Last page na ummy aysher

1.5K 123 10
                                    

KUNDIN HASKE

ALK'ALUMAN MARUBUTA🤝🏻

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡💡💡

Wattpad:- Ummishatu

TARE DA ALK'ALAMIN

*UMMI A'ISHA* 👌🏻

*BAK'ON YANAYI....!*❤
      (Kafar sadarwa)

Babi na Ashirin da d'aya (21)

*Last page*

   ****Washe gari da safe kamar yadda na alkawartawa harun haka yazo ya tisani agaba dan son jin karshen labarin da nake bashi dan adakina ma ya karya,karasa shirya ummulkhair nayi sannan nazo na zauna naci gaba daga inda na tsaya,

"Sallamar na amsa mata nan tace min maman haidar baki ganeni ba ko? Sunana latifat daga group din mom Hisham,murmushi nayi nan muka sake sabuwar gaisuwa kuma tun daga wannan lokaci muka kulla zumunci mai karfi wannan shine silarta na zama kawata babba a online dan tana da pics dinmu nida haidar babu adadi sannan kuma ta bukaceni da wai inbata address din gidana tana so ta zo murna na shiga yi nan nabata,ranar da zata zo nayi mata sauka ta alfarma lokacin abulkhair baya nan,tun daga wannan zuwan nata bata sake dawowa ba duk da dai tayi min karyar cewa wai ita matar aure ce ashe karya take,muna zaune da mijina lafiya sai kawai naga yafara canja min baya dawowa gida da wuri idan yana gari sai can dare sannan ya daina tattalina kamar da gashi babu kulawa da tausayi kamar da nanfa abun yafara damuna har nake sanar da latifat ko zata bani shawarar da ta dace amma sai tace ai wulakancin maza kadan nafara gani badai nace ni mijina dan aljannah bane to gashi yanzu yafara nuna min halin nasu. Abun duniya fa duk yataru ya isheni daga karshe yasanar dani wai aure zaiyi kuma shi bama yason ganina kwata kwata kawai hakuri yake yi,shirye shiryen aurensa kawai yasaka agaba duk da su innah basuyi na'am ba amma haka yadage yace shi aure zaiyi,bayan ansaka rana anyi komai yace indawo gidan innah wai zaiyi gyara agidan to tun daga wannan zuwan har yau dinnan ban sake saka kafata agidanba dan sai biyoni yayi da sauran kayana,ita kuwa amarya ta tare adakin mijinta bayan andaura aure,yakashe mata kudi masu yawa a wannan auren amma ni ko hankici bai hada ni dashi ba,bayan bikin nasu da sati biyu a group naga latifat ta tura hotunan bikinta na dinner da kamu wai atayata aure ina budewa naga abulkhair amatsayin ango ashe shiyasa dama nayita yimata magana tana kin kulani,ashe abinda yafaru bayan tazo gidana awayata ta dauki number abulkhair tun daga ranar ta rinka bibiyarsa itace har wurin aikinsa da sauran wuraren da yake zama da yake abune da aka hada da sihirce sihirce lokaci kadan suka samo kansa har ya amince da batun aurenta nikuma yajuya min baya...... Sauran abubuwan kuwa da suka faru kaima shaida ne saboda wani agabanka ma akayi....."

Tagumin da harun yayi ya cire sannan cikin tausayawa yace,

"Anty..... Anty ni zan taimakeki,zan aureki idan har kin amince domin......"

Cikin razani ta kalleshi da firgici saboda jin abinda yace,

"Haba harun.... Ai abinda bazai taba faruwa ba kenan,ina ni ina kai"

"Wallahi Anty ni zan aureki idan har kina sona...."

Wannan shine ya zama sanadiyyar rikici da fadansu wanda har yake neman shafar zumuncin da ke tsakaninsu abulkhair yana cewa ajawa harun kunne babu shi babu ni,nikam da abun ya isheni kayana nasoma tattarawa zan tafi gidan iyayena amma su innah suka hana.

***
Bayan wata uku.

Al'amura sunci gaba da faruwa nidai na dukufa da addu'o'i da kai kuka na ga Allah akan yayi min maganin damuwata sannan yayi min zabi na alkhairi,

Muna zaune nida inna atsakar gida tana surfen alkama wadda zamuyi dashishi da ita saiga abulkhair kamar anjeho shi kai da ganinsa kasan babu lafiya domin afujajan yashigo wujuga wujuga,agaban Inna ya zube yana neman yafiyarta mudai gaba daya bamu gane inda maganar tasa ta dosa ba ashe wai adaren jiyane barayi suka shiga gidansa kuma garin neman kudi suka ciro wata tukunyar kasa a karkashin gadonshi wacce latifat tayi tsafe tsafenta aciki ta binne nan fa barayin suka fasa tukunyar ita kuma suka samu nasarar harbinta a kafadarta guda daya,fasa wannan tukunyar shine ya zama sanadiyyar tarwatsewar asirce asircen da tayi masa shi baya garinma yana can birnin kebbi amma da yake asirin ya karye take yaji babu abinda yake son gani sai iyalinsa da iyayensa shine fa ya taho kamar an jehoshi. Duk da cewa ya nemi yafiyata nidai bana sake masa shikuma yanzu babbar bukatar sa shine in amince inyarda insake koma masa domin shima harun tuni yace yabarwa yayansa tunda dama can shine yafi cancanta. Abunka da zuciya abarta akan abinda take so tuni yashawo kaina na amince zan koma gareshi,

Cikin yan kwanaki kalilan ya gama gyaran gidansa ya saka mana komai sabo,nida haidar muka sake zama yan gata awurinsa fiye da yanda muke ada can baya,

Gyaran jiki da k'unshi da kitso nayi nafito das dani ranar da zan tare kuwa shida kansa yazo ya daukemu ya tafi damu bayan baffah da innah sun yimana nasiha mai ratsa jiki musamman ma ni da nayi sakaci ada can baya na rinka tona asirin gidan aurena. Hmmm nida abulkhair yaufa shiru ne kawai saboda dukkaninmu muna dokin juna kuma muna missing junanmu shiyasa muka dunkule muka cure muka zama abu daya muka manta kowa da komai sai iya junanmu. Sati biyu ya kwashe agida yana tare damu baya zuwa ko ina sai kulawa da soyayya da yake nuna mana, farin cikinmu ya dawo kamar baya muna cikin kauna da zaman lafiya,batun latifat kuwa ya tattarashi ya ajiye agefe dan ko sunanta baya so yaji an ambata tana can itama a asibiti tana dandana irin rayuwar da ta saka na dandana abaya dama ai ramun karya kurarrene sannan abinda kayi shi za ayi maka dan ko kudin magani abulkhair yaki taimaka musu dashi nikuwa nan yasaka haidar a makaranta mai tsadar gaske nima ya siya min mota da gida hadadde yace nawane halak malak. Bayan wata biyu da tarewata nafara laulayi kuma a lokacin ne na matsawa abulkhair akan sai munje mun dubo latifat tunda har yanzu matarsa ce bai saketa ba, da yake lallaba ni yake yi haka ya amince,ai da naga latifat sai da nayi mata kwalla dama fa haka rayuwar take inji masu iya magana sukace rawar yanmata ce na gaba sai kaga yakoma na baya na bayan kuma yadawo gaba babu ruwan duniya,gafara ta latifat ta rinka nema tana cewa inyafeta nace babu komai nayafe Allah ya yafe mana gaba daya. Zuwanmu dubota da kwana biyu akace ta rasu haduwa mukayi dasu innah mukaje gaisuwa shikuma abulkhair ya karbo yarshi najlah bayan ya tambayeni wai idan zan riketa babu takura nan nace babu ai d'a na kowane kuma yaro shi me yasani? Nan na hadasu da nawa na rike babu nuna banbanci dan idanma ba fada maka akayiba bazaka taba gane cewa banice na haifeta ba,mijina kuwa zamanmu yaci gaba da wanzuwa cikin so, zaman lafiya da kuma kaunar juna ina fata Yan uwana za akula adaina yada sirrin gidan aurenki a social media,ina fata abinda yafaru agareni ni Radiya zai zama izina agaremu baki daya.

ALHAMDULILLAH

Yan uwa mata sai muyi hattara sannan mu nutsu mu rinka kiyaye sirrin aurenmu mu daina sakin baki muna fadar sirrinmu a inda bamu saniba musamman a online,mata da yawa sun samu kansu acikin hali kwatankwacin wannan ko ma fiye dashi kuma wani lokacin laifinmu ne dan mu muke bada kofar faruwar hakan,ba kowacce kawa zaki yarda da ita online ba duk da cewa akwai nagari to amma fa musani mugu bashida kama,Allah yasa mudace kuma yabarmu cikin kariyarsa akoda yaushe,taku ahar kullum Ummi Aisha.


*_Ummi Shatu_*👌🏻

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now