6

1.2K 109 7
                                    

*KUNDIN HASKE*

            _Al 'kaluman Marubata_

     KUNGIYAR:-

     *HASKE WRITERS ASSOCIATION* (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
           *SAFIYA GALADANCI*

BABI NA GOMA SHA TARA

*K'AIK'AYI*

PAGE 6

Fitowa yayi ya tsaya daga waje har sanda Malam ya fito, da sauri yaje ya sameshi ya riko rigarsa yana cewa "Malam ka dubi girman zatin Allah karka raba ni da matata zan bata lokaci ta huce Na bata hakuri Dan Allah karku yimin haka" ya fada muryarsa Na rawa alamar kuka Malam bai damu ba ya kwace rigarsa driver Na isowa ya shige mota yabar saifullahi a tsaye yana tunanin wannan karon kila rayuwarsa tazo karshe ne, bayajin bayan mutuwa akwai abinda zai rabashi da juwairiyya, kasa dagawa yayi daga inda yake sai ya jiyo muryar juwairiyya tana yiwa khadija sannu, juyawa yayi yana kallon su sai yaga khadija Na bleeding ya zaro ido yana kallon su, amma abin mamaki ta bayanshi suka bi juwairiyya ko kallonsa batayi ba, yaga motar jawahir kanwar juwairiyya tayi parking sun shiga, jawahir tace "inace dazu kunje asibiti ance sun tsayar da zubar jinin"? Juwairiyya tace " munje fa ya tsaya amma inaga cikin ya fita ma Dan koda Na kiraki muna toilet abin tsoro jini kamar an kunna famfo bana tunanin cikin nan ya Na nan" jawahir tayi tsaki tana cewa "gara ma daya zube, kinsan Allah yaya indai khadija tasamu sauki wallahi sai Na zaneta, naji dadin dukan da abbanta ya mata ma" juwairiyya tayi murmushin dayafi kuka ciwo tace "daga asibiti sai Na baki ita ma kije can gidanki ki mata Dan banzab duka nima kai zuciyata nesa kawai nake da tuni Na ballata" shuru sukayi dukansu  khadija ko se sauke numfashi take, duk tabi ta kode idonta sunyi ja saboda kuka, daga yin Abu sau daya sai ciki, tunaninta ya katse jin zancen da su umminta keyi tana cewa "ranar da aka gano cikin shi saifullahi yace yayi magana da Abdullahi amma yace bazai fasa auren khadija ba, saifullahi dai yace sedai ya hada shi da Aisha ita kuma wannan suje su karata da kabir din Malam kuma yace babu ruwanshi yarshi ce Dan fushi ma yake da khadijan" jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "Allah yasa shi yafi zama alkhairi" juwairiyya ta amsa da ameen.

Tuni cikin ya fita, saida aka mata wankin ciki Wanda ya kara kodar da ita sai dare suka dawo gida suka shige abinsu.

Saifullahi kuwa gidansu Abdullahi yaje mahaifin Abdullahi yanata yi masa jaje da nuna masa ba komai bane idan anyi auren khadija da Abdullahi amma sai ya kafe da cewa "ni abinda ya kawoni ba wannan bane maganar Aisha ce Na bawa Abdullahi ita idan yanaso, ko gobe yakeso zan datse karatun ta adaura auren" ya ajiye masa kudi a gabansa yana cewa "sadakin khadija ne Na dawo dashi" shuru Malam Ibrahim yayi Dan baya so ya karawa saifullahi bakin Ciki sai yace "zanyi magana da Abdullahi din,Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi" godiya saifullahi ya masa sannan ya fito, duk ya fige dakyar yake iya gyaran jikinsa ma, yana isa gida ya zauna yana aikin kiran juwairiyya ko zata tausaya masa da halin dayake ciki yanada bukatar ta amma gashi Malam yayi masa Katanga da ita, haka wayar me ringing har ta katse bata dagawa, sai ma massage data turo masa cewa "Allah ya taimake ka shege bai zo duniya da jininka ajikinsa karo Na biyu ba, cikin dake jikin khadija ya fita Dan tun ranar da kayi mata duka take fama da ciwon mara" duk da kalamanta sun dakeshi amma hakanan yayi hakuri, ta wani gefen kuwa yana yiwa Allah godiya daya rabasu da wannan cikin Dan kullum dashi yake kwana yake tashi, yana tsoron suje zubar dashi ta mutu shiyasa ya kasa duk da cikin har ya fita baiyi kwana sittin ba.

Duk yadda yaso malam ya saka baki akan auren khadija da kabir hakan ya faskara, shikadai yasan yadda yakeji aransa, yana zaune mahaifin kabir ya aiko masa da sakon invitation a office, yana dawowa gida yasiya goro ya shiga rarraba katin daurin aure dakansa sai dare sannan ya zauna, ya turawa juwairiyya massage kamar haka "An saka date Na daurin auren yarki, ki aiko Ahmad ya karba miki ki gani, kuma kinsan kina shiga hakkina ko juwairiya, kinsan baki kyauta min ba ko? Dan Allah ki huce hakanan mana" batayi replying massage dinba duk da ta gani sedai ta kira jawahir ta fada mata takuma sanarwa khadija da zancen, a ranar khadija kwana tayi kuka amma tasan uban kuturu ma yayi kadan balle Na makaho tunda Malam yaki saka baki yace eh ko ya hana.

Babbar yayar saifullahi ita taga IV Na yawo. Taji haushi Dan haka ta kira saifullahi ta wanke shi tatas, balain ya masa yawa sai kawai ya kwashi kafa yaje gidanta.

"Haka zaka kwashi yarinya ka basu kamar batada daraja, saboda kawai kaddara ta afka mata, karamar yarinya ce fa duka shekarunta nawa sai kace Wanda bai san Allah ba dubi duk yadda ka lallace" kwantar da bayansa yayi jikin gojerar palonta yace "Anty asabe narasa ta ina zan kama ne, duka gefe biyu babu inda nake saka kaina inji sanyi, kwana goma sha biyar Malam ya bani Na bashi takardar sakin juwairiyya, ta ina ma zan iya sakinta, duk ya sauya min fasalin gida ya toshe hanyar duk da zan ganta, yarana ma Na kwana biyu ban gansu ba, ki fadamin ta inane bazan rikice ba" tsaki tayi tace "ka kwantar da hankalinka wannan duk horo ne abinda za ayi yanzu kaje zan kira ita juwairiyya ta kawomin khadijan bazan yadda ayi aurenta haka nan ba babu wani gyara, kaci gaba da hakuri kuma zasu sauko fushin zuciyane" sai da yajaddada mata zai ringa zuwa cin abinci Dan harda yunwa ke dawainiya dashi.

Kabir dakeda niyyar zuwa ya fadawa Babansu maganar Neman auren wata yarinya dayake so sai ya samu labarin ansaka ranar aurensa, aikuwa seda yayi karamar hauka, yana zaune yana jira har babansu ya dawo, samunsa yayi a Palo yace "gaskiya ni baba bana son yarinyar nan kawai baka tambayeni ba kaje kasa mana rana, yarinyar da duk wani Dan iskan titi yagama saninta" mari ya kwada masa sannan yace "Dan iskan titi ya wuce kai, duk Kaine silar lalata yarinyar mutane kuma wallahi sai ka aurenta"
Ganin yadda babansu yake masifa kamar bashi ba yasa ya bawa kabsgi shawara akan ya sassauta.

"Baba Dan Allah to kayi hakuri ka taimake ni iyayen yarinyar nan sunce inturo nayi maka alkawari zan hadasu su biyu in aura idan ka amince" kallonsa baba yayi yace "bayanzu ba sai naga yadda zaka rike yarinyar nan khadija idan kayi wasa kayi wasa da damar ka" dakinsa ya shige dan shima kansa yanzu ya gaji da damuwar kabir wallahi.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now