Shafi na Tara

1.5K 118 0
                                    

*KUNDIN HASKE*

  *AL-K'ALUMAN MARUBUTAN HASKE.*

*K'UNGIYAR:-*
   *HASKE WRITTERS ASSOCIATION.*
(Home of expert and perfect writters)

*TAREDA AL-KALAMIN*🖋
Zaynab bawa (zeeyybawa)
            
   *TALLACE-TALLACE*
(Sanya idanuwa akan tarbiyar yarnmu)

*BABI NA BAKWAI*

*SHAFI NA  TARA*

   Humaira bata leqa gidan ummanta ba sanda tagama WAEC nata dake WAEC kadai zatayi, bazatayi NECO ba,
  Hutu tajewa ummanta da niyyar tayi mata d'an kwana biyu dake ynzu ba makaranta zatana zuwaba,
Tunda humaira taje gidan kowa yake yaba irin tarbiyarda tasamu domin
A kullum da safe humaira tatashi takan share d'akin mahaifiyarta tayi mata duk wasu ayyukanda yakamata sannan takoma d'akin mama(maman mlm yahuza) itama tayi mata ayyuka,
A kullum itace take share mata d'aki ta mopping d'insa, ranarda mama tazauna sanda kwalla yafito mata domin tana tunanin irin kyawawan halayya na umma da d'iyarta takaicin rasa iri irinna umma takeyi akullum kwanan duniya,

Shikuwa mlm yahuza baisan wanda mahaifinsa ya auraba shidai kawai yasan cewa mahaifinsa yayi aure sannan kuma duk ranarda yashigo gidan bayan yagaida mahaifiyarsa itama yakan shiga ya gaidata,

Yauma kamar yanda yasaba yashigo gaida mahaifiyarsa zai fita makaranta,
Da sallama ya shiga humaira wacce take shara ta amsa sallamar kunnuwansa suka jiye masa kamar muryar humaira amma kuma sai yake gani muryarce kawai tayi kama idan kuma bahakaba mai zai kawo humaira gidansu?"

Amma yana shiga idanuwasa sukayi tozali da humaira tana shara mamakine yakamashi sosai harya gaza boyuwa,

D'agowarda humaira zatayi kenan suka had'a idanuwa da mlm yahuza, d'an rusunawa tayi tagaidashi, batareda wani alamun birkicewa kokuma akasin haka afuskartaba, domin tana cikin shigarta ta kamala kamar yanda tasaba,

Amsawa yayi sannan yace mama tana cikine?"
Gyadakai humaira tayi had'eda fad'in eh tana ciki,
Zama yayi d'aga daga cikin kujerun palourn sannan yace" d'an kiramun ira dan Allah, toh humaira tafad'i, had'eda
Ajiye tsinstiyar hannunta tashiga ta sanarwa mama zuwan mlm yahuza sannan tadawo taqarasa sharan,

Fitowa mama tayi tana fad'in sannu y'ar albarka d'iyata nagode sosai, Allah yayi miki albarka,

murmushi humaira tayi had'eda fad'in ameen sannan  fice daga d'akin,

Rusunawa mlm yahuza yayi ya gaida mahaifiyarsa sannan yadubeta cikin mamaki dakuma al'ajabi yace" mama naikuma humaira takeyi anan gidan?"
Aiki take muku?" yayi maganar cikin alamun tambaya da qin gaskatawa,

Girgizakai mama tayi sannan tace" Aa yahuza ba aiki takeyiba mahaifiyarta itace matar babanku aii,

Jijjigakai yahuza yayi yana tuno maganar mahaifinsa dayake fad'in yasan abinyi wato abinyin kenan shine ya auro mahaifiyar yarinya,

Allah yakyauta yafad'i afili sannan yadubi mahaifiyarsa yace" mama nizan wuce makaranta, cikin tausayawa mama ta dubeshi sannan tace" yahuza idan bazakayi lattiba ina bukatar yin magana dakai,

Komawa yayi yazauna yana fad'in mama kefa mahaifiyace ko umartata kikayi da kada naje makarantar bazaniba, balle kuma kinason magana dani,

Gani kiyi duk wata maganarki babu wani lattinda zanyi,

Murmushi tayi sannan tace" toh Allah yayi maka albarka,

Dama zan baka hakurine gameda maganar humaira, dan Allah kayi hakuri nasan nayi maka ba dai-dai ba  matsayina na mahaifiya kamata yayi ace nayi bincike akan yarinyar, batareda nayi hakanba na yanke hukunci, kasancewar yarinyar tana zaune gaban mahaifiyarta,

Abunda bansaniba shine muda yaranmu suke gabanmu nida mahaifinka muke ikirarin sun sami tarbiyar uwa data uba,  babu abunda zasu nuna mata wajan tarbiya, nayi dana sanin wannan kalma tawa ta y'ar mace, nagane cewa bawai don mace ta goyi yarinya shine hakan yake nufin yarinyar batada tarbiyaba,

Tunda mama tafara magana kan mlm yahuza yana qasa bai iya furta komaiba,

Sanda yaji tayi shiru saiya d'ago yace" mama dan Allah kidaina bani hakuri kefa  mahaifiya tace kuma kinada iko akaina, banga laify donkin hanani wani abun kin za6amin waniba,

Girgizakai mama tayi sannan tace" hakane yahuza amma kuma kaika kasance yaro mai biyayya gareni, domin baka yimun musu kokad'an sannan kuma aiyazama dole nidakai muyi jimamin rashin wannan yarinya mai tarbiya, amma matar mutum kabarinsa bancirerab cewa zata zama matarkaba, amma ynzu muyi addu'a  Allah yayi mana za6i mafi alkhairi,

Ameen mlm yahuza ya amsa mama tace tashi kaje yahuza Allah yayi maka albarka,
Nanma ameen d'in yasake amsa sannan yayi mata sallama yafice,

Koda yafita bai fice kai tsayeba sanda ya shiga d'akin umma itada humaira yasamesu  apalour suna shirin karyawa gaida umma yayi yatashi zai fice umma tadubi humaira tace" humaira haka akeyi?" babu gaisuwa, murmushi mlm yahuza yayi sannan yace" ai umma mun gaisa ad'akin mama,
Eyyer toh aina d'auka baku gaisaba umma tafad'a cikin dariya, dawonan ka karya kullum kazo d'akinnan saina yimaka maganar karyawa amma sai kaqi, murmushi yayi baita6ajin yana sha'awar karyawa ad'akinba sai yau don haka yadawo yazauna umma tadubi humaira tace zuba masa abincin, cikin nutsuwa ta qaraso tazuba masa, yadubeta yanda take komai cikin nutsuwa, lallai zancen mahaifiyarsa gaskiyane dole suyi jimamin rasa yarinya mai tarbiya irinta,

D'aki humaira takoma tazauna tabarsu awajan harsuka gama sai bayan yatafi sannan tafito itama takarya sannan takwashe kayan takaisu wajan wanke-wanke."

********

Tafiya takeyi kamar zata tsinke sai wani karai raya takeyi kamar zata kamar wata karuwa haushi ta takaici suna gama cika mlm yahuza wai arasa wace yarinya za'a had'ashi da ita sai wannan marar tarbiyar, hanya yake qoqarin canjawa domin kokad'an baiso suhad'u takaici yakeji idanya ganta,

Ganin yana neman kaucewa yasanya qara sauri harta cimmasa, tana zuwa ko sannu babu tace yaya yahuza guduwa  zakayi?" tayi maganar tana qass ta chewing gum, kallonta yayi cikin  takaici duk fuskarta tayu wani farii fauu hannayenta baqaqe qirin da qafafunta gawtaa babbar waya a hannunta wanda zai iya rantsewa idan za'a saida duk wani abunda yake cikin gidansu bazaikai kud'intaba sannan kuma yasan kud'in tallanta bai isa yakai kud'in wannan wayaba, koda yake yasan ynzu tadaina talle tunda yafara nemanta yahanta yin tallan tunda idan tafita banda sheqe ayarta babu abunda takeyi awajan, tayi shigar banza tatafi wajan talle shago-shago babu wanda bata saniba, tunda yahanata talla sai shegen tambayarsa kud'i datakeyi har dana sanin hanata yayi,

Maiya fito dake dasafe haka?" yafad'a yana 6atarai, kame-kame tafara tana fad'in yaya gidansu qawata naje nakwana shine ynzu zan koma gida,

Tsaki yaqaraja domin yasan qarya takeyi babu wani gidan qawarta dataketa,
Baisan cewa gidan saurayinta taje takwana ad'akinsaba, subhanllahi wannan wace irin rayuwace, wani haukane zaikaiki matsayinki na uwa kibar d'iyarki tatafi gidan kawarta takwana?" kinbita kinga gidan qawartan takwana?" shinwai idanma kawartarce kinmanta meyake faruwa yanzu tsakanin mata da mata, wannan cuta tafi zina illa, illolin mad'igo yawa suke dashi, wallhy jarabar wannan abun tafi jarabar zina, jarabar wannan abu tasanya mana al'umma agaba,Wallhy iyaye saimun tashi tsaye wajan tarbiyar yaranmu, ba mu'amalar d'iyarki da maza kawai zaki dubaba wallhy harda matanma domin suma yanzu sun zama tashin hankali ga al'umma, idan y'ar mad'igo d'aya tashiga cikin al'umma zatayita 6atata, Allah ka karemu, sukuma masuyi susan cewa illar wannna abun wallhy bayanzu abun yakeba saikinyi dana sani marar amfani cikin rayuwarki,
Gara tun wuri ku shiryu wallhy, wai tayayama za'ace jarabawa kala-kala baza suna sauko manaba?"😭😭 bayan irin sa6o kala-kala damukeyi yiwa ubangijinmu, wallhy Allah yana hakuri damu, domin irin abubuwanda akeyi awannan zamani yawuce tunani, ya Allah, Allah, ya arrahman ya al-rahim ya al-mulk ya al-quddsu ya al-salam, ya zuljalal wal ikram, Allah muna tawassali da sunayenka kyawawa Allah ka kare mana al'umma, Allah kakaremu da kariyarka, Allah kakare al'ummar musulmi daga fad'awa halaka ameen ya Allah."😭😭😭👏👏👏

Cikin kyankyami mlm yahuza yake dubanta yace kibari zanzo da daddare, domin shikam idanba hancinsaba wallhy wani irin warin gardawa takeyi tun tsayuwarsa yakeji kuma yadameshi,

Murmushi tayi tace toh saikazo gyadakai kawai yayi yawuce yabar wajan."

To be continued

Ur's zaynab Alabura."

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now