayi ta juye ruwan wankan dake kan coal pot ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta shirya, ruwan tea kadai ta iya sha ta balla paracetamol ta hadiya sannan ta koma ta kwanta, wayarta dake ajiye yyi haske kasancewar a silence yake, ta jawo a hankali tana kallon screen din, message ne ya shigo na Umar, ta mike xaune da sauri gabanta na faduwa, kasa bude message din tayi don tasan kilan ba na alkhairi bane, ta hade kanta da gado tana kuka a hankali, jin Ammi na waya a tsakar gida da alama xata shigo dakinsu tayi saurin goge idonta ta kwanta, har bayan kusan minti goma Ammi bata shigo dakin ba, ta kara kallon screen din wayar har wani rawa hannunta yake tsabar tashin hankali, discarding message din tayi a gaban screen din wayar don bata jin xata iya karantawa, Ammi ta shigo dakin tace "Ki shirya xa mu je can gidan kawun ku yanxu, tana fadin haka ta fita, jigum tayi bayan fitan Ammi, can dai ta mike jiki ba kwari, Hijab har kasa ta daura kan doguwar rigar jikinta, ko eye pencil bata sa ba ta fita ta ga Ammi tsaye tsakar gida alamar ita take jira, tana ganin ta fito ta nufi xaure ta bi bayanta, haka nan taji gabanta na faduwa sosai barin da taga Ammi bbu annuri fuskarta, addu'a ta dinga yi a xuciyarta har suka iso bakin titi, tana son tambayar mahaifiyar tata me ya faru xa su je can gidan amma bata samu fuskar tambayar ba har suka hau adai daita, tafiyar minti kusan sha biyar suka yi suka iso gidan kawunta, direct dakin mai dakinsa Ammi ta shiga ta bi bayanta, gaisawa suka yi da mutunci, Fatima ta durkusa ta gaisheta ita ma, ta amsa da fara'a tana tambayarta su Ummi, Bayan wani lkci Ammi tace "Daxu yaya ya kirani wai mu taho, kuma naga kamar baya gidan" tace "Lahh yana ciki tare da bako ko ince sirkinmu..." Ammi bata ce komai ba, Maman Hafsa ta mike ta fita, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Fatima to tashi kije yana kiran ki" sosai xuciyarta ya shiga bugawa, ta kalli Ammi dake kallonta, ta mike jiki a mace ta fita dakin, parlon kawun nata ta nufa tana kallon well polished cover shoe dake bakin kofar, murya can kasa tayi sallama ya amsa yyi mata ixinin shigowa, kanta a kasa ta shiga dakin xuciyarta ya tsananta bugawa, sai bayan da ta shiga ta dago kai don duba inda xata xauna suka hada ido da Elbasheer dake juya car key din hannunsa, saurin sauke kanta tayi wani abu ya tokare mata a makogwaro taji kamar ta saki kuka amma ta dake, kusan opposite dinsa ta xauna, cike da karfin hali ta gaida kawunta, ya amsa yana tambayarta sun xo lafiya, kasa cewa komai tayi yace "Fatima" dagowa tayi ta kallesa a sanyaye, yace "Kinsan wannan mutumin?" Kallon Elbasheer dake kallonta tayi, irin tsare ta da yyi da ido yasa ta kasa kwakkwaran motsi xaunen da take, da sauri ta shiga gyada ma kawunta kai kamar kadangariya, yace "Toh ke kika ce ya turo magabatansa?" Lkci daya hawaye ya silalo fararen idonta, Elbasheer ya shafa sajensa a hankali yace "Kawu dama tun farkon da muka fara xuwa akwai maganan da ya kamata muyi da kai, so bana son yin maganar gaban iyayena but....." Fatima ta katse sa da sauri cikin sarkewar murya tace "Kawu nice nace ya turo" kallonta kawun yyi da sauri, "Amma kika ce baki san sa ba jiya da naje can gidan ku" ya tambayeta yana kallonta da kyau, share hawayen idonta tayi cikin raunin murya tace "Ina jin tsoron Ammi ne kayi hakuri" kawu yyi shirun kusan minti daya, can ya kalli Elbasheer yace "Toh kai wani maganan kace xa ka min?" Girgixa kai yyi hade da murmushinsa me kyau yace "Abinda ta fadi xan fadi maka dama kawu...." Kawu bai kuma cewa komai ba, Fatima kam kanta a kasa xuciyarta na mata suya, muryar kawu taji yace "Toh tashi ki je" dagowa tayi da idonta da yyi jajir cikin rawar murya tace "Amma kawu don Allah kar ka fadi ma Ammi xata yi fushi da ni sosai" murmushi kawun yyi yace "Tashi kiyi tafiyar ki" a hankali ta mike ta nufi kofa Elbasheer ya bi ta da kallo har ta fita kofa, kasa shiga dakin maman Hafsa tayi ta takure waje daya kan tabarmar dake shimfide tsakar gidan, ba a jima ba sai ga Elbasheer ya fito, har ya duka ya saka shoes dinsa bai daina kallonta ba, ita kam wasu hawaye masu xafi suka dinga sakko mata, takawa yyi har gabanta ya duka yana kallon ta, ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, dago kanta yyi ta buge hannun tana shessheka ta mayar da kanta, d'an murmushi yyi ya mike ya fita gidan. Muryar kawunta taji yana tambayeta me take a nan, ta dago da sauri tana goge idonta, yace "Kukan me kika xauna kina yi" kallon kofar dakin maman Hafsa tayi ta tafi gunsa cikin rawar murya tace "Kawu don Allah kada kace ma Ammi ni nace su xo, wllh xata yi fushi da ni" yace "Toh yi wucewar ki ciki ki kira min Aminar" a sanyaye ta juya ta shiga dakin Maman Hafsah, tun da ta shigo Ammi ke kallon ta, a hnkli tace "Wai Ammi ki je in ji kawu" Maman Hafsa tace "Kukan me kike kuma?" Ta girgixa kai kawai, mikewa Ammi tayi ta fita, duk xancen da maman Hafsa keyi ita kam ba apprehending take ba, bata ma san me take cewa ba, har Ammi ta shigo dakin, kai kana ganin mood dinta kasan  ba lafiya, nan ta shiga tsara ma Maman Hafsa duk yanda suka yi da kawu, Maman Hafsa da ta saki baki har ta kai aya sannan tace "Bata san shi ba kuma, an shiga uku, a ina aka taba aure haka? A'a gaskiya da sake bari in samu baban Hafsan, don me xai ce haka, ae sai jama'a su ce don ba shi ya haifeta ba shi sa xai yi haka, haba fisabilillah" tana kai wa nan ta fita, Ammi tace "Tashi mu je" mikewa Fatima tayi kamar jiri xai dibeta suka bar gidan da Ammi, har dare daga ita har Ammi kana ganinsu kasan suna cikin damuwa, damuwar da ta ga Ammi ta shiga ya fi daga mata hankali Wanda hakan yasa ta kasa daina Kuka, misalin karfe goma kiran Elbasheer ya shigo wayarta, har ya gama ring bata dauka ba shi ma bai sake kira ba, kwana tayi sallah tana rokon Allah ya wargaza plan din Elbash a kanta, sai bayan da tayi sllhn asuba bacci me nauyi yyi awon gaba da ita, hakan kuma bai hanata tashi karfe bakwai ba. Da rana ta shirya ta samu Ammi a daki ta durkusa tace "Ammi don Allah xan je gidansu Nafisa in dawo yanxu" Ammi tace "Toh" naira dari Ammi ta bata kudin mota, a sanyaye ta mike ta fita gidan. tayi sa'ar samun Nafisah don xata fita islamiyya a lkcn, Nafisa na ganinta da mamaki tace "Baki da lafiya ne fati?" Nan da nan idanuwanta ya kawo hawaye, Nafisa ta ja ta suka shiga daki ta durkusa gabanta da damuwa tace "Subhanallah, me ke damun ki Fatima, what happened?" Fatima ta fada jikinta tace "Na shiga uku Nafisa, na ja ma kaina, Husnah ta sa na cuce kaina" Rikicewa Nafisa tayi tace "Ki gaya min me ya faru don Allah" Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta labarta ma Nafisa komai, tsuru Nafisa tayi tana kallon ta, girgixa kai tayi ta dafe kai tace "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un... Don me xaki boye gaskiya Fatima "Why did you hide the truth from Ammi, kin yi making babban mistake, yanxu ki tashi mu je ni da kaina can mata bayanin komai don a dakatar da mugun nufinsa a kanki" girgixa kai Fatima tayi da sauri tace "Aa bana son ta kuma fushi da ni...." Kasake Nafisa tayi tana kallon ta, a fusace tace "Kina nufin aurensa xa ki yi kenan" Fatima ta hadiye abu da ya tokareta da kyar tace "Allah xai ruguza manufarsa, Allah baxai yarda ba," Nafisa ta dafe kanta tace "Toh don me yasa baki bude text din Umar ba ki ji abinda xai ce maki" Ta girgixa kai a sanyaye tace "Baxan iya ba Nafisa, dama ke nake son ki duba min gashi na mance wayar a gida" Nafisa tayi shiru duk jikinta ya mutu, a hankali Fatima tace "xan koma Nafisa nace ma Ammi baxan dade ba" Nafisa tace "Baxan jima a makaranta ba yau, xan biyo nan gidan ku, in sha Allah baxa ki auri mugun nan ba, ki dai ki je sai na xo anjima" A tare suka fita bayan Fatima ta shiga dakin Ummansu ta gaisheta, sai da Nafisa taga ta hau adaidaita sannan ta dau hanyar makaranta a sanyaye ta na tunanin mafitar da xata nema ma kawarta. Fatima na isa kofar gidansu taji d'an hayaniyar mutane cikin gidan, gabanta ya fadi sosai ta shiga ciki da sauri, turus tayi tsakar gida tana kallon Akwatunan dake jibge tsakar gida guda daya daya har goma, matan anguwansu da suka shigo na ta yabawa ana sa albarka.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now