Shafi na tara

1.3K 122 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *ALKA'LUMAN MARUBUTAN HASKE*

    *KUNGIYAR:*
        *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
( *home of expert and perfect writers)*

     
   *AL'KALAMIN*
       *SLIMZY* ✍🏼

*RASHIN IYA ZAMA DA SURUKA*

  *BABI NA GOMA*
  *shafi na tara*

Kaiwa da komowa kawai takeyi a cikin dakin zuciyarta na tsakanin tafarfasa ko Ina a jikinta tsattsafo da zufa yakeyi lallai Abubakar ya shammaceta haka zaiyi Mata?Dan tsaki taja ta nemi waje ta zauna ta rafka uban tagumi ba karamin damuwa ta tsunci kanta cikiba domin burinta bai Gama cika ba tsakanin Abubakar da mahaifiyarsa burinta be wuce ta rabashi da kowa ba ta tabbatar da ya Zama mallakinta ta juyashi ita kadai Sai yadda taso....

********Daren ranan mama a tsaye ta kwana Tana sallah tanasaka Abubakar a cikin addua Dan burinta be wuce taga hankalin danta ta karkata garetaba Allah ya tsallakar dashi daga dik wani tuggu da matarsa zata hada Masa,Allah ya dawo da hankalinta gareshi ga Yan uwansa itama sadiya Allah ya shiryeta su zauna lafiya....

********Da safe Abubakar ya Gama shirinsa tsab zai fita kasuwa ya fito parlor sadiya na zaune fuskarta babu yabo babu fallasa yasha mamakin ganin canjawarta daga jiya zuwa yau dikda be tambayeta meke damunta ba yasan rigima takeji sai ya basar da ita,

  Yana hular kansa ya kalleta yayi Dan murmushi sanan yace "uwar gida sarautar Mata ranki ya Dade halimatu saadiya"

  Harara ta wurga Masa ta juyar da kanta gefe Nan da Nan ta kakalo kwallar kissa a idanuwanta,shiko gogan ganin haka ya zauna gefenta ya janyota jikinsa ya rugume sanan ya shiga shafa bayanta ta sigar lallashi,can kasa da murya yace "babyna ya akayi me kikeso?waya tabamun ke?"

  "Kaine"abinda tace kenan a takaice,Dan murmushi yayi yace "nida kaina?to ayimun afuwa yanzun a fadamin laifin danayi"

  Kara kwantar da kanta tayi a kirjinsa cikin muryar shagwaba da kissa ta Soma magana"haba Abubakar gaskiya Ni bakayimun adalci kamar ba auren soyayya mukayi ba yanzun ace sallah guda lace din da ka siyawa mama tsohuwa yafi nawa tsada?fisabilillahi ka hadamu nidasu shukra kannenka ka siya Mana Kaya tsada daya,har na mama yafi nawa?haba Abubakar"

  Ajiyar zuciya ya sauke dikda ransa ya Dan sosu Amma Sai ya danne "haba sadiya na dauka mun wuce wanan matsayin nidake,Nasha fada Miki ban hada mahaifiyata da kowa ba a rayuwata Dan meyasa kike kishi da ita?dik irin kyautatawar da nakeyi Miki Ina kokari wajen Kare hakkin ko wanne daga cikinku,gaskiya banji dadin wanan kalmar data fito daga bakinki ba"

  Tunda Abubakar ya Soma magana sadiya tayi kurrr da Ido Tana kallonsa bugun zuciyarta ya tsananta,tabdijan Ashe Abubakar be Gama kamuwa ba a wajenta,meke Shirin faruwa da ita?gidan jiya zata koma?inaaaa bazai yuwuba

   Mikewa tayi daga rikon da yayi Mata ta tsaya ta rike kugu ta Tana mishi kallon sama da kasa sanan ta Soma magana cikin tsananin tsiwa da rashin kunya"wallahi bazaa taba zaman lafiyaba matukar kana fifita mahaifiyarka da Yan uwanka Akaina,na Dade da fahimtar kana aurena ne bawai Dan kana Sona ba,saboda haka Ni wallahi gidanmu Zan tafi"Ta  fashe da kuka Nan da nan hankalin Abubakar yayi kololuwar tashi,ya tallabota jikinsa ya shiga rarrashunta kamar wata jaririya,

"Haba sadiya meyasa kikeson ki rinka tada hankalinki akan Abu Dan kankani bayan kinsan fa bake kadai bace ga ciki kinadashi baason Mai ciki da damuwa umm?yanzun ki kwantar da hankalinki zaa canjo kayan kinji banason kuka ya Isa"ya Sanya hannunsa ya goge Mata hawayen da takeyi ta Kara lafewa a jikinsa Saida ya tabbatar tayi shiru sanan ya gyara Mata kwanciya Akan doguwar kujera ya Mike tsaye yace "Ni Zan wuce kasuwa kinji ki kula da kanki saina dawo"

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now