3

1.3K 107 9
                                    

*KUNDIN HASKE*

   *ALK'ALUMAN MARUBUTAN HASKE*

   *K'UNGIYAR HASKE WRITER'S ASSOCIATED*💡
(Home of expert & perfect writer's).

*Tare da:-*
     *Alk'alamin*

*MARYAM IBRAHEEM*
(Ummu Hanan).

*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*

  *SATAR FITA*
       (Halayyar wasu matan).

*SHAFI NA UKU*

  
    *Bayan sati d'aya*

Rabi'a bata k'ara fita ko Ina ba saboda zazzab'in da take yini dashi, gashi duk jikinta ba dad'i hakan yasa dole ta hak'ura da yawace yawacen da take.

   Ranar da taji dama dama kuwa sai data tambayeshi unguwa dan jin zaman gidan take kamar akan k'aya.

   "Dan Allah Abban husna ka barni yau inje gida kaga na dad'e ban jeba"(dan duk d'an banzan yawonta bata cika zuwa gidansu ba saboda tasan halin babansu baison yaga an cika zuwa sai yace yawo suke kuma dole idan taje saiya ganta saboda a k'ofar gidan yake sana'arshi) cikin marairaicewa tayi mgnr tana kallonshi.

   Goshin shi ya dafe yace
   "Kai Rabi'a, kina fama ma da kanki amma bazaki hak'ura ba ba inda zaki gaskiya.

Shagwab'e masa tayi tana masa magiyar ya barta taje.

Tsaki ya d'an ja yace
   "Naji to amma ba yau ba kibari sai gobe idan Allah ya kaimu lahadi ce bana fita da wuri sai in kaiki nima sai in gaishesu daga nan".

   Har zatayi masa musu sai kuma ta tuna yadda take fita batare da saninshi ba wannan d'in ma ai ba sani zaiyi ba.

   "Shikenan Allah ya kaimu goben" ta fad'a cikin fara'a.

   "Amin".
Ya amsa mata yana fitowa daga d'akin dan dama yana shirin fitane suke mgnr.

Har soro ta rakashi bayan ya fita da mashin d'inshi bayan tafiyarshi ta rufe gidan ta dawo ciki.

   Tana dawowa ba b'ata lokaci ta hau shiri, nan da nan ta shirya sannan ta shirya husna dan yau da ita zataje.

Fitowa tayi ta kulle gidan, tun a layin ta tare mai napep daya kawo wasu ta hau tana fad'a masa inda zai kaita.

   
          ★★★
Yinin gidansu tayi ranar sai la'asar sakaliya sannan ta baro gidan, maimakon tayi gida sai ta wuce gidan wata kawarta dake kusa da unguwar🤦🏻‍♀wadda sukayi islamiyya tare, can ta shantake sukai ta hira kasancewar sun dad'e basu had'u ba, sai datayi sallahr magreebah sannan sukayi sallama ta tafi bayan ta had'awa husna kayan kwalliya.

    Tun kafin magreebah yaji jikinshi ba dad'i kamar zazzab'i na shirin kamashi ga kanshi dayake masa ciwo dan haka suna idar da sallahr magreebah a inda suka saba gabatar da jam'insu cikin kasuwar yayi sallama da mutane ya tattara komi ya maida shagon ya kulle ya hau mashin d'inshi ya tafi gida.

    Sai dai me?, Yana tsaida mashin d'inshi yaga gidan a kulle da kwad'o, wani irin b'acin rai ne ya ziyarceshi gami da takaici, wato daya hanata fita saida data fitan?, Lallai kuwa zai nuna mata kuskuren ta na k'etare mgnr sa datayi.

   Sauka yayi daga mashin d'in, Allah ya taimakeshi dama yana da spare key a hannunshi wanda ya hadasu da key d'in mashin d'in nasa, bud'e gidan yayi ya shiga da mashin d'in ko d'aki bai shiga ba ya fara safa da marwa a tsakar gidan cikeda tsananin b'acin rai.

     Tun daga nesa take ganin kamar gidan a bud'e, sauri ta k'ara dan tabbatar da abinda idanunta ke gani gaskiya ne, tunda iya saninta Ahmad sai bayan sallahr esha'ee sosai yake dawowa.

     Wani irin muguwar faduwa gabanta yayi sakamakon tabbatar da zarginta, gida a bud'e ga mashin d'inshi a soro.

   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'oun,na shiga uku". Abinda ta ambata kenan cikin tsananin faduwar gaba.

  Tamkar marar laka jikinta yayi bala'in sanyi ta shiga gidan ko sallama kasayi tayi.

   Kai da kawowa kawai yake yi ya goya hannayenshi duka a bayanshi, cak ta tsaya tana kallonshi jikinta sai rawa yake ji take tamkar ta juya ta koma, shima d'in itan yake kallo cikin tsantsar takaicin abinda tayi masa, husna kam tana sauketa ta nufi gurinshi da murnar ta,
  "Daga Ina kike?" Ya jefo mata tambayar yana huci.

   "Dan Allah kayi hak'uri abban husna wlh gida kawai naje", cikin rawar murya tayi mgnr tana matso hawaye.

   "Me nace miki d'azu da mukayi mgnr..? Shine saboda kin rainani ban isa in fad'a miki mgn kiji ba kika d'auki k'afa kika tafi ko?, to kuwa saidai ki koma inda kika fito''

   "Dan Allah kayi hak'uri Ahmad bazan k'ara ba, wlhy tsautsayi ne me kakeso inje ince musu...dan Allah ka taimakeni" cikin kuka ta k'arasa mgnr tana hada hannuwanta alamar rok'o.

   Fumfurus Ahmad yak'i kulata duk da irin magiyar da take masa hakan baisa ya saurareta ba saima husna daya dauka ya sab'a a kafad'arshi ya fice daga gidan, ganin hakan yasa itama ta fito tana cigaba da rok'onshi amma bai kulata ba ya dire husna ya fito da mashin d'in ya d'orata suka bar gidan.

   Kuka take sosai, bata tab'a zaton Ahmad zaiyi fushi haka ba, dan ta sanshi yanada sanyin hali da hak'uri, dana sani fal ranta tunanin ta d'aya ta Ina zata fara da iyayenta me zataje ta gaya musu.

    Dolenta ta k'ara fita titi ta tare mai napep ta shiga tana ta kuka gamida faduwar gaba dan tsoron mahaifinta dan mutum ne mai zafi sosai.

***
      Hajiya na zaune kan kujera a falonta, itada rufaida suna kallon tashar arewa 24 cikin shirinsu na gari ya waye da suke maimatawa, rufaida nak'asan darduma tana shafawa hajiyan man zafi a k'afafunta, yayi sallama ya shiga, amsawa tayi tana binshi da kallo daga gani tasan ba lafiya ba saboda yanayin yadda ta ganshi ga kuma husna data gani a hannunshi.

   Zama yayi bayan ya zaunar da husnan kan kujera ya fara gaida hajiyan.

Sai data yiwa husna alamun tazo wajenta da hannunta sannan ta amsa masa.

    ''lafiya kuwa Ahmad...?"

    Ta tambayeshi cikin kulawa,
   A hankali ya sanar da ita abinda ya faru.

    Kai ta shiga girgizawa cikin rashin jin dad'in abinda ya faru

   "Kayya Ahmad,kayi saurin yanke hukunci kuma gsky banji dad'i ba".

  "Hajiya na fara gajiya ne ko ranar da kukaje d'in nan fa kuka tarar bata nan bansan ta fitaba wllhy taya zaman aure zai yiwu a haka?"

   "Wllhy kuwa yaya sau nawa Ina zuwa gidan bana sam.... hararar da hajiya ta jefa mata ne yasa taja bakinta ta tsuke

   "To y'ar k'arawa wuta fetur ana neman ayi sulhu kina dad'a rura mgnr, juyawa tayi wajen Ahmad d'in tace

   "Ya kamata gobe kaje ka dawo da matarka kayi hak'uri zaman aure dole sai ana hak'uri daga duka b'angarori biyun wato miji da mata, kayi hak'uri bawai goyon bayanta kuma nake ba a'a nima insha Allah zanyi mgn da ita, zan yiwa Aminu magana(babban yayansu), sai yaje suyi mgn da mahaifinta kafin kaje ka taho da ita".

    "Shikenan hajiya za'ayi yadda kikeso insha Allah". Ya fad'a ba wai don ranshi na soba sai dan baya k'etare mgnr mahaifiyar tashi, amma yadda yaso saita dad'e a gida ta gane kuskuren ta sannan zai maidata.

   "Masha Allah ubangiji yayi albarka".

   "Da Amin ya amsa yana lumshe ido dan jin dad'in addu'ar mahaifiyar tashi.
  

     "Rufaida tashi ki kai husna d'aki tunda tayi barci sai kizo ki zubo masa abinci nasan dai bakaci abu ba ko...?" Ta fad'a tana maida kallonta gareshi.

   Kai kawai ya kad'a mata batare daya yi mgn ba....

*Mrs Salees Mu'az*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now