Shafi na biyu

2.6K 204 5
                                    

KUNDIN HASKE

            Al K'ALUMAN Marubatan HASKE

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   AL 'KALAMIN✍🏼
  MAMAN KHADY

ABOKIYAR ZAMA
(Kishiya)


BABI NA HUDU
Shafi na biyu


GIDAN ABDALLAH; maganafa ta kankama domin kuwa nan da nan akafara hidima kasancewar daidai bakin gwargwado yana rufin asirinshi,itako yarinyar da zai auradin tuni dama sunriga sun shirya sabida da wani zata aura wata matsala ta gittawadda tasa auran yafasu shine yanzu Allah yabata abdallah.
   sunanta aisha,gidan iyayenta yana cikin layinsu abdallah din sannan tasami shaida mekyau ita da iyayenta.

Aisha baxangaji da yimiki nasihar kiyi hakuri da mijinki da abokiyar zamankiba dan Allah kadda kibari asami matsala ta bangarenki,banso ki biyewa zugan kawaye masu cewa wai zaki auri me mata yoshi me matar ba mutun bane koba namiji bane?
   Danhaka matar mutun kabarinshi inji hausawa dan Allah ki watsar mana da mutunci ki daraja uwargidanki idan kinaso ki sami nutsuwar auranki,kuma lallai ki dauketa amatsayin yayarki idan wani abu yashige miki duhu ko damuwa kamin duk wani yasani to ita tafara sabida tanada kusancin dake fiye da kowa sannan kidinga lura da duk wani takunta domin ki kwai kwaya domin kula da mijinki, kinsandai sun dade tare yasaba da ita da duk wani abu daya shafeta yanzu zaiji daban sabida zaijiki da sabbin abubuwa.
    idan tanada tsafta kekuma kikai kazanta to kinsami matsala.
   Allah yaimiki albarka yasa gidan aurenkine nahar Abada.

GIDAN ABUBAKAR; babu wani abu daya fasa na auranshi yana shirye-shiryen auran kuma yana kula da yaranshi domin kuwa tuni tabarmishi komai daidai da cikin jikinta cewa tayi dan bata da yadda zatayine lallai da shima saita ajemishi.abubuwa sunyimishi yawa amma tuni shimafa yafara sharewa da duk wani abu daya shafeta sabida lallai yafara gajiya da iskancinta sabida yagadai aiko mamanta su biyune kuma zamqnsu lafiya amma shine shi zataraina mishi wayau ta tadamishi hankali.
   wajan iyayenta ya shirya yatafi yaran na biye dashi.

kasancewar dama iyayen salma sunsan da maganar auren, saikawai yaimusu bayanin halin dayake ciki na abunda salman takemishi.

   Mahaifinta yaji haushi sosai na kasancewar salma cikin matan dakeda duhun kai na bangaren addini domin shi abunda ya dauka kenan cewa lallai duk wanda zaiyi jayayya da wani hukunci na Allah to lallai akwai jahilci cikin rayuwarshi.
   Hakuri sukabashi kamin mamanta ta tabbatarmishi da cewa lallai tana nan zuwa gidan zakuma tajamata kunne inda yabar yaran gidan yace idan maman zata wuce to tawuce dasu zai wuce wajan aikine.

Salma ashe baki da hankali bansaniba muzaki jama zagi da aibatawa cikin gari salma ina kokarin da mukayi wajan ganin kinsami wadataccen ilmi kaddai ace kudin banza muka kashe akanki?
   to waima idan kikace bakison abokiyar zama nufinki ke kadaice matarda mijinki zai zauna da ita?
   Sannan dazaki bakiso ya kara aure,inace ubankima biyun gareshi ko?

  To wallahi ki kiyayi kanki lallai alhaji yace wallahi kikabari abbakar ya sakeki to saidai ki nemi wani uban amma badaishiba haka nima dan haka idanma kinci gaba da yimai abinda kikaga dama to lallai kitanazarma kanki wasu iyayen da wajan zama amma badai muba,wawuya kawai me wayan banza,Ai anwuce wannan zamanin da mata ke tada hankalinsu akan abokiyar zama wallahi yanzu kan kowacce mace ya waye amma bandake, kije kita hauka harsaikin futa aranshi kinga amarya na shigowa saiya manta dake.

GIDAN ABDALLAH ;sam be nuna zakewa akan auran nashi bawai dan be farin cikiba a a kawaidai domin hankalin bilkisu ya kwanta kuma yasami hakan domin da ita akeyin duk shirye-shiryen daya dace 'yan uwanshi duk gidan suka zaunamata domin akwai fahimtar juna tsakaninsu domin akwaima wa inda suka nuna sam bekamata yai aureba tunda zamansu lafiya lau, saidai ya nunamusu yana bukatar aurenne bawai dan tagaza tawani wajeba.

An daura aure lafiya kuma komai yatafi yanda ake bukata,sai  dare sannan gidan yasarara da mutane anyi duk abinda yadace amarya na dakinta hakama uwargida tana daki da yaranta gidan yayi shiru.

  Shi kadai yashigo gidan kuma koda yazo falo yai zamanshi,saida ya huta sosai sannan ya kira wayar amarya data uwargida akancewa su taddashi falo.
     Kusan atare suka shigo kowacce jikinta da hijab murmushi yayi kamin yace ah malam abdallah duk malamai ya tara kenan.
    Duk murmushi sukayi kamin aysha takuma gaida bilkisun sannan ta gaida mijinnata.
    nasiha yaimusu sosai tare da addua yakuma bawa kowacce damar tafadi abinda ke ranta bayan raba kwana da sukai bayan gama kwanakin amarya.
   Addua sosai bilkisu tai musu sannan tace nidai amatsayi na babba na karamaka sati daya kacal akan satin da zakayima kanwata domin ku fahimci juna sosai Allah yabamu hakurin zama da juna dan Allah kanwata idan naimiki wani abu kigayamin mu daidaita sannan kadda kiyadda da zugan kawaye na dauki alkawari tsakanina da Allah matykar kinyi ba daidaiba zangayamiki domin bazan kullacekiba harmu sami matsala Allah yasa zamanmu ya dore har gaban Allah, saida safenku.

Dawani mayen murmushi yabi bayanta har cikin ranshi yakejin dadin da farinciki kasancewarta mata agareshi, danhaka abubuwan daya siyoma saidai ya adanasu a kichen.
     aisha kingadai yayarki ko?
   duk wannan maganar data fada har cikin zuciyartane ina sonta kuma ina alfahari da ita tana matukar gudun bacin raina dan Allah kuzauna lafiya idan naga wani sabon abu agidana to tabbas kece domin kuwa nasan halinta kema kiyi kokari ki kasance macen da mijinta zaiyi alfahari da ita kinji ko?
    Sosai yafara gwadamata halinshi domin kuwa abdallah lafiyayyen namijine aiko tai kuka da idanunta.

Koda yaje kichen domin doramusu ruwan wanka taddawa yayi bilkisu tasamusu harma yatafasa danhaka nashi ya diba ya gyra jikinshi sannan yatashi aysha bayan yakaimata ruwan shikuma ya wuce masallaci.

Bakaramar tausa bilkisu taima zuciyarta danhaka kamin garin Allah ya idasa wayewa har tagama shiryamusu abin kari,tagama gyara gidan da yaranta.

Zamansu lafiya babu wata matsala tsakaninsu da juna wanda hakan yai matukar faranta ran oga abdallah,da wannan damar bilkisu tacigaba da gyaran jikinta hankali kwance.
Aysha na matukar son yaran idan tafara shirme dasu kowa saiyayi dariya tuni yaran sun saba da ita.

AGIDAN ABBAKAR ;kuwa sam salma takasa kwantar da hankalinta balle kuma tasamar ma mijinnata shima.
Wannan shine dalilin dayakuma tunzurashi neman auren gadan-gadan cikin ikon Allah aka daura auranshi da jidda,wata kanwar abokinshi.

Salma irin matannan ne basu iya nuna fishi akan abuba sosai ta dauki fishi wanda ya tunzura mutane da yawa, mahaifinta ya hana kowa zuwa gareta danhaka koda aka kawo amarya babu kowa daga dangin salma saidai kawayenta masu zigata.

Duk irin yanda jidda amarya taso su zauna lafiya amma ina wulakancin yau daban nagobe daban sam sam taki bari su zauna lafiya.
     babu kalar bacin ran da abbakar be shaka ta bangarenta wanda arzikin yaranta kawai takeci da tuni ya yabata takardarta sabida yafara gajiya.

Salma kinyi mantuwa fa, domin kuwa duk abinda hakuri be baka shiba to lallai rashin ya bazai bakaba har gaba da abada kuwa.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now