Babi na biyu_pherty Xarah

5.4K 333 5
                                    

KUNDIN HASKE

            Al 'kaluman Marubata

     KUNGIYAR:-

     HASKE WRITERS ASSOCIATION (home of expert and perfect writers)

   TARE DA AL 'KALAMIN✍🏼
          Fertymerh Xarah💞

HANGEN NESA.....

     
BABI NA BIYU

Shafi na d'aya

  Meyasa a rayuwa baki da gode Allah ne, meyasa kike hangen na wasu bayan ni ina iya bakin qoqari na naganin na faranta maki, arziki na da nasu ba daya ba, kimin adalci Safiya.

Adalcin kenan Aliyu idan har baxaka min abinda xai fito dani cikin jama'a ba, dubi dan Allah atamphar dake jikina, kudin ta dubu biyar ne kacal, na fita unguwa ana nuna ni, idan biki naje duk sai an fini fitowa amma ka dubi irin kayan da Bilkisu take sakawa na dubu ashirin xuwa sama, saboda mijinta yana son ta.

Ni bana son ki ne Safiya?

Baka sona kam idan har baxaka iya fitar dani kunyar jama'a ba, haba dai.

Yanxu fisabilillah atamphar dubu biyar banyi qoqari ba, mata nawa ne a gidan maxajensu masu saka atamphar roba wani ma ta dubu biyu xuwa uku yake siyawa matar sa, ina laifina, gaki ga mahaifiyata ga yarana duk nauyin ku yana kaina, duka duka albashina na nawa ne.

Taja tsaki ta nufi dakin ta tana fada sosai, ni na fara gajiya gsky.

Yayi shiru cikin tunanin hali irin na matarsa, kuma yana addua Allah ya shiryeta domin yana son ta.

Da dare ya shigo da Leda baqa a hannunsa, tana xaune a falo tana cin abinci,

Ganin baqar ledar hannunsa ya saka ta tasowa cikin murmushi tana masa sannu da xuwa,

Yaji dadi sosai yanda tayi masa,

Ya gida da yara, na same ku lafia.

Ai tun daxu suka yi barci fa, me muka samu haka acikin Leda yau kuma,

Ya miqa mata ledar cikin murmushi, sabulan wanka ne dana wanki na siyomana kafin kuma akai da cewa babu, kinsan ni bana son jin babun nan.

Tayi kicin kicin da fuska, ta tabe baki tana karban ledar a wulaqance a xaton ta wani abin dadi ne ya siyo ya kawo mata irin su tsire bayan ga nama a abinci tana ci.

Ta duba sabulan tana kallonsa cikin mamaki,

Yanxu dan Allah Aliyu ka rasa sabulun siyowa sai Giv ina ma laifin Premier idan baka da kudi ne,

Yace yanxu ma nayi laifi kenan Safiya, sabulu ai duk sunan ta sabulu buqata kayi wanka ta wanke maka jiki da kyau, amma ina laifin Giv.

Gsky ni bana son ta baxan iya wanka da ita ba, yanxu ma sabulun da naga bilkisu ke amfani da ita ta ruwa ce, irin ta nake so na fara amfani da ita saboda gyaran jiki.

Cikin fusata yace sai anyi magana kice bilkisu wai ni da mijin bilkisu daya ne, abinda nake da dashi xanyi amfani idan bakyaso ki bari.

Tace to shikenan ka dauki abunka bana so, ta dauki abincin tayi shigewar ta daki a fusacce.

Shiru yayi yana kallon ikon Allah yanda Safiya ke neman maida kanta wata mace ta qarfi da yaji bayan ba haka take da farko ba, baisan a ina ta dauko wannan d'abiar ba, idan ma arziki ne ai har yafi iyayen ta ma,

*

'Washe gari bayan fitar sa gurin aiki ta nufi gidan maqociyar nan bilkisu, ta bar yaran ta biyu a gida ko wanka bata masu ba.

Ta sami bilkisu ta hada custard tana sha ga wainar kwai a gabanta,

Tace yau me ake cine haka bilkisu,

Tace bismillah Safiya xo kici, sauri ma nake ina so na fita kafin abban waleed yaxo.

Safiya ta xauna tana cin wainar, tace ina xakije haka.

Gida xanje nayiwa babana godia kinsan na gayamiki ya siyamin telar dinki, amma baxan jima ba xan dawo.

Shiru Safiya batace komai ba sai custard take faman sha, bilkisu ta tashi ta soma shiri cikin wani material,

Kai amma material dinnan yayi kyau bilkisu, nawa kika siya cewar Safiya tana kallonta,

Abban waleed ya siyamin lokacin bikin qanwata, ai ba wani mai tsada bane kudin sa baxai wuce dubu takwas ba, ai na gayamaki ina saka kaya marar tsada.

Eh na tuna haka ne, gsky yamin kyau idan kin dawo xaki bani na nunawa aliyu ya yimin irin sa.

Tace ke kin fiye fitina Safiya bafa komai bane ka gani kace lallai sai mijinka ya siyama ka ina yawan gayamaki hakan, nifa wlhy duk abinda abban waleed ya kawo min kome tsada ko marar tsada ina so kuma haka nake karba nayi masa godia saboda yaji dadin siya min wasu, kinga ma wasu flat shoes da ya siyo min jiya, ta dauka tana nuna mata.

Kai amma fa sunyi kyau bilkisu, nawa kudin nasu.

Gaskiya ban sani ba saboda xumudin takalmin a jiya ban tambaya ba, yauma yace yana so nayi masa farfesun kayan ciki idan na dawo.

Iyyeh kice xakici dadi yau, gaskiya kinji dadi bilkisu.....

Da yamma Aliyu ya dawo gidan, ya ajiye dawa da yaxo da ita yana kallonta,

Yau Safiya ba gaisuwa ne?

Hmmm ta tabe baki tana fadin, menene haka kaxo dashi.

Yayi murmushi yana fadin wallahi tuwon dawa nake sha'awar ci Safiya ki daure ki min shi a gobe.

What? Ni nayi maka tuwon dawa haba Aliyu wai me ka dauke ni ne, kowace mace mijinta na sha'awar ya kai mata, nama ko kaxa ko kayan ciki ayi masa farfesu yaci iyalinsa ma suci su more amma kai kake mgnr tuwon dawa a yanxu, gaskiya baxan yi ba, kaji na rantse wallahi baxan yi ba, ta kife shinkafar da take gyara a gurin tayi shigewarta.

Shiru kawai aliyu yayi baice komai ba, ranar ko girki bata masu ba haka ya dauki yaransa yaje dasu inda mahaifiyar sa suka ci abinci da cewar maman tasu ba lfy.

'Washe gari ya tafi gurin aiki dama malamine a makarantar boko.

Tana ganin haka ta dauki dawar taje da ita gidan mahaifiyarsa.

Inna ga dawa Aliyu yace a kawo maki,

Dawa kuma bayan wadda ya kawo min a jiya, ai yabani tawa inaji taku ce ko kuma yana nufin ki kai gidanku.

Kai haba, taki dai ce Inna,

Nagode sosai, Allah ya masa albarka ya qara budi, ki qara masa godiya.

Safiya ta tashi tabar gidan tayi shigewarta gidan bilkisu.

Aliyu da yaje gaida mahaifiyarsa take cewa, harda wata dawa kuma kake aikomin bayan wadda kabani a jiya, dawainiya batayi maka yawa bane Aliyu,

Yayi shiru yana kallon dawar da mahaifiyarsa ke nuna masa babu tantama wadda ya kai gidansa ne.

Da kyar yace ba komai Inna,

Tace nagode Aliyu Allah shi maka albarka.

Yace ameen.

Ya tashi ya fito jiki a sanyaye.

KUNDIN HASKE💡Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora